Download A SANADIN MAKWABTAKA Hausa Novel Complete PDF

A SANADIN MAKWABTAKA is a popular Hausa novel that tells the story of a young woman named Aisha who falls in love with a man named Aliyu. However, their love is threatened by various obstacles, including family conflicts and societal expectations.
In this blog post, we will provide information on how to download the complete PDF version of A SANADIN MAKWABTAKA Hausa Novel.
*_💖A SANADIN MAKWABTAKA💖_*
_*(Love and Destiny)*_

_*BY ZAINAB LALUH*_🌹
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
*4️⃣6️⃣*
…….
Suna shiga ta cikin gate d’in fatuu ta kalleshi,”lah Ya Handsome ashe da gaske kasan makarantarmu ɗin” Murmushi yayi baice mata komae ba yana ci gaba da shiga cikin Makarantar gaba d’aya hankalin Mutane ya dawo kan Motar ba kamar Students dake ta faman shigowa,
“Yauwa Ya handsome wannan gate ɗin na farko ne section dinmu”,
Juya kan Motar yayi yai horn don a idasa bud’e mashi d’ayan 6arin gate d’in,lek’owa Maigadi yayi koda yai arba da Motar da tai horn d’in da sauri jiki na kerma ya shiga bud’e d’ayan side d’in don a zaton shi Babban bak’o ne yazo Makarantar kamar yadda aka saba yin Manyan Baki,kutsawa yayi cikin Makarantar ya nufi gaban Admin Block inda akai parking wasu motocin ciki harda ta Principal ya parker shima ba tare da ya kasheta ba,
kallon fatuu yayi tare da lumshe ido”here we come”,calmly yayi maganar,
yar dariya tayi ta kai hannu ta ɗauko jakarta dake aƙasan seat,
“Zarah”taji ya kirata,
kallonshi tayi,wallet ce ruk’e a hannunshi ya fiddo 1k yana miko mata,
“Ta micece Ya Handsome?” ta tambaya ba tare data kar6a ba,
“Ba ki yin break ne”,
“ina yi,amman gwaggo ta bani ai kud’in break d’in”
“Ok,ki ƙara”,
zaro ido tayi”ai wanda ta bani fa zasu ishe ni,in na amshi wannan bansan ya zanyi da ita ba”,shiru yayi yana kallonta yayin da itama take kallonshi,
“Owk ki amsa sai ki biya kuɗin friend ɗinki da kika kashe mata”he said calmly,
“Wai kana nufin kud’in da na siyo maka fruit?” kai ya d’aga mata alamar eh,
wani kallo tayi mashi”kam kenan kai zaka biya kud’in abun ciwon naka kuma”
“Ai ba wani abu bane nasan ke kika siya man am grateful for dat,wannan na baki ne kyauta sai ki biya”,
wani kallo take mashi a shagwa6e tace”ni dae gaskia ban yarda ba Ya Handsome Allah wayau kake son yi man,salon kayi man gorin kai ka biya abun ciwon dana kawo makan”,
Haisam baisan lokacin da ya saki dariya ba jin abunda ta fad’a ya d’an juyar da kanshi,kallonta ya sake yi still yana dariyar,ita kam Fatuu sai binshi da ido take don ba k’aramin kyau yake yi ba in yayi dariya har jerarrun fararen hak’oransa suka bayyana,ko dan bai cika yi bane,
“Do i look like wanda zai maki gori?”,kai ta girgiza masa alamar a’a,
“to ki amsa ba zan maki ba ai baida kyau”,
“kayi Alkawari?”kai ya d’aga mata,
