Download DOCTOR ESSHA Hausa Novel Complete PDF

DOCTOR ESSHA is a popular Hausa novel that tells the story of a young woman named Eesha who falls in love with a man named Aliyu. However, their love is threatened by various obstacles, including family conflicts and societal expectations. In this blog post, we will provide information on how to download the complete PDF version of DOCTOR ESSHA Hausa Novel.

DOCTOR ESSHA

By J hajara

25..

Tycoon ya nemi guri ya zauna a gefeshi ya kalli fawaz yace” Doctor yajiki nashi?
Fawaz ya su sa Kai yace” da sauki dad.gani sauki ne shiyasa aka canza mishi room.
” Ya farka dai ko ? Mami ta tambaya
Yace” eh mami ya farka around two na dare, sai sambatu yakeyi Yana Kira suna dai Essha, shine kawai mikamishi allura bacci, inshallah na bada jimawa ba zai farka”
” Inalilahi waina ilaihi raju’un, Essha Essha haba haba, wanan Essha mutum ce ko aljan da zata adabi rayuwa dana” Mami ta fada ta rike Kai ta fashe da kuka..
Suleiman dake gefe ta ya Mike ya dafata yace” Mami ba kuka zakiyiba, addu’a zakimishi, Allah yabashi lafiya, yanzu Yana farkawa yaji kina Kira suna Essha Dina Kara rikecewa zaiyi”
Mami ta hada hannu ta na addu’a Tana haweye tace” Allah ga Dana na, ka. Fitar da shi daga ciki wanan hali dayake ciki, Allah na rokeka” suka amsa da ameen, suna amasawa sukaji an bake kofa anshigo bako sallama, suna daga Kai sukaga suhaima ne, dogo riga ne a jikita na atamfa ta cugale dauri dankwali bako mayafi s jikita, car key ne da waya a hannu ta kirar iPhone 11 pro max, Suleiman na gani itace ya baka mata harara, ya Mike ya fice, saura ma suka bi bayashi, don bakarami haushi ta sukeji ba, toh su San hali, ita kam ko ajikita kallo sama da kasa ta binsu dashi taja tsaki.
Suleiman suna yaja tsaki yanemi guri ya zauna yace” wlh I hate this girl, gsky an cuce Buddy, yariya batasan daraja mutani ba, Mai karanci addini” ya Kara ja wani dogo tsaki..
Hafiz yace” Nima ko kallo ta basanyi Mai Kama da sisiya, wlh ko a office ko kallo Bata isheniba, Allah ancuceshi , dubeta ma Kama kara, Allah yasa ma aljanana Essha Dina , aljana ce dagaske, Allah zan iya biyata tayimin maganita yariya ba tarbiya kawai (lolz kuji Hafiz fa).
Haydar yace” Kuna ma da lokaci ta kenan bara kuga hoto da ta daura a page nata na Instagram guri misali karfe 3 na dare fa” ya ciro wayar shi daga aljihu Yana nunamusu hoto suhaima, suhaima ne zaune a club, su hudu itace kawai mace a ciki su, tasa dogo riga ne a cikita ya matse ta sosai ko rabi cinyar ta baiyi ba, fixing da tayi na attach duk ya barbaje tukunyar shisha ne a gabansu, tana tsakiyar maza, hayaki take fesowa cike da korewa a fuska yan samarin.
Fawaz ya ja tsaki yace” tir da hali iri nata, ni narasa dalili da yasa for the first place daddy ya Amince da aure na, wlh da abani irita guda goma goda aban Yar karkara wancan batasa komai ba” duk suka fashe mishi da dariya..
Hafiz yace” ahaf Kar kudamu nasan buddy zaiyi maganita, zanta gane kureta, Allah sarki buddy yaro kirki Allah yabaka lafiya” suka amsa da ameen..
Ciki daki kuwa, suhaima Chewgum take fasawa fas fas kas kas batama San da su Tycoon a daki ba, hankali ta na waya tana chatting, yantsu zaro zaro yasha pink artificial nails, Mami sai binta take da kallo mamaki, Bata cemata uffan ba, ita akullum tir takeyi da Wana Hadi aure batasan maiyasha kan maigida nata ba da ya nace sai ya aura ma Aliyu Wana gataleliyar, kwanaki baya har batawa sukayi akan magana aura Ammi ne tabata hakuri tace su zubamishi idon Allah yasa haka shine mafi alkhari..
Mami ta tabe baki ta bita da kallo.. Tycoon yace” a’a daughter welcome ga guri ki zauna”
Suhaima har ta Dan firgita da taji magana ta daga Kai suka hada Ido da tycoon ta saki murmushi tace” good morning Dad ” a tsaye ko ta Dan ragwafa.
Yace” morning daughter ga Mami ki ” ta juya ga kallota ga inda yanuna mata, Mami sai binta take da harara kamar idon zai fadi.. na take taji shakku Mami ta sukunyar da Kai tace” good morning ma”
Mami ta amsa fuska a hade ta kauda Kai..
Suhaima Sumi Sumi taja jiki zuwa gefe Aliyu tace” dad ya Mai jiki?
