Download Complete MATAR DAMUSA by MALLAKIN ASMEETAH Romantic Hausa Novel PDF

FREE BOOK

MATAR DAMUSA

(the wife of tiger)

MALLAKIN

ASMEETAH

NASARA WRITERS ASSOCIATION
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

BOOK ONE

PAGE 19 to 20

Mommy fad’uwa tayi sumammiya ganin halin da Junaid ya shiga, tinda uwarta ta haifeta bata ta6a ganin wannan al’ajabin ba sai yau akan d’anta wanda ta haifa.
Junaid ne a manne da jikin gini an d’aga shi sama yayi cross kamar yanda akayiwa Jesus Christ, jikinsa yayi jawur sai tabo-tabon ‘kunar wuta ga shatar bulala ajikinsa duk ya faffashe babu kaya a jikinsa sai jageren wando wanda baije gwiwarsa ba, kansa a sunkuye wuya ya karye kamar wani matacce ko numfashi bayayi, sai gumin da yake gangaro mishi daga cikin sumar kansa,
Abunda ya faru da shi shine 👉. Naushin AYUSH da yayi a rashin sani shi ya jawo masa wannan bala’i, domin Naushin ba iya ita kad’ai taji ciwo ba hatta mahaifinta sarkin matsafan duniya sai daya jijjiga da wannan naushin! hakan yasa ya turo mutanensa wato Manya-manyan Aljanu guda uku don su hukunta shi,
Allah sarki bawan Allah yana cikin baccinsa yaji sau’kar bulalar kaca wacce aka cirota daga cikin wutar su na tsafi, duka d’aya fatar jikinsa ya fashe a razane ya tashi yana waiwaye amma baiga kowa ba su kuma suna tsaye a kansa, cikin fushi babban aljanin cikinsu ya yi wurgi da shi sai da kansa ya bugi jikin gini, kafin ya Ankara an sake d’agashi sama aka buga shi a ‘kasan tiles, haka suka cigaba da buga shi da ‘kasa tsabar wahala ko kuka ya gagara yi balle ihu, har sai dayayi jina-jina suka d’aga shi kamar tsumma ko motsi bayayi sai numfashi sama-sama, suka d’aure hannunsa d’aya da kacar wuta haka d’ayan hannun, wannan aljanin ya ri’ke hannun dama shima wannan ya ri’ke na 6angaren hagun sawayensa suka had’a biyu suka d’aure guri d’aya, suka manne shi a jikin gini.
Cikon na ukun kuma bulala ya fara zabga masa shi kuwa hatsabibin uba wato Ayush father watsa masa garwashi ya Fara yi ajiki ta cikin madubin tsafi, ana jibgarsa kuma ana watso masa garwashi, haka jikinsa ya koma ba dad’in gani jiki duk ya farfashe suna cikin gana masa wannan azabar wuyansa ya karye ba alamar motsi, shi Ogan yasan bai mutu ba doguwar suma yayi domin tsafin Damusar su bazai bari ya mutu ba sai dai yasha iya wahalarsa.
(Innalillahi wannan ai gwara mutuwarsa).
Haka *BOKA* *ZALIMU* ya bada umarni a cigaba da hukunta shi har na tsawon kwana uku 👌
Farin Bafulatani mai Ba’kar Zuciya, Sarkin Matsafan Duniya (Boka Zalimun) Baban AYUSHH
Shi a fad’ar sa daka ta6a Ayush gwara ka ro’ki mutuwarka,
Domin duk duniyan nan ba wanda yake so sama da d’iyarsa Ayush, ko cinyaka ce ta cije ta saiya zaro hannunsa ta cikin madubi ya mur’kushe ta 😳😳
(Anya kuwa d’aukar fansar Junaid zaiyu akan d’iyar Bara’atu kuwa 🤔).
___________________________
Ihun da Mommy tayi ne ya jawo hankulan kowa na gidan,
Ayush tana cikin cusa abinci sai da ta razana daga zaune ta mi’ke tsaye, sarkin tsoro har jikinta ya Fara 6ari tayi cikin toilet da gudu ta danna sakata!