“To ka rage kud’in sunyi yawa sosae don har na tara 150 sauran 100 zan cika”, hannu yasa ya shafi beard d’insa kafin ya mayar da 1k d’in cikin wallet ya zaro 500 ya mik’a mata,
“Itama tayi yaw….” katseta yayi”just collect it Zarah!”,
tana tura baki had’i da kyakkyafta idanu alamar bataso ba ta mik’a hannu ta amsa”Nagode”,
har ta juya zata kama door d’in ta bud’e taji yace”Wait”dakatawa tayi ta juya tana kallonshi,hannu ya kai ya d’aukko jakarshi dake a seat d’in baya,d’aurata yayi saman laps dinshi ya bud’e ciki,wani k’aton biscuit ne ya fiddo ya zuge zip d’in ya mayar da jakar,mik’a mata biskit d’in yayi”ki had’a da Yoghourt d’in da kika ce kin taho dashi”,
k’in amsa tayi tasa hannu tana d’an sosa gaban kanta”kai Ya Handsome banda kud’in kuma,don Allah ka barshi wllh kud’in ma fa sunyi man yawa,kuma ba sai in siya biscuit din ba in inaso acikinsu”,
Wani kallo ya jefa mata mai kaman harara”What did i told u initially?ba nace maki banson jayayya ba?”,
yana rufe baki ta juya mashi k’eya ta yadda fuskarta ke kallon k’opa,still yayi cike da mamaki yake bin ta da kallo,
“ZARAH!”ya kirata a kausashe, amsawa tayi ba tare da ta juyo ba,aikam a fusace yace”Zarah ina wasa dake!”
jin sautin yadda yayi Maganar yasata juyowa ta kalleshi ganin ya d’aure fuska sosae yasa ta fara ta6e baki alamar zata yi kuka”Don Allah Ya Handsome ka barshi nasan don ka ci ka taho da shi, dama Hajiya tace baka son cin abinci sai irinsu”,sai yanzu ya gane dalilin da yasa taki amsa,ganin yayi shiru kaman ranshi a 6ace taci gaba”Don Allah kaje dashi
ka ci,wllh in Mutum bai cin abinci Ulcer ke kamashi”ta k’arasa tana mutsustsuke ido da hannunta,
Sigh yayi had’i da nodding kanshi”baki so Ulcer ya kama ni?”da sauri ta d’aga mashi kai alamar eh,
“Why” ya tambaya idonshi a kanta,
“Saboda tsinka ma mutum yan hanji take ya Mutu”,
hannu yasa ya ruk’e ha6arshi”To baki son na mutu ne?”
ɗaga mashi kai tayi”eh ai baka yi aure ba kuma ance in mutum bai yi aure ba ya Mutu aza6a ake mashi”,
bud’a mata ido yayi alamar mamaki”waye ya fad’a maki hakan?”turo baki ta ɗanyi”haka naji ana cewa”,
jinjina kai yayi”to ba haka bane,ai Auren ma is not compulsory and akwae wad’anda Allah bai k’addara masu ma zasu yi auren ba a rayuwansu,amman dae yana da kyau Mutum yayi in Allah ya bashi iko don sunna ne kuma yana da falala sosae and daga cikin falalanshi ake samun yara wanda zasu rinka yi ma Mutum Addu’a in ya mutun don Addu’ar ya’ya ga parents dinsu kar6a66a ce, kuma ni nasan zan samu masu yi man wannan kema nasan zaki yi man ai ko?”,
da sauri ta d’aga mashi kai ta kuma ce”amman dae banso ka Mutun”d’an Murmushi yayi kawai,
“yanzu ki amsa tunda na riga na fito dashi a hanya zan siya wani”,
d’an yamutsa baki tayi”to kuma in baka samu ba fa yanzu fa safiya ne”
“In naje wurin aiki sai in siya wani abu in ci”,
“a wurin aikin ana saida irin shi ne?”
