Download Complete A SANADIN MAKWABTAKA Romantic Hausa Novel PDF

A SANADIN MAKWABTAKA

A heart touching story of Love and Destiny

*Mallakin

*🌹ZAINAB LALUH*📲✍

_~(Oummu imam)~_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

49

Haisam zaune saman kujera L-shape ya dan kishingida jikinshi sanye cikin bak’ak’en kaya jeans da t-shirt gaban rigar anyi rubutu golden colour hannunshi sanye da Agogo golden,tun bayan daya dawo daga aiki wanka kawae yayi ko part d’in Hajiya baije ba yaci abinci ya zauna yana yin video call,yana yin firan yana d’an gutsiran cake dake ajiye gefen laptop dinshi dake kan c-table hannunshi guda na ruke da glass cup mai d’auke da ruwan lemu yana d’an sipping ahankali,
Turo kopar tayi bakinta d’auke da sallama ta shigo,a gefen kujeran ta tsaya idonta akanshi,a hankali ya wurga eyeballs d’inshi kanta suna had’a ido ya d’an yi Murmushi hakan yasa itama tayi mashi,
“Who is dat?” wata zazzak’ar murya daga cikin laptop d’in ta tambaya da alama wadda yake yin video call d’in da itace,maido idanunsa yayi kan screen d’in slowly ya furta”Zarah”yayi Maganar had’i da lumshe ido,
“Oh really?” mai muryar ta tambaya,d’aga mata kai yayi alamar eh,
“I wanna see her,where is she” ta sake fad’a alamar tana son ganin Fatuu,daga yadda take turancin zaka yanke ba bahaushiya bace,kallon fatun yayi yai mata alamar tazo da kanshi,sai lokacin tasa hannu ta cire littafin dake asaman kanta ta d’an matso gaba kadan,da yatsanshi ya nuna mata Laptop dinshi yace”zaku gaisa da ita ne”cikin rashin fahimta tace”wa?”,
wani kallo yayi mata”ki duba inda nike pointing mana” da sauri ta juya ta kalli inda yake nuna matan,Matashiyar budurwa ce da zata iya kai shekara 21 zuwa 22 haka,tana zaune asaman gado ta jingina bayanta da kan gadon,lokacin da Fatun ta kalli Computer d’in budurwar ta juya gefe ta dauki ruwan roba dake aje saman bedside drawer ta daga tana sha hakan yasa bata ga ainihin fuskarta ba sai dai dogon gashinta dake gefe da gefen fuskar ya zuba har kan cikinta wanda launinsa brown ne sosae haka fatar jikinta ma fara ce sosae wanda kallo d’aya zakai mata ka kirata da farar fata,sai dae sam kalar hasken fatarta dana haisam ba iri daya bane kowa da launin haskensa,
Ai Koda Fatuu tayi arba da ita a firgice ta juya ta kalli haisam tace”Ya Handsome da wannan zamu gaisa din?”fuskarshi a sake kaman zaiyi dariya ya d’aga mata kai don yadda ta firgitan taso bashi dariya,
a rud’e ta kuma cewa”to amman ai ni fa ban iya irin turancinsu ba mai saurin nan,ba rannan na fad’a maka ba har kace zaka koya man amman sai ka samu isashshen lokaci to yanzu ya zanyi magana da ita…..”kafin ta k’arasa budurwar ta katseta da fad’in,
“karki damu nima bahaushiya ne ai” yadda tayi hausar gwanin dad’i,da sauri Fatuu ta maida kallonta gareta lokacin ta gama shan ruwa ta juyo da fuskarta sosae,Tubarkallah Ma sha Allah,kallo daya zakai mata ka shaida kyawun fuskarta,kyakkyawa ce matuk’a ga kwayar idonta brown ce har wani kyalli take,waro ido Fatuu tayi tana kallonta arazane,ba kyawunta ne kad’ai ya razana ta ba, harda furucin da tayi na wai itama bahaushiya ce to ta yaya?shine abunda ya tsaya ma fatun arai.
