Download Complete SONE KO K’IYAYYA by Prince Neh Romantic Hausa Novel PDF

SONE KO K’IYAYYA??

It’s rometic love story

Story & written

by mommyn fareesa

.

33…

k’ofar parlourn suka shiga”umma da Abdul hakeem da yaya isma’il na zaune a parlourn”umma ta bisu da kallo tana Amsa sallamar su”Aranta tana fad’in dama nace yadda kika kori kanki da kanki kece zaki dawo da kanki d’in”saidai hasken dataga mama gaje da zubaida sunyi yabata mamaki”bata gama mamaki ba”saida mama gaje ta zauna ta cire mayafi suna gaisawa”tana yatsina fuska tace”ga zubaida nan zata zauna Anan zamuje wajen taronmu na y’an kasuwa sbd Abubuwa sun k’ara kud’i”idan nadawo zan biyo natafi da ita gida”isma’il da Abdulhakeem suka gaisheta suka fita”umma na murmushi tace”kasuwanci kika fara kenan?
“Eh sati 2 kenan kuma Alhamdllh”bara natafi kar Ayita jirana”ta fad’a tana gyara mayafinta”umma tabi suturan jikinta da kallo tana mamaki”wanda mama gaje na lura da hakan”Aranta tace”kin zata d’aura manyan kaya saike matar me kud’i ki cire ki bani kwance”to yanzun na wuce wannan matakin…. kud’i y’an 500 guda 4 ta zaro ta mik’ama zubaida tana fad’in gashi Idan kin buk’aci wani Abu”kafin zubaida tayi mgn”wayar mama gaje tayi ringing”ta zarota dg cikin jaka tana fad’in kinga yaya hauwa Anata kirana saina dawo”dg haka ta fice”umma baki bud’e take binta da kallo harta fita dg cikin parlourn….fitowar mama gaje dg gidan”yayi daidai da In’am ta bud’e gidan gaba na motar yaya Aliyu zata shiga”shima yana k’ok’arin shiga driver sit”kallo d’aya ta musu ta d’auke kanta tayi hanyar titi”tana tunanin idan tadawo saita sanarwa umma ta ganshi da yarinyar nan….
yaya Aliyu yana driving d’in yakira me yimasa Aski yasanar masa nanda y’an mintina yana nan isowa”In’am dai na saurarensa har yagama wayar batayi mgn ba”kallonta yayi yana fad’in gobe karki bari yusuf yacemun kin b’ata masa lokaci”k’arfe 7 ki tabbatar kun shirya”7:30 tayi muku a skul”to yaya nifa bacci nake komawa idan nayi sallah sai wajen 7 d’in nake tashi ko?”kuma wannan yaya yusuf d’in yayita zagina yana mun fad’a”ke kuma bakya son fad’a gashi bakyajin mgn ko?”to bari kiji muddin kika b’ata masa lokaci baki shiryaba”da kaina zanzo natasheki da bulala”meyasa bazaki kwanta da wuriba sbd ki tashi da wuri?
“shiru tayi tak’i mgn sbd taso yagoyi bayanta Amma yak’iya”shiru shima yayi be koma mgn ba…sadda suka iso islamiyar hud’u saura minti 8″dama kuma 4 daidai suke shiga Aji”sadda ta fito dg cikin motar”su kuma su Aseeya su ukku zasu shiga ciki…… maryam! zonan ki Amsa”yafad’a cikin sanyayyar muryanshi yana fitowa dg cikin motar”in’am ta juyo tanata b’ata rai”Aseeya ta tsareshi da ido tana kallo kamar zata cinyesa” tana tafiya har tana yin tuntub’e bata luraba”In’am dake lura da ita taja tsaki sbd mugun haushi taji tabata”ta wani gallah mata harara”yaya Aliyu da farko ya d’auka koma shine tayima tsakin”saida yakalleta yaga yadda ta harari Aseeya dake k’ok’arin shiga cikin get d’in makarantar”Anan ya fahimci da ita take….ina wuni?”cewar Aseeya tana d’an murmushi”yaya Aliyu yamata kallo d’aya ta cikin bak’in tubarau nasa yace” lafiya qlau…
. b’ata fuska In’am tayi tana cewa”yaya shine ka Amsa gaisuwar wannan y’ar rainin hankalin?”maryam bazaki dena wannan rigimar da yaraba ki nutsu kiyi karatu?”ina fayi ko?”shikenan da dare zanzo na duba books naki”to gani ko?”saikin gama b’ata ran saina sallameki ko?”shiru tayi tana dai tsaye gefensa tana wasa da yatsun hannunta”yayinda tuni su Aseeya sun shige ciki…. Ahankali yasaka hannunsa cikin Aljihun 3quater d’in dake jikinsa yazaro big bom da wata chacoolate yamatso yana mik’a mata”d’an murmushi tayi tace”yaya ban manceba tun ina js 1 kake bani irin wannan chacoolates d’in da big bom”har na girma baka dena bani ba”ta k’are maganar tasaka hannu biyu ta Amsa tana masa godiya”shidai yana kallon ta can yamotsa red lips nasa yana fad’in daga dai iya js 1 d’in kika iya rik’ewa”Amma tunda kin girma zan dena baki ko?”nidai bafa haka nake nufi ba”ki wuce kije”batace komai ba ta juya ta tafi”saida tazo zata shiga get ta juyo ta kallesa taga yana danna waya”ta shige ciki tana b’ata rai”yaya Aliyu yayi murmushi sbd tunda ta juya yake kallonta da yaga zata juyo yamaida idonsa kan waya”motar yabud’e yashiga”ya aza kansa saman sitiyarin motar ya lumshe ido yana tunani…..yafi mintina 10 Ahaka sannan cikin mutuwar jiki yaja motar yabar wajen….