“Yeah,har ma abinci dasu snacks akwae”,
“To kayi man Alk’awari zaka ci abinci ka ƙoshi”,tayi Maganar tana mik’o masa yatsan hannunta da ta d’an lanƙwasa,
kallon yatsan yayi”mi kenan”ya tambaya,
“Alk’awari zamu k’ulla don kar ka k’i cin” dariya ya sake yi har fararan hakoransa suka sake
bayyana”No ba sai munyi hakan ba,ai nace zan ci so don’t worry”,
hannu ta kai ta d’auki biscuit d’in don ya aje shi akan lap dinshi,ta bud’e jakarta ta saka hada kud’in da ya bata daga haka ta juya zata fita,
“Mom Zarah rigima” yar dariya tayi lokacin ta bud’e kopar motar ta zura kafarta guda,juyawa tayi ta kalleshi “Ya Haisam mai balaen kirki” daga haka ta fita daga cikin motar tana zuge zip d’in jakarta,tana fitowa aka bita da ido don glass din motar black tinted ne sam ba’a ganin wanda ke aciki,dama kowa ya k’osa yaga wanda ke cikin Motar ba kamar wasu Students yan section d’in da suka ga shigowar Motar tun a main gate,Maigadi ma tsaye yayi yana jiran wanda yazo d’in ya fito ya kasa k’arasawa wurin Motar don fargaba,a tunaninshi bak’on wurin principal yazo to kuma yasan bata Office d’inta tana wurin Assembly kasantuwar yau Monday hakan yasa Maigadin yin tunanin ita yake jira shiyasa bai fito ba,
Idasa fitowa tayi waje,tana niyyar rufe mashi kopar Motar ya hango Principal cikin shigar alfarma tare da muk’arrabanta sun tunkaro Admin block d’in don angama Assembly d’in,cire seat belt dake ajikinshi yayi ya bud’e Motar ya fito,fatuu da ta rufe kopar ta bishi da ido ganin ya fito,
“Ya Handsome ko raka ni aji zaka yi ne?”,
shaking kai yayi alamar a’a,tsaye tayi tana kallonshi ganin ya zagayo ta bayan Motar,cike da tafiyarshi ta k’asaita ya tunkari principal d’in,Yasalam!zo kaga idanu ba Students din ba,ba malaman ba mai gadin ba,kowa ya zuba mashi na mujiya,tun bayan da ya fito daga cikin Motan principal d’in taja ta tsaya haka ma Vice principal dake a gefenta da sauran malaman da suka rufo mata baya,cike da mamaki take kallon Haisam har ya k’araso gabanta,tunkan yace wani abu ta rigashi,
“Who am i seeing in my School like Haisam?”,fuska a d’an sake yace”it’s me Maa”,gaidata yayi ta amsa,dama haisam Mutum ne mara shariya duk inda yaga wanda ya sani in dai da dama sai ya tsaya sun gaisa koda yana cikin mota ne,hakanne ma yasa da ya hango principal din ta kopar da Fatuu ta bud’e ya fito don ya gaidata,
“Haisam mi kazo yi school d’in nan,ko dama kana zuwa baka ta6a zuwa mun gaisa ba?”,
“No,i just drop off a sis”,ya bata amsa,
“A sis…”, principal ta maimaita yayin da ta maida idonta akan Fatuu dake jingine da Motar haisam sai hura hanci take yi,kai ya d’aga mata itama ta jinjina mashi kai kafin ta kalli malaman da suke gefe da gefenta tace”Malamai Meet Haisam,Son of Senator Ali Adamu Zakee”,gaba daya suka shiga gaisawa dashi bayan ya gaisa da kowa ya yi mata sallama tana cewa ya gaida mata da Hajiya kwana biyu bata samu taje sun gaisa ba,amsa mata yayi da Ok,daga haka ya nufi Motarshi,kallon Fatuu dake mashi Murmushi yayi shima ya maida mata tana ganin zai shiga motan ta d’aga mashi hannu tana mashi bye bye maigadi dake atsaye a sukwane ya