Hannu ta d’aga ma Fatuu”hi,Zarah how’re u?”,
Cike da mamaki fatuu tace”da gaske ke bahaushiya ce?”
“Yeah,kuma ina jin hausa kaman jakin kano ba” tayi Maganar tana dariya haka kuma ba k’aramin kyau ya k’ara mata ba,kan fatuu fa ya Matuk’ar daurewa hannu guda tasa ta rufe bakinta alamar mamaki kafin tace”wai har sunan jaki ma kin sani kenan!”,ba budurwar ba har Haisam dake saurararsu saida ya d’an murmusa,
“Na fad’a maki nima bahaushiya ne ko baki yarda ba,nasan komae ai saboda nima yar Nigeria ne, anan aka haifeni, anan nayi wayo har na girma”,
kai abunfa nayi ne,neman wurin zama Fatuu ta fara don da a duk’e take tayi ruku’u,ganin haka yasa Haisam janye kafarsa daya mik’e kan kujeran ya matsa can gefe,zama tayi sosae tace”to ke wacece,kuma wane gari kike ko ke yar gidansu Ya Handsome ce amman kuma naga ba kalarku daya ba”duk ta jero mata tambayoyin nan,
Murmushi tayi tasa hannunta tana gyara gefe da gefen gashinta kafin ta fara magana”sunana FANAN,ni yar Lagos ne and ni kanwarsa ce but am his Cousin sis kinsan me cousin ke nufi ko?”da sauri Fatuu ta d’aga mata kai”Eh nasani anyi mana shi a English,diya ko dan kanin ko yayan iyayen Mutum”,
“Yeah,You’re right Zarah ni d’iyar kanwar babanshi ce”, cike da mamaki Fatuu tace”wllh nama gane ki,Mamanku diyar Hajiya ce wadda ke lagos kuma Babanku Bature ne ko?” Fanan na dariya ta d’aga mata kai alamar eh,
“To ke yaushe zaki zo nan Katsina?” fatuu ta tambaye,
“Currently now am not in Nigeria,ina India ina karatu,sai dae watarana in nazo” zaro ido Fatuu tayi”India!yanzun nan da nike yin magana da ke kina India?”kai Fanan ta d’aga mata alamar eh,
“To mi kike karantawa anan d’in?”,
“Medicine”ta bata amsa,
“had’a Magunguna kenan?”,
“No,karatun likita kenan”,cike da mamaki Fatuu ta ruk’e baki tace”kai ashe wai shine Medicine,shifa nike son in karanta amman bansan sunan karatun ba kenan,ni karatun Doctor kawai nike cewa”,sosae Fanan d’in ke dariya jin shirmen Fatuu nan suka shiga yin hira sosae atsakaninsu da alama itama Fanan d’in bakinta asake yake har Fatuu na tambayarta wai tana zuwa wurin yan Film d’in suburbud’a dasu Sharukhan,tace mata a’a ai Karatu ne ya kawota amman dae wani lokacin suna ganin yan Film d’in in sunzo makarantarsu shooting ko akan hanya ko a Mall in sunje Shopping da dae sauran wurare kaman wurin shak’atawa haka,anan Fatuu ke ce mata wai in zata zo tayo mata tsarabar sari amman ba wanda ake nad’awa ba wannan kada ita zai rink’a yi irin masu wando take so irin wanda Roshni d’in Aman na cikin film d’in Shu’umin iko take so,nan Fanan d’in tace mata bata gane irinsu ba don ba kallon film d’in take ba,Fatuu tace mata in anayi a tauraruwa zatasa Ya Handsome ya d’auki hoton irinsu ya turo mata tace to,daga haka Fanan d’in tace mata zata tafi tutorial yanzu sai wani lokacin zasu sake gaisawa Fatuu ta amsa da toh,
“Beb where are u?” Fanan ta fad’a tana d’an kallon gefen Fatuu,Haisam na jin hakan yayi ma Fatuu alamar ta juyo mashi da Laptop d’in,kallonta yayi fuskarshi da Murmushi itama Murmushin take mashi tace”I will be offline now so u can have more time wit ur Funny Mom”lumshe ido yayi still da Murmushi akan fuskarshi slowly ya furta”Ok,Bye Sweethrt”,
“Bye Beb”ta d’an ja Maganar daga karshe had’i da yin kiss daga haka ta sauka,waro ido Fatuu tayi tasa tafukan hannayenta duka biyun ta rufe baki alamar mamaki tana kallonshi,kallonta yayi,ganin abunda tayin yasashi cewa” What?”
