Download Complete SONE KO K’IYAYYA (32) by Mommyn Fareesa Romantic Hausa Novel PDF

SONE KO K’IYAYYA??
It’s rometic love story

Story & written
by mommyn fareesa

32

“Aikuwa tana shigowa gabanta yafad’i dataga motar yaya Aliyu a parking lot”Alamar yana gidan”can gefe kuma ta hango yaya sulaiman da nafeesa suna mgn”wanda shine keta surutunsa ita kanta Ak’asa yake”yana zaune kan resting chair ita tana dg tsaye”In’am ta bisu da kallo bbu ko k’iftawa”yaya sulaiman na lura da ita ya banko mata harara”ta d’auke kanta tana gunguni tana fad’in waishi nan son nafee yakeyi?”da wannan tunanin ta nufi part d’in yaya Aliyu tanata y’an kalle kalle sbd kar umma ta ganta….

Ahankali ta tura k’ofar parlourn”ni’imtaccen k’amshin turarensa dana Air fresheners da turaren wuta yadaki hancinta”ta lumshe ido tana yin sallama cikin siririyar muryarta kamar bataso”yaya Aliyu na zaune kan kujera 2seeter”yamik’e dogayen santala santalan k’afafuwan sa Asaman center table yana girgizasu”yana sanye da wondo 3 quarter da t-shirt”sumar kansa tasha gyara ta cika sosai”da Alama tana son Aski”yana sanye da tubarau fari idanuwansa Alumshe kamar meyin bacci”ga Abinci nan samqn center table A aniye Amma beciba….da farko da yaji sallamarta ya d’auka ko gizone take masa”

Amma da yaji motsin rufe k’ofar datayi ta shigo sai ya bud’e lumsassun idanuwansa da sukayi jaa”yana binta da kallon k’asan ido”k’asa kan carpet ta zauna tayi k’asa da kanta tana fad’in yaya ina wuni??”shiru yayi yak’i Amsawa”saima jeho mata tambaya yayi kamar haka”menene?toka Amsa gaisuwata mana”zancen kikeso aja?ki fad’amun meye ki tashi ki bani waje”batayi mgn ba tafara k’ok’arin tashi sbd yabata haushi….koma ki zauna ki fad’amun meye?”yayi maganar murya Akausashe yana d’aure fuska dukda ba kallonsa takeyi ba”nidai tunda baka buk’atar zuwana basai najeba”kuma fa naga an kwana biyu banganka ba”sai nazo naga lafiya??…..iya nan ta fad’a tayi shiru”shi kuma sosai yaji sanyin kalamanta Aransa sbd ya fahimci ko yaya tadamu dashi”saidai ya lura batama san meyasa yafita harkanta ba ay’an

kwanakin….shiru yayi kusan mintina 5 kafin cikin jarumar muryarsa yake fad’in 2 days normal nake na fita dg harkan kine sbd ganin kin d’auka kamar ina takuraki ne…nice nace haka kuma yaya?”ta fad’a tana d’ago kanta ta tsuke d’an bakinta”yabita da kallo yana fad’in gata nake miki da kulawa dake maryam sbd inaso kiyi karatu”Amma ke hankalinki ba’a nan yakeba”rannan da muka dawo fita kikayi bakimun mgn ba” na fito zan tafi masjeed na sameki da yaro nan kuna fira”ke harkinyi girman fira da wani banza ko?”to yayi kyau ai”tunda haka kika zab’a fine kije kici gaba rayuwarki nina cire hannuna Akanki tun…..

knocking d’in da yaji yasaka yayi shiru k’irjinsa na bugawa sbd muryar umma da yaji tana fad’in Aliyu wai kana inane??ita kanta in’am gabanta wani irin mugun fad’uwa yayi ta tashi tsaye da sauri tana zaro ido. Da kallo kawai yaya Aliyu yakebi in’am dashi” shima yana mik’ewa tsaye bbu wata Alamar damuwa ko razana Atare dashi”yaja hannunta da sauri ya nufi d’akin daya keyin exercise Aciki da ita”batare da yace komai ba”tana shiga yajawo k’ofar yarufe”hakan yayi daidai da shigowar umma parlourn”yasaki wata iriyar Ajiyar zuciya Ab’oye yana hamdala ga ubangiji cikin zuciyarsa”yasan ba wani yabu umma zata masa ba idan ta ganshi saidai tayi fad’a kawai “In’am kawai ke beso ta furtama wasu kalmomi marar dad’i…..