sha gaban haisam d’in ya bud’e mashi motar yana gaishe dashi jinjina mashi kai yayi ya amsa daga haka ya shige cikin motar maigadin ya fara mashi Allah ya kiyaye yalla6ai,Allah ya tsare,Wallet dinshi dake ajiye agefe ya d’aukko,kud’i ya kirgo yan dubu dubu ya mik’o masa daga haka yakai hannu don ya rufe kopar da sauri mai gadin ya rufe masa yana cigaba da yi mashi Addu’a yana d’aga mashi hannu,adaidai lokacin d’ayan baba maigadin da ya zagaya toilet d’in cikin d’an d’akinsu na masu gadi ya fito hannunshi ruk’e da yar buta,ai yana hango abunda ke faruwa ga kudi a hannun abokin aikin nasa yai saurin aje butan ya tunkaro su da hanzari saidai ko kafin ya k’araso haisam ya tashi motar yana yin reverse, hannu ya fara d’aga mashi shima duk da baida tabbacin ko yana gani don glass d’in motan dind’im yake,yana juya kan motan ya tunkari gate d’in fita daga section din,jiki a sanyaye baba maigadin ya tunkari abokin aikin nasa,
“Ashe bak’o akayi”,
ba yabo ba fallasa ya amsa mashi”umm wata ya kawo kuma ma kaman d’an uwan Hajiya ne don naga suna gaisawa”,
gyada kai yayi can kuma yace”naga ma har alheri yayi maka,ai sai ka d’an samman wani abu tunda ba rabona, dama wllh fankan fayau na tashi tun jiya nike istigfari ashe ta wajenka arzikin zaizo” ya k’arasa da d’an murmushi akan fuskarshi,shi kam wanda aka ba kudin tunkan ya k’arasa maganar yake wurga mashi harara,k’okarin saka ma kud’in acikin aljihunsa ya fara yi Horn d’in da akayi ne yasasu d’aga kansu su duka,a wani irin slow glass d’in kopar driver ya sauka,zuro da santalelen hannunsa yayi yai alamar kira,don sonkai irin na wasu Mutanen da sauri mutumin da aka ba kudin ya nufi motar,alamar bashi yake kira ba yayi masa da hannun
nan take yaci burki yai turus awurin shikam wanccan bawan Allah sai yayi tsaye bai tunkari motan ba gudun kada ace shima bashi ake kiran ba,haisam dake hangensa ta side mirror ganin bai taho ba yasashi zuro da kanshi ya yi masa alamar yazo da kan nashi aikam da sassarfa ya nufe shi,yana zuwa haisam ya mik’o masa kud’i masu yawa shima yan dubu dubu da gani sunfi na wancan yawa sosae,hannu na kerma ya kar6a nan take ya durkushe yana mashi godiya harda hawayen farinciki,alamar ya mik’e yayi mashi daga haka glass d’in ya fara rufewa sama yana gamawa yaja Motar mutumin na ci gaba da yi mashi godiya,ko kallon inda wanccan yake bai yi ba ya nufi d’an d’akinsu na gadi,
Uhmm har na tuno da baitin wakar Naziru sarkin wak’a da yake cewa,
*_in rabo ya tsago da kai,kuma abun ya tabbata da kai,Rabbi ne yace saida kai in saida kai kawae sai da kai,in abun yazo babu kai,rabbi ne yace babu kai,in babu kai kawai babu duk duniya ba mai sa dakai…..😍_
Duk wannan abun akan idonsu Principal da sauran malaman dake a wurin harda ma wasu Students ɗin,Murmushi principal d’in tayi bayan Haisam ya fuce ta furta”That’s haisam”,ba k’aramin burge duk wanda ke a wurin yayi ba,kallon Fatuu dake tsaye itama tana kallon abunda ya faru principal tayi ta kirata da sauri ta taho wurinta ta tsaya a gabanta,bin ta da ido tayi ta shiga tunanin tasan yarinyar a Makarantar,kuma tabbas ta santan don irinsu fatuu masu k’okari yawanci zaka ga duk an sansu a makaranta ba kamar ita dake a English Club na Makarantar,
“Which class are u?” principal d’in ta tambayeta,