cikin sa’a mama gaje ta sami nafef ta shiga bayan ta gama waya da hjy wasilah”wani d’an k’auye ne yakaita”ta biyashi 1500″bayan ta sauka ta hango hjy wasilah nesa da ita tana tsaye jikin wata bishiya”mama gaje ta nufeta tana mamakin dama A wannan k’auyan ne dodon yake?……naso mu taho tare dake to sai kikace sai kin fara zuwa gidan hjy hauwa”cewar hjy wasilah sadda mama gaje ta iso gefenta”kedai bari naje dan ta ganni tasan na sauya nima na samu duniya yanzun”dariya hjy wasilah ta dingayi”kafin su kutsa cikin daji Inda keda dogayen shifkoki suna tafiya”sau 3 mama gaje nayin sartse da k’aya sai mita takeyi tana fad’in itafa ta gaji da tafiya”hjy wasilah na bata hak’uri da sanar mata sun kusan kaiwa…sunyi tafiyar kusan mintina 30 kafin su iso Adaidai bakin wani iccen gawo”suka tsaya suna kallonsa da waige waige sbd kar wani yagansu”wanda da wuya kaga mutum Anan sai idan manomi ne”wasu surutai hjy wasilah tayi….
Atake dg tsakkiyar bishiyar yabud’e “saiga hanya da k’ofa”babu b’ata lokaci suka shiga wajen ya rufe”sai gasu adajin Allah ta’ala “saidai Inda suke zagaye yake k’asa da sumunti”sannan Akwai bukkoki da gulbin ruwa can baya”sai wata bukka babba da’akejin motsin mutane Aciki”hjy wasilah tace”muje can zamu shiga”kowa nacan da mun gama had’uwa dodo zai fito muyi mgn”dato mama gaje ta Amsa suka shiga…bbu jumawa suka fito suda yawa”d’aya bayan d’aya haka suka jera suna dg tsaye”kowane da riga bak’a babba ta yadi Ajikinsa” sun aza saman kayan jikinsu “sai hula jaa duk kowa yasaka”maza su sha ukku ne guda yak’aru”wanda Ada su 12 ne”mata kuma su takwas ne yanzun sun koma su tara”bayan dodo ya bayyana”akace sabbin shiga k’ungiya su fito”Atake mama gaje da safwaan suka fito dg gaba”Aka basu wani Abu kamar jini Acikin wata k’warya sukasha”tunda safwaan yaga mama gaje yaga kamar yasanta”
Amma saiya share”mama gaje Aka bata wani dutse ta dafa tayi Alk’awarin kawo mijinta”bayan ta gama Aka bama safwaan yadafa”shima yayi Alk’awarin zai kawo mahaifinsa sati na sama…..bayan kowa yagansu kafin dodo ya sallami kowa”kasancewar kusan k’ofar shigowa matsafar guda hud’u ce”gabas, yamma, kudu, Arawa”ta yamma Anan mama gaje da hjy wasilah da safwan da wani suka biyo”suna fitowa safwann yace”duk A cikin garin kano kuke ko? yafad’a yana kallon su mama gaje”kasancewar shi namijin da suka fito Atare shinema yasaka safwan cikin k’ungiyar”mama gaje na washe baki tace”Eh nida ita duk Anan muke”okay bbu damuwa muje na saukeku Agida nima can nayi”gaskiya ka kyauta sosai”Amma nidai bama gida nayiba”GRA nasssarawa zanje”okay yafad’a”Amma saida yaji fad’uwar gaba sbd yasan Anguwar su dr Aliyu me tubarau ce”bece komaiba suka dinga tafiya har suka iso Inda safwaan yayi parking”mama gaje da hjy wasilah suka zauna a back sit”safwan da gudan suka zauna A front sit”suna fira jefi jefi har suka iso Anguwar G R A gab da magrib… Adaidai bakin k’ofar wancan gidan zan sauka”cewar mama gaje”k’irjin safwan na bugawa yace”me jan get d’in?”Eh nan “Allah sarki Anan kike kenan?”ah ah yayata hjy hauwa ke Aure Agidan”ta k’are maganar tana fitowa dg cikin motar tana musu godiya…. Atake safwan yafahimci mama gaje k’anwar mahaifiyar dr Aliyu ce”wani shegen murmushi yasaki me wuyar fassara”k’asan zuciyarsa yana zargin k’ilan umma bata taimakama mama gaje”ko kuma mama gajen nason tafi umma wadata shiyasa ta zab’i shiga k’ungiyar Asiri..
..yana wannan tunanin yaja motar yayi gaba”wanda tun lokacin da motar tayi parking Akan idon yaya Aliyu dake zaune cikin mota ya Ajiye In’am harma ta shiga gida”shi kuma zai tafi Asibiti”yana k’ok’arin tashin motar yaga motar dayabi last week har k’ofar gidan safwan tayi parking”gashi me tinted ce ba’a ganin na ciki saidai na ciki yaga na waje”kamar yadda motar yaya Aliyun shima take”gaban yaya Aliyu yayi mugun fad’uwa da yaga mama gaje ta fito dg cikin motar ta shige gidansu….✍️
Prince neh

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.