wai baka jine ina mgn?da sauri yashafa kansa yana fad’in ina cikine yanzun na fito umma”dama bakaci Abincin ba?”ta fad’a tana kallon warmers d’in Abincin”yanzun zanci saina fita nayi la’asar”takalmin waye wannan??k’irjinsa yabuga! Amma saiya b’oye yanayinsa batare daya kalli takalmin ba yace”nafeesa ta mantasu d’azun da tazo gyaramun d’aki”tab’e baki tayi kafin tace”Anjima ka tabbatar kaje gidan gaisuwar nan dan Allah”insha Allah umma zanje”dg haka ta juya ta fita dg cikin parlourn”yaya Aliyu yasaki Ajiyar zuciya yaje ya murza key jikin k’ofar”kafin yaje yatura k’ofar d’akin dayake yin exercise”in’am na tsaye tanata zare ido duk tayi gumi….

sosai yaji tausayinta”yalura tana tsoron mahaifiyar tasa sosai”shiyasa duk idan yatuna da umma bata son ummi da Ahalinta sai yaji tausayin kansa daya kamu da soyayyar In’am…zo muje parlourn kici Abinci… yafad’a yana kallon ta”k’asa tayi da kanta tana fad’in na k’oshi tafiya zanyi”dama ba wajena kika zoba?”to Amma yaya shine kace naje na baka waje ko?”kin b’atamun rai ne maryam shiyasa”to ai nace kayi hak’uri ko?”to zokiji idan kinaso na hak’ura”batace komaiba tafara tafowa kanta Ak’asa shi kuma yanata kallonta”bana hanaki yawo bbu d’an kwali ba?”narasa meyasa bakya son kitso?”yafad’a yana janyewa dg bakin k’ofar ta fito tana fad’in zafi ke Akwai kitson yaya”hmm! ragguwace ke kawai”yafad’a yana kama hannunta….wani iri taji Ajikinta harta d’ago kanta suka had’a ido dashi”itace ta fara janye idanuwanta da sauri tana jin fad’uwar gaba”wanda batasan dalili ba”suka nufo cikin parlourn yana rik’e da hannun ta….

kinsan Allah zan b’ata miki rai”ki zauna muci Abinci”nasan dama Ai Abinci Abokin gabarkine ko? bafa haka bane yaya Aliyu” lokacin islamiya yakusa kuma ni naci Abinci….ta fad’a Ashagwab’e tana k’ok’arin janye hannunta dake cikin nasa”beyi mgn ba yacika mata hannunta yana kallonta”to yaya yanzun ka hak’ura tunda nice nayi laifi ko?”ya zanyi maryam na hak’ura Amma idan baki zauna kinci Abinci ba bazan hak’ura ba” kaima yaya baka son cin Abinci duk ka rame….sai kuma tayi shiru tana dana sanin furta Abinda ta fad’a”sbd tasan halinsa karya mata wata mugunta”shi kuwa da ido yatsareta yana tunanin dama Ashe tana kallonsa har gashi ta gane yayi rama”bece komaiba yabud’e warmers d’in Abincin yazuba musu”yaya ni wannan yamun yawa”kuma ni shinfaka bata dameni ba”ta fad’a tana kallon Abincin kamar zatayi kuka….

na riga na zuba sbd haka wajibi kici ki tafi ki shirya na saukeki”nafef zan hau”d’aure fuska yayi yace”Akan me?”Amma yaya yaushe rabon daka kaini islamiyar koka saka wani ya kaini??”maryam bansan yaushe kika rainani har haka ba?”kinsan dai bansan dogon zance da jan mgn ko?”