cire tafukan tayi tana d’an murmushi tace”Nagane Budurwarka ce,amman shine kace man baka da Budurwa ko” ta k’arasa tana tura baki tana yi mashi wani kallo irin ya raina mata wayon nan,
Murmushi yayi yace”Who told u dat?” tana tura baki tace”ba gashi nan kace mata Sweethrt ba kuma tayi maka…” kasa k’arasa Maganar tayi tana guntse dariya,shiru yayi yana kallonta still da Murmushi afuskarshi,ita kuma sai faman guntse dariya take,
Sigh yayi”ai wannan duk wanda ka damu dashi who is important to u zaka iya ce mashi hakan ba sai wanda ake Soyayya dashi ba” daina yin dariyar tayi tace”da gaske?” gira ya d’aga mata”yeah,kaman Grandma d’inki da Uncle d’inki duk zaki iya ce masu hakan is normal”,cike da mamaki tace”ashe ba dole sai wanda ake Soyayya ba?”kai ya d’aga mata kafin ya kuma cewa”Mutum mai kirki ma zaki iya ce mashi hakan,kaman wanda yayi maki wani abu kika ji dadi” zaro ido tayi “to kuma in Namiji ne kada yayi tunanin sonshi nike fa”,hannu yasa ya shafi forehead dinshi”ai zaki ce ne yadda zai fahimta kaman kice,u’re such a Sweethrt”dariya tayi tace”Ya Handsome u are such a Sweethrt” shima dariyar yayi har hakoransa suka bayyana ya furta”thanks,har kin gama fushin dani kenan” turo baki tayi”ai na kyaleka kaci gaba da cin abunda ka saba”,
“Kin daina damuwa da Ulcer zai kamani na mutu kenan” d’an yamutsa fuska tayi”to ai tunda su ka saba dasu kilan kana koshi ko,kuma koma na matsa ma ba bari zakai ba” ta k’arasa da sigar shagwa6a,d’an ta6e baki yayi kafin ya kai hannu ya d’aukko sauran cake din da ya aje agefen Laptop,har yakai baki zai gutsira suka had’a ido hakan yasa ya dakata don baida sauranshi da zai bata,mik’a mata yayi ta kalli cake d’in ba tare data amsa ba hakan yasashi cewa”take”maimakon ta amsa d’in sai ta turo mashi baki tace”Nima bancin sauran wani”,
waro ido yayi lokaci guda ya gane Magana ta gaya mashi,wato abunda ya fad’i mata rannan data bashi ice cream acikin motane itama ta gaya mashi yanzu,ganin yadda yake kallonta yasata fashewa da dariya tana rufe bakinta da hannunta,aikuwa baisan lokacin da ya dauki throw pillow dake a gefenshi ba ya jefa mata a fuskar,dukar da fuskar tayi tanata dariya kitsonta ya zuba yaraf akan kujeran,still yayi yanata Murmushi shima,can ta d’ago ta mik’a mashi hannu alamar ya bata,shiru yayi yana kallonta kaman bazai bata ba sai kuma ya mik’a mata ta amsa tace”thank u Sweethrt ya Handsome”dariya yayi ya d’an girgiza kai kawae ita kuma ta fara cin cake din,
“Mi yasa kike fitowa haka,where is ur headtie?