Security gidan kuwa suma da gudun gaske suka shiga cikin d’akin direct d’akin Junaid suka nufa saboda sun san duk wani problem daga d’akin Junaid yake fitowa,
Suna shiga cikin d’akin suka tarar da abun al’ajabi, zaro idanuwa sukayi waje sun firgita da ganin Junaid a haka ga kuma mommy a shanye a ‘kasi sumammiya, cikin zafin nama suka nufi gurin da Junaid yake Gadan-gadan sun d’ago hannu zasu jawo Junaid nan sukaji an had’a kayuwansu biyu aka gwara kamar daga sama kuma basuga kowa ba, ba ‘karamin buguwa akayi musu ba kwakkwalwarsu ne ya fara juyawa kafin nan kowannen su suka fad’i sumammu, sauran two bodyguard suma ganin hakan yasa suka nufi gurin babu tsoro a fuskarsu zasu sa hannu su finciki Junaid daga jikin gini sukaji an sha’ko wuyansu duk su biyun an d’aga su sama kakaki suka farayi suna ri’ke wuyansu, saiga mai gadi shima ya shugo da gudu cikin d’akin abunda ya ganine yasa shi tsayawa cakk ganin gardawa a sama suna lilo da ‘kafafuwansu kuma bai ga abunda ya d’agasu sama ba, nan take yasau fitsari a wando jikinsa ne ya hau 6ari,
Su kuwa sai da numfashin su ya tsaya cak sannan aka wurgar dasu kan mai gadi da yayi sumar tsaye, sai yaraff duk su biyu akan mai gadi shima saida yayi asalin suma jin Manya-manyan gardawa a samansa.
Bayan 1hour Ayush dai tana cikin toilet jin ihun da akayi yasa ta 6oye a gurin, tana tsugune har ta gaji jin babu komai yasa ta bud’e ‘kofar toilet tana Le’ke-le’ke cikin sand’a take tafiya har ta sau’ko falo babu kowa,
A hankali take ‘kiran sunan “Aunty, Aunty, kina Ina ne” taji shuru ba’a amsa mataba, ta nufi kitchen tana bud’ewa taga wayam ba kowa
Anan fa ta fara rawar jiki tsoro ne ya bayyana akan fuskarta, “innalillahi wa inna’ilaihi raju’u, Allah yasa dai ba 6arayi bane suka shugo gidan, naji ihu kuma yanzu babu kowa”
Tana magana cikin kuka hawaye ne sharaf-sharaf suka fara gangaro mata a saman kunci, ta lalle’ka ko Ina amma bataga Mommy ba, ta duba agogon saman bango 12:30 ne.
Tayi hanyar waje ko zataga security hankalinta zaifi kwanciya,
“May be an kirata ne a asibiti” a cikin ranta take wannan maganar!
Abun mamaki ko dataje waje bata ga kowa ba hatta mai gadin sai haske Dara-dara ta ko Ina,
Wani irin yawu ta had’iya ga gumi kuwa daya fara tsirto mata, kakkarwa ta somayi tana tunanin kar itama a sace ta
Da gudun gaske ta koma cikin d’aki tana maida numfashi,
Ta zauna a saman kujera 1seater dafe kanta tayi ta fara rera kuka
Ita kanta ta rasa shin kukan mai takeyi
Shin na rashin ganin mutanen gidan ne ko kuma kukan tsoro ne, tana cikin wannan halin ta tuno da Junaid! Da sauri ta d’ago kanta idonta sun rine sunyi jaa “Ina yaron gidan, ko shima an sace shi” tana magana tana kallon upstairs d’in d’akin Junaid
Cikin rawar jiki ta mi’ke da sauri tayi hanyar d’akin Junaid tana taka matakala da sauri-sauri kamar zata kife,