“Am in class 3c”ta bata amsa,jinjina kai tayi ta waiga gefenta in da discipline master yake tare da wasu prefects da zasu fara taren yan makara bada jimawa ba,
“Malam Mahadi ka kaita Class”da sauri yace”Ok Ma”,kallonta yayi yai mata alamar su tafi ta wuce gaba yabi bayanta daga haka principal d’in da sauran malaman da suka rako ta suka nufi cikin Admin block din,
Tafiya take hankalinta kwance sai fanan shan kamshi take,yayin da wasu Students din keta faman bin ta da kallo,shi kanshi discipline master din kanshi ya d’aure,tsananin mamaki yake ta yadda akai yarinyar keda dangantaka da Senator Ali don yafi kowa sanin halin fatuu a Makarantar shiyasa kullum cikin yi mata horo yake ita kuma tana ganin ya tsaneta ne,kasa daurewa yayi ya dawo daga gefenta yace”dama kina da alak’a da Senator Ali?”,
d’aga kai tayi ta kalleshi sai kuma ta sauke kan fuska adan d’aure ta furta”eh”,
jinjina kai yayi can kuma ya sake cewa”Amman ya kike dashi ne?”shiru ta d’an yi tana tunanin amsar da zata bashi, tsoronta kar tace ita d’iyarshi ce ace kuma shi yasan ya’yanshi tunda gashi ya sanshi,
“Kawu nane shi”ta fad’a cike da fargaba,
“ke yar Daura ce?”da sauri ta d’aga mashi kai alamar eh,
“To amman ya akai kike wannan makarantar”turo baki tayi”to ita ba makaranta bace?”shiru yayi ya rasa amsar da zai bata,lokacin da suka iso bakin class d’insu har ciki ya shiga da ita Malamin English dake da period d’in farko tuni ya shiga kuma shima ya ga lokacin da aka kawo Fatun, hannu discipline ya d’an d’aga mashi”Sannu da aiki malam”,amsa mashi yayi da”Yauwa”,kallon fatuu yayi”jeki ki zauna”ta amsa da toh ta nufi seat d’insu sallama ya yi ma malamin ya juya ya tafi,saida ta isa seat d’in nasu sannan ta tuna da Haulat ganin bata a zaune sai d’ayar da suke zama atare ita kadae dama su ukku suke zama,
Sai da malamin yaci kusan rabin first period sai ga Haulat ta shigo cikin ajin da yar sallama,nufo cikin ajin tayi sumimi sumimi zata wuce,
“From where are you?” taji Malamin dake yin note a allo ya fad’a,tsaye tayi duk tasha jinin jikinta,juyowa yayi ya kalleta,
“Baki ji bane,daga ina kike?” cikin en ina tace”daga bakin gate tare mu akai”,
“Ok ki fita idan na gama kya shigo”,
Magiya ta fara yi mashi tana rokon ya barta ta zauna,daka mata tsawa yayi”I said get out!kinsan kina son ki zauna a class kika ƙi zuwa da wuri”,
Jiki a sanyaye ta juya zata fita fatuu dake kallonta duk bata ji dad’i ba don sai taga kamar laifinta ne da bata biya mata ba kallon Malamin tayi Cikin sanyin murya tace”Sir pls Sorry,Wllh tare muke zuwa kullum da wuri”,wani kallo yayi ma fatun ta d’an marairaice mashi fuska dama suna shiri da ita saboda k’okarinta gashi tana a Club din shi,juyawa yayi yaci gaba da yin rubutu,
“Go and sit down”yace ma haulatu da har tasa ƙafarta guda waje,juyowa tayi ta dawo ciki tana zuwa saitin shi tace” thank u sir”,kai ya d’aga mata ta nufi seat d’insu don ta zauna,suna had’a ido da Fatuu dake ta faman sakar mata Murmushi ta galla mata harara ta fara k’okarin fiddo English Note Book d’inta don tayi copying note d’in da malam ke yi,fatuu kuwa sai faman k’umshe dariya take don tasan laifin da tayi ma haulatun.