Ya amsa da sauki Yana shafa kafa Aliyu, yana shafa kafa kuwa, kamar ace ma Aliyu ya farka, ai da sauri Mami da Tycoon suka Mike , Tycoon ya rike hannu shi Yana murzawa yace” Aliyu bude Idonka kaji “
Aliyu dayayi kamar zai bude sai yakara lumshe dasu, har yazo yabudesu gabadaya..
“Aliyu, Aliyu ” yaji daddy shi na Kira, bai iya amsawa ba, ya yinqura zai tashi Tycoon yayi sauri taimaka mishi ya zauna yace” son sannu yajiki? Bai amsaba ya binshi da kallo yasoma motsa baki yanasa yayi magana ama yakasa. Mami ta rike mishi hannu tace” boy badai jiki bane ko?
Kamar ansashi magana dole yasoma magana a rarabe yace” da…ddy m..ami, kun..gan..ta, kug…amin Essha na”
Tycoon yace” subhanallahi, Aliyu ba kabar magana Essha Dina ba?
Ya dafa saiti zuciya shi yana cewa” daddy zuciya na zata buga da Allah ka taimakeni kanemo mi Essha, daddy imbahakaba wlh zaku iya rasani” da sauri Mami ta rugumeshi tana shafa bayashi Alama rarashi tace” boy kadaina fada haka, kaji ko, take it easy, ba abunda zai saimeka, this Essha you are talking about , we don’t even know whether ita mutum ce ko aljan, I probably guess ita jinnu ce, don inba jinnu ba, babu mahaluki da zai’iya rayuwa a ciki wanan daji, ka Manta da ita kaji ko”
Ya girgiza Kai yana haweye yace” no Mami bazaniya mantawa da itaba, she’s my wife, my happiness” Mami kalloshi ta tsaya Yi ta mamaki dan nata, daga jiya zuwa yau duk ya canza ya birkece aka mace, har da kirata matashi, Kai gaskiya na yarda Wana aiki jinnu ne…
Suhaima dake tsaye taji duk kalamai Aliyu kefada ai sai ta tsandare a guri, zuciya ta yayi baki,tasoma fitar dawani haweye Mai zafi , ranta yakai kololuwar baci, tanuna kanta” wato ma Aliyu wata yakeso baniba , dun su Raina min hankali shine sukece aljana ce,har dawani kirata my wife my happiness,kan burar ubancan, wlh ko waye ita saita gane kurata” ta fice a daki a fusace..
Su Tycoon ma hankali su baya kata, basumasan ta fice ba,
Aliyu ya rike hannu daddy shi yace” please dad ka taimakeni”
Yawun Mai daci Tycoon y hadiye ya dora hannushi a sama gashi kan Aliyu yana shafawa har sanda ya daina kuka sanan yace” Aliyu kayi hakuri, dakai fa mukaje nemamta bamuganta,mu nemata murasa, Kai bana tunani ma akwai wani dan Adam dake zama aguri, inason ka dauka cewa faruwa haka daga Allah ne, yayi hakne don ya jarraba Imani ka, na tabbatar idan kayi hakuri wata Rana zai zama labari”
Yajijiga Kai yace” no no daddy bazai iya jurewa ba, daddy she’s hurt, tana bukatar taimokona, nasan duk inda take hankalita yafi nawa tashi, daddy help me please “
Tycoon yaja numfashi yace” kayi hakuri mana Aliyu be strong”
” a’a daddy bazaiyab, Ina ratsa ta, na ratsa fariciki na, she’s my first love, daddy bazakara samu wani fariciki ba, inhar Essha Bata tare dani”
Tycoon yace” haba son , zaka samu fariciki inshallah fiye da kake zato, nasani wanan duk abunda kake na dan lokaci ne da an daura aureka da suhaima shikena zata mantar da Kai so called Essha”
” a’a daddy I can stop loving Essha, sonta a jinina take, Kuma bazata ba so wata baya ta ba, zan auri suhaima ne kawai saboda …..
Mami ta katseshi tace” ya’isa boy don’t talk again, bakada isheshe lafiya “
Yace” daddy promise me Ina warke zaka barni naje nemanta, da Allah daddy promise me that, daddy dun girma Allah kada kace aa “
Tycoon ya sauke nannauyar ajiya zuciya yace” na Amince maka, ama da sharadin…
Ya zabura yace” daddy shara din daka gindayamin zanbi “
Tycoon yace” akodayaushe in zaka fita, zaka Riga fita da masu tsaro lafiya, sama da ashiri, ka Amince?
Ya sukunyar da Kai kasa gsky baiji dadi wanan sharadin ba, ama ya zainyi, dole zai Amince sbd ya nemi sanyi idanuwanshi, yadaga Kai yace” na Amince dad”
Tycoon yasake cewa” kuma duk abunda ummi zata daura ka akai, Kar kamata musu” Aliyu ya kalli mami yasake kallo daddy shi, fuska shi da alamu tambaya ama sai Bazar dun haushi ummi yake ji, ita tafara Kira Essha da aljana..
Murya ciki sanyi yace” na Amince”
Tycoon yace” yawwa good boy, yanzu Bara na Kira Hafiz su zo su taimaka ma , kayi wanka ka Rama salloli dake kanka “
Yace” zaniya daddy”
Mami tace” a’a boy Karka yi musu, jiki ja ba karfi..
Prince neh