” yayi mata tambayar had’i da dan kwantar da kanshi jikin kujeran,sai lokacin ta tuna da abunda ya kawo tan,baki cunkushe da cake tace”ba kawu Amadu bane ya biyo ni zai bugeni shiyasa ban koma na daukko kallabin ba”,
“Mi kika yi mashi?” idasa cinye cake d’in tayi sannan ta fad’i mashi abunda ya had’a su,idonshi akanta yace”har yanzu kina rashin kunya ko Zarah!”ta6e baki tayi kaman zatayi kuka”to ya kasa yi mun kuma maimakon ya barni inji da abunda ya isheni sai yake ta man maganganu ni kuma naji haushi bansan lokacin dana fad’i mashi hakan ba wllh kaji na rantse,amman bazan k’ara ba” ta k’arasa maganar tana d’age baki had’i da jujjuya kai alamar nadama,still yai yana kallonta ya d’an 6ata fuska,ita kuma sai sussune kai take,
Sauke ajiyar zuciya yayi yace”Let me see d Assignment ” aikuwa da sauri ta juya gefenta ta d’aukko littafin,mik’a masa tayi bayan ta bud’o daidai inda tambayar take,hannu yakai ya amshi book din,
“Wai wannan tambayar za’a fidda kuma ga amsar da yake so asamo nan a k’asa wai in batayi irinta ba to ba’ayi daidai ba”,shiru yayi yana kallon Assignment d’in can k’asan mak’oshinshi ya furta” CALCULUS” janye littafin yayi ya kalleta da mamaki”Ajin ki nawa kika ce ma?” da sauri ta bashi amsa”Js 3 nike kuma ban dade dana shiga bama” d’an jinjina kai yayi ya k’ara d’aga littafin yana sake kallon question d’in,yasan lissafin sosae tun yana 100lvl yake yinshi,yana da wahala amman awurin wasu don shi lokacin yana degree d’insa na farko yana koya ma mutane shi sosae wadanda basu ganewa in akayi masu,yayi mamakin ganin tana js 3 an bata shi, dama a Senior Secondary take anayinshi a Further math ga wad’anda suke yin Subject d’in shima kuma wanda ake yi masun introduction ne ba’a nitsa masu can ciki don lissafi ne mai rikitarwa sosae gashi yana da yawa,
“Mi kika yi aka baki wannan Assignment d’in?” ya tambayeta fuska a d’aure,nan ta fara inda inda tana zaro ido ba abun tayi mashi karya ba don ta fahimci ya gane laifi tayi,
“Am asking u Zarah!” ya d’an yi mata tsawa aikuwa a rud’e ta fara kora mashi bayani bata 6oye mashi komai ba,tana gama fad’i mashin kwalla suka zubo mata sharrr,shiru yayi baice mata komae ba,a zahiri ta wani 6angaren tana da gaskiya yadda ya rikesu tsawon lokaci dole su gaji kuma dama lissafi in rana tayi
ba kowa ke fahimta ba shiyasa mafi akasari aka fi sa period dinshi da safe,ko kuma ana dawowa break kaman yadda tashi take sai kuma ya had’e masu da double periods d’in malama dole ma su gaji ai,matsalan yadda Fatun tayi Maganar dole zaiga tayi mashi rashin kunya,
“Ke kad’ai ne ajin?” haisam ya tambayeta,girgiza mashi kai tayi idanunta sunyi rau rau,
“Ke kika fi kowa rashin kunya kenan”, da sauri ta k’ara girgiza kan tace”a’a wllh nifa bada niyyar rashin kunya nayi Maganar ba,kawae gaskiya na fad’i mashi don ya sani”shiru yayi yana ta kallonta fuskarshi still a d’aure hakan yasa ta sunnar da kanta k’asa tana ajiyar zuciya,
Sigh yayi”as from today,i don’t want u to dat again,ba ko ina mutum keda right na ya fad’i abu ba koda yana ganin yana da gaskiya hakan na iya zama ma mutum matsala like it happens to u now,ki koyi yin shiru understand?”,