Tun bayan da haulat ta shigo basu samu damar yin magana ba don Malamin English din double period gareshi yana gamawa kuma Malamar dake da Next period ta shigo har saida akayi break sannan fatuu ta kalli haulat,
“Sorry k’awata wllh Mantawa nayi in biya maki saboda….” a harzuk’e Haulat ta katseta”Yar rainin sense,ba dole ki manta dani ba ankawo ki cikin had’addar mota,sanyin Ac ya ratsaki ta ina zaki tuna da wata Haulatu”fashewa Fatuu tayi da dariya,
“Ya akai kika san a Mota aka kawo ni?”,
Dan ta6e baki Haulatu tayi”harma wanda ya kawo ki na sani ba Dan gidan Hajiyar Sanata bane?”da sauri fatuu tace”shine ya akai duk kika sani wai?”,
“Inata jiranki naga baki zo ba kuma nasan kin tabbatar man yau zakizo to don kar mu makara yasa na nufi gidanku ina zuwa bakin kopar gidan Umar na gidansu Bello yace man wani mai mota ya tsaya kin shiga kun tafi,ina jin hakan na juyo na nufi bakin hanya inata tunanin ko waye ya d’auke ki don sam ban kawo d’an gidan hajiya araina ba,koda nazo bakin hanya wani Mutum yace man Bus ta wuce baki ji takaicin dana ji ba dole na hawo mashin koda na iso har an fara taren yan
makara,a bakin gate d’inne naji prefects nata Maganar Motar da aka kawo ki suna kuma zuzuta Mutumin da ya kawo kin,kinsan fa A.Sp Asma’u Kabeer har tambayata tayi wai ya kuke dashi…..”, katseta Fatuu tayi da sauri,”ya kika ce mata muke dashin?”,
Dariya haulat tayi”Yo cewa nayi Yayanki ne”,
“Yauwa Allah gwara da kika ce masu hakan yan sa ido kawae,wai kinga yadda aka rink’a bin Motar da ya kawo nin da ido sai ma da ya fito zai gaisa da Principal ashe ya santa innalillahi!ke kinga kuwa yadda ake kallonshi”,
“Ai naji ance wai har kud’i yaba masu gadi,Binta Musa duk ta rud’e wai yadda ya kira Baba maigadi mai kirki ya bashi abun kaman a film…” da sauri fatuu ta amshe”Wllh baki ga uban kud’in da ya mik’o mashi ba,dafa inaga Maigadi Masifaffen hana shi yaso yayi wanda aka bashi aikau ashe Ya Handsome d’in na kallo shine ya kira shi shima ya bashi”,
“Ai in gaya maki suna can sun rud’e sai faman santinshi suke yi anga Mijin Novel,Labour Prefect Binta Musa ma wai zata zo kamun k’afa a wurinki,kinsan ma lokacin da aka samu a layi za’a kaimu muyi punishment ita tasa ni in gudo wllh sauran na can suna shara wasu na wankin toilet,ke hardae Sp Ni’imatu Abdullahi da take miskila saida ta tanka akanshi wllh”,Wata Mahaukaciyar dariya Fatuu tayi,
“Ƙyale banzar tazo d’in,yama za’ai Ya handsome ya sota da fuskarta kaman an ƙona baƙar leda”,hannu Haulat ta kai ta d’an bugi kafadarta”wllh baki da kirki fatuu,aikam tana da kyawunta daidai gwargwado kawae don dai tana bak’a sosae ne,kuma ba ita kadai ke son nashi ba Asma’u Kabeer ai ba laifi tana da kyau kuma wankan tarwada ce….”