DOCTOR ESSHA

By J hajara

22…

Aliyu yasa ihu kamar ba shi ba yarike hannu Ammi yace” No*3 Essha na ba aljana bace, mutum ce, Ammi ki yardadani… Ya rike Idrees Yana girgiza shi yace” Bro kaima ka yarda kenan cewa Essha na aljanace, a’a ya kadan kai” Bro please Kar ka yarda da batu ummi please…. Idrees rasa baki magana yayi Yana binshi kawai da ido yaje…
Yaje gaban tycoon yace” Daddy zo na kaika ka ganta, kaji dad don’t say no please ka biyoni, please dad my heart is burning, in bagantaba zuciya na tarwasewa zaiyi , please dad ka ceceni” ya kife Kai a kirji tycoon yana kuka Mai cike da kunci,
Tycoon yace” calm down nayarda zan bika kanuna mi ita, if dat is d solution”
Yadaga da sauri Yana murmushi yace” dagaske dad” Tycoon ya lumshe minshi idon sanan yace” amafa zaka Bari sai gobe, kaga yanzu baka da lafiya”
ya Bata fuska yace” no daddy dat place it’s not safe, za ta cutu aguri, Kuma dad na warke muje kawai”
Ya jijiga Kai yace” son yanzu dare fa yasomayi”
Ya shagwabe fuska” daddy muje yanzu if not za’a cutar da ita”
” Toh Aliyu muje”
ya rugumeshi yace” nagode dad”
Tycoon yace” u r welcome boy, can do anything for you….
Ummi matsifa takeyi wai anki yarda da zanceta, gashi yanzu ya biye mishi har da wani zuwa a dubata tace” wlh Nima sai na binsu Naga wanan ya Mai suffar aljanar na inhar dagaske ke ne”
Tycoon yasa aka Kira doctor yamishi bayani komai, doctor yace” ba matsala sir sai ku dawo”
Duk family su yake za su bisu, fawaz, Hafiz haydar Allah Allah suke suga yariya da ta ruda musu da aboki haka.. ajere motoci kuda takwas, manya manya Jeep ne, Aliyu dakanshi yake driving ,ayi ayi driver ya yi driving yaki, yafadi suna anguwar yace” baisaniba”
Shidai kawai abinda yasani zai kaisu guri Essha, su hudu ne a ciki motar daya, tycoon, mami, Ammi da oga boss din dake driving, saura Kuma su fawaz, su ummi siyama da su Idrees sai guda biyu Kuma bodyguards ne ke biye dasu..
Aliyu sai sharara gudu kawai yake , Mami suyi shiru suna kallo iko Allah, har su fara fita gari, da’a Ammi ta tambeya shi” Aliyu ba’akai bane?
sai yace ” mun kusa”
Su matukar tsorata dasu ka ga Aliyu yayi corner ta hanya daji, ama duk suka zuba mishi na mujuya ba Wanda ya’ iya cemishi ko da ka’ala.. har sanda ya tsayar da motar a ciki tsakiyar daji, ya Parker ya fito yace” dad, Ammi Mami kifito nane , duk suka bude suka fito..
Sofia da rahma su tsorata daji yanda daji yake motsi, don ba alamu wani Dan Adam na rayuwa a ciki, Kara tsutsaye ne kawai da macizai da abubuwa da baza arasaba ke tashi, gashi yayi dulum dulum..
Ai da gudu suka rugume Ammi, su ka kakemeta..
Ummi da siyama sai Bari..
Ammi tace” Auzibillahi, Aliyu Ina ka kawo mu Kuma?
Tycoon sai bin daji yake da kallo, Yana mamaki yanda Aliyu yasan daji, don daji Mai hatsari ne ba kowa bane keshiga, sai ka shirya kanka…
Aliyu yayi murmushi” yace Ammi Essha na ana take, tana can a bukka kuzo muje”
Wa?!!! Hafiz da Isa har suna hada baki.. Hafiz yace” gaskiya badaniba” da gudu suka shiga motar suka rufe ..don daji ya matukar Basu tsoro..
Isa yace ” gaskiya batun hajiya gaskiya ne da tace Yaya da aljana yayi gamo”
