Download Complete Bintu Diyar Bayi Book 2 Romantic Hausa Novel PDF

Bintu Diyar Bayi Ce Book 2 Complete

Written By: Khadijah Sidi

Tuni waje ya kaure da salati da salallamin bayi, Jakadiya ce ta sa aka yi maza aka shigar da K’amariyya daga cikin d’aki gudun gulman da ta san tabbas sai ta yad’u daga bakin bayin da ke wajan. Bintu kuwa ta ma kasa gane komai, kukan ta kawai ta ke, aure dai an d’aura mata, ko ta na so ko ba ta so tafiya ne dole a tafi da ita. Gashi a rasa wanda za a d’aura mata sai saurayin Gimbiya K’amariyya, Yerima Barde na Fabarusa! Hannu biyu Bintu ta d’aura bisa kan ta ta na mai fad’in

‘’Wayyo ni Bintu alk’iyama ta ta zo’’

Daga cik’in uwar d’aka, bayan an kori duka bayin da ke b’angaran Jakadiya, Hajja Kilishi da Inna Salti wanda Jakadiya ta aika Ladiyo da Kyallu su sheda ma su abun da ke faruwa ne su ka shigo d’aya na bin bayan d’aya, biye da su Gimbiya Binta ce, wacce ita ma labari tuni ya je mata.

Jakadiya ta umarci bayin da su ka taka mata baya su yi jiran ta waje. Bayan an watsa ma Gimbiya K’amariyya ruwa, da rokan Allah ta farfad’o ta na mai bin su da kallo kamar lokacin ta fara ganin fuskokinsu. Kanta bisa kan cinyar Inna Salti, Jakadiya zaune gaban ta sai kuma Gimbiya Binta wacce ta dad’e da gigicewa da jin lamarin da ya faru, in ban da kuka babu abinda ta ke don gani ta ke duk laifin Bintu ne ko shakka babu ita da uwarta ne su ka sa musu hannu wannan balk’in ya fad’a kan ‘yar uwarta.

Ko da idanun Gimbiya K’amariyya ya sauka kan Gimbiya Binta, ita ma d’in ta fashe da kuka don sai a sannan ne ta dawo cikin hayyacinta sosai. Cike da damuwa Hajja Kilishi ke tambayar

‘’Menene ne? Gide menene ke faruwa? Tun dazu fa nake tambayar ki Binta amma amsa ta gagara daga gareki, yanzu kuma mun samu ta farfad’o maimakon a sami sauki ina, kun maishe da gida kamar wajan makoki! Shin ba kwa gudun abinda zai je ya dawo? Kun fa san gidan ga cike yake da baki da kyar na sami hitowa daga cikin jama’a, ko rufa mana asiri ku sheda mana abun da ke faruwa.’’

Cikin kuka muryarta dak’yar ya ke fita, Gimbiya K’amariyya ta amsawa Hajja Kilishi, ta na mai fad’in

‘’Na shiga uku Hajja, Inna Salti na shiga uku, na d’au wuk’a na dab’a ma kaina, Allah Ya nuna min ikonSa, Barde…..Yarima Barde na Fabarusa……’’

Kuka ya ci k’arfinta, ta kasa k’arasawa sai shasshek’a ta ke. Cikin rashin fahimta Inna Salti ta ce

‘’Barde? Me ya faru da Barde na Fabarusa?’’

‘’Ni kam ta dad’a sa kai na cikin duhu, jakadiya wagga yarinya ba gamo ta yi ba kuwa?’’

Cewar Hajja Kilishi cike da damuwa.

‘’Yarima Barde da Didi masoya ne, shi ne dalilin ta na k’in amincewa ta auri sarkin Fabarusa wanda yake mahaifi a gareshi.’’

Gimbiya Binta ce ta amsa ma su.

‘’Kayya! Kai wagga lamari da me yayi kama! Kun ga irin ta ko? Gashi dai an cuci d’iyar mutane kin kuma cuci kanki K’amariyya, anyi gudun gara an tadda zago! Jakadiya dai ga irinta nan dai kin gani don kuwa wagga kulli ke da wagga d’iya ku ka kulla.’’

Fad’in Inna Salti ta na mai nuna matuk’ar b’acin rai.

Jakadiya da tunda aka fara maganar ta sha jinin jikin ta, jikinta ya yi sanyi kamar wacca aka tsunduma cikin ruwan sanyi cewa ta yi

‘’Uhum Allah shi ja da ran ki, yo to ni me zance? Ni ina naga ta ce wa? ‘’

Cikin kuka don kuwa idanunta sun rufe K’amariyya ta furta

‘’Don Allah ku taimaka a warware wanga lamari, don Mai Sama, kwarankwatsa zan iya rasa rayuwata, dan Allah ayi maza a shedawa takawa kafin na rasa raina, Ammu ki taimaka min…..’’

Kai Hajja Kilishi ta jinjina kafin ta ce

‘’Gide Takawa zai saurari wanga azzance kuwa Jakadiya? Yanzun ga ya na can wajan liyafar d’aurin amren nan……’’

Kafin Jakadiya ta amsa Gimbiya Binta ta yi saurin taran numfashin ta ta hanyar fad’in

‘’Ku taimaka tun kafin a makara, dan kuwa ba Sidi ba ko ni ma ina tara muddin ba a warware wanga
amre ba, ya d’iyar bayi za ta amri mutum kamar Barde, dan Allah Jakadiya ki sama mana mafita tun kan na had’iyi zuciya na mutu dan kuwa ciwon da na ke ji ya ma fi na Didi’’

‘’Makara kam an riga an makara, saidai fa a jira bayan komai ya lafa a yiwa Takawa magana watakil shi bai zai rasa dabara ba.’’

Cewar Hajja Kilishi yayin da tashi tsaye jiki sanyaye, tak’ara da fadin.

‘’Kunsan mu na da baki, duk abinda za ku yi kada ku manta da martabar Takawa, ku kula ku kame kanku kada ku jawo mana abun da zai halaka yankin ga gaba d’aya’’

Ta na gama Magana ta juya abun ta ta fice, ta bar Inna Salti tare da Jakadiya cikin al’ajabi. Gimbiya Kamariyya gani ta ke sam Hajja Kilishi ba ta damu ba saboda ita dama ba ta ta6a haihuwa ba shi ya sa sam ba ta damu da lamarinsu ba. Ita kuwa Gimbiya Binta abinda ya tsaya mata a rai bai wuce na ta na murnar raba Bintu da masoyin a Aisar, sai gashi ta zama matar wanda har ta gama rayuwar ta a doran k’asa ba za ta sami kamar shi ba, abun takaici ta yiwa yar uwarta asarar masoyi, duk akan wanda sam be ma san ta nayi.

 

FREE DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Bintu Diyar Bayi Book 2

The most reliable and easiest way to obtain the complete Bintu Diyar Bayi Book 2 isto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Bintu Diyar Bayi Book 2 in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete Bintu Diyar Bayi Book 2 booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.