koma miye Ai laifin kine”maganata dake ta k’arshe”duk ranar da nakoma ganinki da wani namiji kuna mgn bbu wani dalili me k’arfi wlh zan baki mamakin daban tab’a bakiba”oya d’auki Abinci kici”yadda taga bbu Alamar wasa kan fuskarsa yasaka batayi musu ba” taja plate d’in Abincin ta aza samqn cinyarta tayi bissimilah ta fara ci kamar mecin magani”kuma badan bbu dad’i ba”ga uban nama yasaka mata Amma tak’i ci“shi kuma yana cin Abincin yana duba time har ukku da rabi tayi”mintina 10 na baki ki idar kije kisaka yunifoam kizo muje na saukeki”dan Allah na k’oshi yaya Aliyu”shareta yayi yak’i mgn”

bbu shiri taci fin rabi tana nishi tace”na k’oshi wlh”ki tashi kije”iya Abinda yafad’a kenan yana cigaba da cin Abincinsa”ta mik’e tsaye tana b’ata fuska ta d’auki plate shoes nata ta nufi k’ofar”saida ta murza key sannan ta murd’a handle d’in k’ofar ta fita”me tubarau dake binta da kallo ya sauke Ajiyar zuciya yazuba ruwa yasha ya mik’e tsaye yawuce ciki sbd yayi Alwalah yaje yayi sallah saiya kaita islamiya d’in….

Anutse yabaro part nasa zuciyarsa wasai sbd shiryawar da yayi da In’am”fushin nan da yayi da ita na 6days yaji jiki”dan ba kad’an ba yayi missing nata”yanata tunaninta”yanufo bakin get”hakan yayi daidai da shigowar mama gaje da zubaida Agidan”da kallo yabi mama gaje bbu ko k’iftawa ta cikin bak’in tubarau nasa sbd canzawar da yaga ta masa”wanda in baka saniba zaka d’auka kamarma be gansuba”zubaida na kashe murya tana karairaiya ta gaidashi”yatura k’ofar get d’in yana fad’in mama ina wuni?

“be jira Amsar taba yayi gaba yabar musu daddad’an k’amshin turarensa”mama gaje dake sanye da wani had’add’en leshi blue da mayafi blue”ta tab’e baki tana fad’in karki koma gaidashi dg yau tunda baya Amsawa”ta fad’a tana canza tafiya”ta k’ara fito da sark’ar dake wuyanta ta yadda za’a gani”bbu kuma laifi tayi kyau sbd hasken bleeching data keyi”zubaida ma dubai Abaya ce Ajikinta tayi kyau da hasken mai itama”suna k’ok’arin wuce part d’in mommy”sukaga yaya sulaiman da nafeesa suna zaune kan resting chairs suna mgn da yunifoam d’in islamiya Ajikinta…mama ina wuni?”cewar nafeesa kanta Ak’asa”lafiya qlau”ina wuni?”cewar yaya sulaiman”ikon Allah! ka rik’e taka gaisuwar tatama ta wadatar”tana fad’in hakan ta yatsina fuska tayi gaba”duk kallon mamaki suka bita dashi”kasancewar sunsan ko wacece ita Awajen umma”suna yin gaba zubaida

tace”gaskiya baki kyautaba mama”ya gaisheki kin disgashi? Eh nayi ai d’an mak’iyiyar yaya hauwa neshi”da Alama k’ilan son nafeesar yakeyi”to A banza A wofi muddin ina numfashi Adoron k’asa bazan bari yaya hauwa ta Amince Aliyu ya Auri wannan shegiyar yarinyar me kama da Aljannu ba…shiru tayi gabanta na wani irin mugun fad’uwa sbd Abba data gani zai rab’asu ya wuce yafito dg parlourn umma”in….ina wuni Alh?”lafiya qlau! Iya Abinda Abba yafad’a kenan yayi gaba”bema ji gaisuwar da zubaida ke masa ba”Allah dai yasa beji mena ceba ni gaje”ta fad’a suna tura k’ofar parlourn suka shiga”
Prince neh

 

FREE DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete SONE KO K’IYAYYA

The most reliable and easiest way to obtain the complete SONE KO K’IYAYYAisto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete SONE KO K’IYAYYAin Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete SONE KO K’IYAYYA booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.