“Allah yasa wankan kada ce wllh Ya Handsome ba abunda zaiyi da ita,ce man fa yayi shi baida budurwa”,
ita dae haulat dariya kawae tayi tace”wai bazamu fita break bane sai an dawo”,
“Wane break ai yau a aji zamu yi break d’inmu basai munsha wahalar fita ba”Fatuu tayi Maganar yayin da ta kai hannu ta d’aukko jakarta ta zage zip, fiddo abubuwan dake aciki tayi ta d’aura su saman desk,bin yoghourt da fruit da k’aton biscuit d’in haulat tayi kafin tace wani abu Fatuu ta fara bata labarin kayan dubiyar daya kai mata jiya da daddare da biscuit had’i da kud’in daya bata lokacin da ya kawota,
“Kai Amman Mutumin nan yana da Mugun kirki wllh….” katseta Fatuu tayi”Mugun kirkin ma,ba kinga kayayyakin daya siya man ba lokacin da kika zo gaida ni”,
“Gani kai,nida har na samu rabona,da wani ne kika ma laifin da kikai mashi tun farko ko kallonki ma zai sake yi ne in ma bai d’au mataki akanki ba kenan,amman shi ji abun arzikin da ma yake maki wllh yaji dadi,ga kyau ga kudi ga kirki ko nayi rantsuwa bazan yi kaffara ba samun irinshi a wannan lokacin zaiyi Matuk’ar wahala wllh”, Murmushi kawae fatuu ke saki ta bud’e masu biscuit da yoghourt d’in suka fara ci,
Suna cikin yin break d’in sai ga prefects su biyar sun shigo,su Binta musa ne,Asma’u Kabeer,Amina Aminu,Halima lawal,sai Sp,dama mate dinsu ne suma duk Js 3 suke itama Fatun lokacin da suka shiga aji ukkun harda ita cikin wad’anda aka za6a za’a basu prefect d’in Displine master ne ya hana a bata don cewa yayi in aka bata watarana sai ta kashe wata tunda kaman yar dambe take bunu bunu an kai k’arar ta bugi wata harta raunata ta,gashi kuma lokacin sam bata da wani tsawo yar k’arama ce kan sauran da aka za6an,
tana ganin sun shigo ta wani sha murr,saman Desk din wasu suka zauna wasu kuma suka tsaya a tsaye,tambayarta sukae wai haulatu ta gaya mata sak’onsu tace masu eh,nan suka shiga zuzuta haisam din suna fadin basu ta6a ganin mutum mai irin kyawun shi ba a Nigeria,tambayoyi suka rink’a yi mata cike da rainin
wayau take basu amsa wani lokacin kuma ta 6a66ake masu da dariya ganin yadda duk suka susuce kan Ya Handsome,ba kamar Binta Musa da Asma’u Kabeer su da gaske sonshi suke sai faman rokonta suke wai ta shigar dasu wurinshi da taga dae bilhakki da gaske suke sai tace masu ita bata iyawa don bai wasa da ita duk wadda ke sonshi in ya k’ara zuwa taje da kanta ta fad’i mashi,nan take duk suka ce gaskia bazasu iya ba,bai yi wasa da ita bama ita dake yar’uwarshi balle su, kuma sunga yasan principal kar su ja ma kansu,fatuu tace to sai suyi hakuri kawae,k’arshe dai atare suka idasa cinye kayan break d’in su Fatun kafin suka tafi.
Kallon Haulat Fatuu tayi fuska a tur6une”banzayen sun zo sun cinye mana abu gashi ma ban k’oshi ba”,
d’an Murmushi tayi tace”rabonsu ne ya tsaga suma”,
ta6e baki tayi”to sai kiyi sauri ki taso muje mu siya wani abu kafin adawo”,tayi Maganar had’i da mik’ewa tsaye itama Haulat d’in ta tashi suka fita daga cikin class din.

How To Get Complete A SANADIN MAKWABTAKA

The most reliable and easiest way to obtain the complete A SANADIN MAKWABTAKA  isto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete A SANADIN MAKWABTAKA in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete A SANADIN MAKWABTAKA booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.