Suleiman don tu fitowar daga motar jikishi ke Bari saban tsorata yace” buddy kana nufi kenan ana ku ka hadu? Yayi tambaya har muryashi na rawa.. Aliyu ya gada Kai alama eh Yana murmushi…
Suleiman yace” lallai da sake, Kai badaniba” ya make a baya Aliyu yace” Buddy su San ka baza su cutar da mu ba”
Aliyu ya Bata fuska yace” Mai kake nufi??
Yace” su suke gani mu ba mu muke gani su ba, shiyasa na boye a baya ka Koda wani abun zai faru, kaga su Saba da Kai , Kuma na ga baka tsorata ba” ya Kara noke fuska a baya Aliyu..
Siyama tace” gaskiya shi ne Yaya, tsoro na keji da Allah kuzo mu bar na guri tunkafi dare yayi ko ummi?
” Eh mana, da Allah umaru kuzo mubar daji na tunda wuri, gashi ma ba ko haske… Mami kam kasa magana tayi..
Tycoon yace” ku natsu mana aduba, Bari a kunna haske”. Ya umarci driver’s da su Kuna fitilu motoci.. duka Jeep takwas a kunna fitilolusu, farare kal kal, ya haske guri gabadaya, ya kalli Aliyu da duk jikishi yagama sanyi yace” son Ina take?
“Daddy a can ne, zo mu karasa ” ya furta murya a sanyaye… Ya jasu suka Kara sa dai dai spot din da abun ya faru, ama ba Alama wata bukka a guri, kamar ba abunda aka taba ginawa a gun..
Aliyu ya rikice ya daburce sai zangaya wuri yake Yana” wlh daddy ana ne, daddy bataa, su dauke ta, daddy ka taimakeni 😭 ummi Mami Ammi wlh ana Essha take, ana aka daura Mana aure, my heart is bleeding ya rike sai tin zuciya shi, ya saki ya da fe kansa da hannu bibibbiyu Yana gani komai da ke daji Yana juya Masa, numfashi sama sama ya ke fita, a hankali ganishi yayi rauni , idanuwansa suka rufe ruf ruf Nan ya sulale ya fadi kasa….
Da sauri wani guard ya sukeceshi , tycoon dakeciki tashi hankali da gani hali da Aliyu yake ciki murya na rawa yace” sanshi a motar Abuja zamu koma, da sauri suka tada motoci, Idrees ya zauna a mazauni driver Yana driving dinsu Ammi, hankali su duk a tashe yake, Airport suka wuce, ambulance aka kira da sauri akasa ma Aliyu abun numfashi akasan Masa don ceto rayuwarshi. Baya jirgi ya daga, suka sauka a Abuja, motar asibiti fawaz yakira suka duguma sai asibiti, family din tycoon suga tashi hankali dun Dakar aka ceton Rai Aliyu, kwana shi nagaba, a ICU ROOM aka ijeshi, bamai shiga sai dai su hangoshi ta window glass din kofar daki, duk ya rame a lokaci daya, yakara haske fayau sai hanci…
Fawaz ya fito Yana sharce gumi duk jikishi yayi sanyi yace” daddy kuje gida mu zamu kuladashi inshallah, kusamu ku huta kodan lafiya ka”
Idrees yadafashi yace” daddy you always encourage us da muriga juriya baikamata ace kanuna kasawaka ba, Yaya zai samu sauki inshallah,.kayi hakuri muje gida ka huta, kaga yadda Yan news suka taru a baki gate, nasan damuka zasuyi”
Tycoon ya gyada Kai Yana haweye yace” muje ku”
Mami tace zata kwana ita..
Siyama tace” haba Mami kiyi hakuri Yaya ba’abunda. Zai sameishi , gasu yaya haydar zasu kuladashi”
Mami Taki fiti fiti, Dakar siyama da Isa suka convienceing nata tabisu, su Rahman har su fara bacci.. suna kaiwa gida acikisu babu Wanda ya iya bacci, Tycoon kwana sallah yayi Yana roko ubangiji ya fitar da danshi daga ciki Wana hali, hk ma Ammi da Mami
Prince neh

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.