da sauri ta d’aga mashi kai”to ya Handsome wllh bazan k’ara ba”,jinjina kai yayi yai shiru yana d’an tunanin yadda zai solving mata don lokacin Sallar la’asar ya riga yayi gashi sai dae ya hakuri da zuwa gym don ko zata fahimta sosae har ta yi bayani a aji sai an d’auki d’an lokaci,ana haka aka fara kiran sallar la’asar mik’ewa yayi tsaye yana gyara rigarshi Fatuu ta d’aga kai tana kallonshi,
“Zanje sallah sai na dawo zan nuna maki yadda yake”,jin haka yasa lokaci guda ta saki Murmushi,hanyar Bedroom dinshi ya nufa yana shigewa ta hau yin murna tana bubbuga kujeran kaman sabon kamu, bayan wani lokaci ya fito lokacin ta natsu har ta kwanta ma asaman kujeran,tana ganinshi tayi saurin mik’ewa zaune yana zuwa zai wuce yace”ke bazaki sallan bane?”tana kallonshi tace” to ai banda Hijabi”
“Kije wurin Hajiya sai kisamu kiyi sallan inna gama zanzo nan” amsawa tayi tare da mik’ewa tabi bayanshi,
_________________
Lokacin data shiga parlon hajiyan ba kowa aciki hakan yasa ta nufi dakin Saude don tasan Hajiyan Salla take,da sallama ta shiga cikin dakin lokacin Sauden na niyyar tada salla,juyowa tayi ta kalli bakin kopan shigowan tana ganin fatuu ta saki Murmushi,
“Fateema ce”
“Eh Aunty Saude ina yini”
“Lafiya lou ya Makaranta an dawo ko”,
” Eh,Don Allah hijabi zaki ban zanyi salla”,amsa mata tayi da to ta nufi wardrobe din bango ta d’aukko mata wata wadda take tunanin bazata yi mata yawa ba sosae ta aje mata agefen Katifarta don fatun ta riga ta shige toilet.
A tare Haisam da Hajiya suka shigo parlon sai kace tare suka je masallacin,yana ganinta ya sakar mata Murmushi ya nufeta,hannunta ya kamo suka nufi kujera 3 seater ya zaunar da ita kafin shima ya zaunan,
“Sai yanzu kaga damar shigowa bacin tun d’azu kana gidan nan” yana niyyar bata amsa Fatuu ta shigo cikin parlon ta nufi kujera one seater ta zauna tana yima hajiyar Murmushi,
“Ke kuma yaushe kika shigo?” gaidata ta fara yi kafin tace”da aka fara salla”,
Kai hajiya ta d’aga sai kuma tace”yau baki zuwa islamiyya ne kuma ina kallabinki?”amsa ta biyun ta bata tana tura baki”ban zo dashi ba,kawu Amadu ne zai bugeni shine na taho haka”
“Laifi kikai mashi ko” shiru bata ba ta amsa ba hakan yasa Haisam fad’i mata laifin data yi mashi,girgiza kai hajiya tayi”Fateema hoo,baki dai daina rashin ji wllh,Allah ya shiryeki”maida kallonta tayi kan haisam tana yar dariya”kace yau ba zuwa d’aga karfe kenan,yar gidanka ta jawo aiki,Allah ma yasa kai ka iya ai da tasha punishments ja’ira”ta k’arasa idonta akan Fatuu tana dariya itama dariyar tayi tana sunna kai k’asa,
“Ko har kayi mata ka fitan?” hajiya ta tambaya jin baice komae ba,
“No,we need enough time,zanje Gra after magrib sai inyi acan”, kai hajiya ta d’aga”wannan abu dae shima kaman shaye shaye yake ace dole sai mutum yayi zai jishi daidai ya zauna lafiya”wani kallo yayi mata ba tare da yace komae ba,
“a zubo maka Abinci ne ko yau ma yar gidan taka tasa kaci Abinci awurin aiki?”da sauri Fatuu ta d’ago ta kalleshi lokacin shima ya d’an kalleta suka had’a ido ta tura mashi baki,d’an murmushin gefen baki yayi ya janye idonshi Hajiya dai nata murmushi,