Tana zuwa daf da d’akin tasa hannu zata bud’e naushin da Junaid yayi mata ne ya fad’o mata a rai, tsayawa tayi cak cike da fargaba ta fara tunanin “ya za’ayi na shiga d’akin wannan azzalumin d’azu ya naushe ni yanzu kuma ban san wani muguntar zai ‘kara mun b, ta juya zata bar gurin ta koma falo sai wani tunanin ya sake fad’o mata shin idan kuma shima ansace shi fa? Inma ba’a sace shi ba ai zai fita ya nemo mutanen gidan!
Knocking ta fara yi taji shuru ko motsi bataji ba ta sake buga ‘kofar still ba motsi
Almost 30minute tayi a tsaye tana sa’ke sa’ke a raanta
Daga baya ta yanke shawarar shiga kawai, cikin rashin sa’a tana shiga tayi tuntu6e da mutum a gabanta,
Juyowa tayi ta kalli gurin ganin Mommy a kwance yasa taji fad’uwar gaba,
“Innalillahi was inna’ilaihi raju’un Aunty meya sameki” jijjigata ta somayi taga babu alamar motsi
Juyawar da zatayi taga mutane uku aguri d’aya 2 bodyguard da mai gadi ja da baya tayi cikin firgici da tsoro tana waiwaya gabanta taga still 2 bodyguard kwance ba motsi
Daman bodyguard 4 ne a gidan sai mai gadi
Bakinta ne ya soma kakkarwa ko magana ta kasayi
Ga wani irin guminda yake yarfo mata
Cikin fargaba da tsoro take bin d’akin da kallo
Karaff idonta ya sau’ka akan Junaid dake manne saman bango rai a hannun Allah, ‘Kara ta sau tare da toshe bakinta kuka ne yaci ranta yau taga abunda tinda aka haifeta bata ta6a gani ba.
Da gudun gaske ta nufi gurin da Junaid yake, jinin da yake d’idd’iga daga jikinsa duk ya 6ata tiles d’in d’akin,
‘Dagowa da kanta tayi ta ‘kura wa fuskarsa ido lokaci guda kuwa ta zaro Manya-manyan idanuwanta waje bakinta ne yake motsi kamar maiyin magana, jikinta kuwa rawar sanyi ta soma, cikin firgici ta jaa baya da sauri sai da ta fad’i ‘kasi still idonta akan Junaid
Da kyarr ta iya bud’e bakinta cikin kuka ta fara fad’in
“Wayyo Allah nah Umma nah, Kaine ka kashe mun Ummana bazan yafe maka ba, ka sanya ni cikin maraici! Saika tozarta a rayuwa, sai kayi mutuwar wulakanci kamar yanda ka kashe mun mahaifiyata”
Gaba d’aya Ayush idonta ya rufe bata ganin halin da Junaid yake ciki, kamar zautacciya haka take maganganu cikin fitar hayyaci,
Saida ta gama surutanta ta mi’ke da gudu ta fice daga cikin d’akin…
Shi kuwa Junaid duk abubuwan da yake faruwa bai saniba , baya cikin hayyacinsa,
A halin yanzu taimako yake bu’kata
Kuma Ayush ce kawai zata iya wannan taimakon, in har ba itaba ba Wanda zai iya ceton Junaid daga hannun azzaluman Aljanun nan da kuma mahaifinta.
Barin Ayush cikin d’akin falo ta nufa ta kwanta ‘kasan carpet tana rera kukanta mai cin rai, a halin yanzu ba mutumin da Ayush ta tsana kamar mutumin da ya kashe mata mahaifiya,
Kuma saita d’au fansar mahaifiyarta akan sa,
Wato JUNAID………

FREE DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Matar Damisa

The most reliable and easiest way to obtain the completeMatar Damisa Book isto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Matar Damisa Book in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the completeMatar Damisa Book booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.