“Yanzu nagama cin abu,amman zanci bada yawa ba”, Saude hajiya ta kwala ma kira,bayan ta fito ta bata umarnin kawo mashi Abinci,kallon Fatuu tayi tace” ko kema zaki ci?”kai ta d’aga mata alamar eh dama kuma bata wani ci abincin kirki ba,
“bi Sauden kice wai ta zubo harda ke acikin nashin sai kuci tare” amsawa tayi da to ta mik’e ta nufi kitchen d’in,shi dae Haisam shiru yayi bai tanka ba dama Hajiyar da biyu tayi hakan wai ko yaci sosae,bayan ta kawo abincin tashi Hajiya tayi ta koma saman 2 seater tace ma Fatun ta zauna sai su saka abincin a tsakiya,yin yadda tace tayi,ganin Haisam d’in idonshi na akan waya ahankali tace”Ya Handsome ga abincin”ba tare daya kalleta ba yace”ki ci” k’in ci tayi ta bishi da ido fuska a daure alamar fushi can ya d’an d’ago ya kalleta ganin yadda tayi yasashi d’an yamutsa baki ya kai hannu ya d’auki spoon d’in ya fara ci,sai lokacin itama ta d’auki nata cokalin ta fara ci,abun mamaki,in yaci sai taci,in ya tsaya sai ta tsaya itama,duk wannan abun hajiya dake kallo na satar kallonsu sosae abun ya bata dariya amman sai tayi kaman ma bata san abunda suke ba,ganin zata 6ata mashi lokaci yasashi aje wayar ya maida hankali kan abincin,ba 6ata lokaci suka kusa cinyewa ya aje spoon d’in tana niyyar ajewa ya wurga mata wata uwar harara hakan yasa ta idasa cinyewa,
Mik’ewa yayi “ki same ni can” yace mata daga haka ya fara k’okarin nufar hanyar fita daga parlon,
“Ba za’ayi anan ba nima in koya” Hajiya ce tayi Maganar cike da zolaya,
“Yana da d’an yawa we need to do it on board” ya bata amsa yana tafiya,mik’ewa Fatuu tayi tana niyyar d’aukar tray d’in da aka d’auro kayan abincin ta kai kitchen,
“Ki barshi za’a d’auke kije ya koya maki yamma na yi” amsawa tayi da to tana niyyar juyawa Hajiya ta kira sunanta,amsawa tayi tare da kallonta,
“Badai zaki daina rashin ji ki natsu ba ko Fateema!” fuska a Matuk’ar d’aure tayi Maganar, nan da nan Fatuu ta rud’e ta nufi gabanta ta duk’a”Don Allah Hajiya kiyi hakuri wllh na daina ko rannan saida Gwaggo ta fad’i hakan yanzu ba ruwana da kowa”,
“Amman ai har yanzu kina rashin kunya ko tunda gashi kinyi ma kawun ki da Malaminku”,idonta cike tabb da kwalla tace” shi Malam wllh bansan rashin kunya bane nayi tunanin gaskiya ce na fad’i mashi amman Ya Handsome ya man fada yace in rinka yin shiru,shi kuma kawu Amadu raina ne ya 6aci da baiyi man ba kuma yana ta yiman fad’a,amman wllh tllh kinji na rantse bazan k’ara ba”,sauke ajiyar zuciya tayi”in kika k’aran fa mi zanyi maki?”da sauri tace”komi”jinjina kai tayi tace”tashi kije” mik’ewa tayi tana goge kwallan da suka gangaro mata ahaka ta fita daga parlon…..

FREE DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete A SANADIN MAKWABTAKA

The most reliable and easiest way to obtain the complete A SANADIN MAKWABTAKA isto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete A SANADIN MAKWABTAKAin Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete A SANADIN MAKWABTAKA booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.