Download Complete A SANADIN MAKWABTAKA Page 22 Romantic Hausa Novel PDF

A SANADIN MAKWABTAKA

BY ZAINAB LALUH
(Oummu Imam)
Paid Book

Free Page 22

Fatuu na tsaye ta jingina da karfen barandar gaban ajinsu ta tafi duniyar tunani,Malam ya fito,tsaye ya yi a bayanta yana kallonta kafin yace “ke cewa nayi ki fito ki tsaya? Wato kinfi karfin ki rage tsawon ki ko? Juyowa tayi ta kafe shi da idanu batare da tace komae ba,hakan yasa ya k’ule cikin daka tsawa yace ” ba dake nike bane! Sunkuyar da kanta tayi k’asa tace”baka ce in rage tsawo na ba ai,cewa kayi in fito waje kawae…..” katseta yayi “da yake ke dak’ikiyace komai sai ance ki yi ko?”
kallon k’asan ido tayi masa suka hada idanu,a fusace yace “kee! ni kike harara….” daga bayansa yaji ance”abunda yafi harara ma yi maka zatai indae wannan ce” a tare suka juya don ganin mai maganar,wani matashin malami ne ya tunkaro su yana sanye cikin farar shadda jamfa hannunsa na dama rungume da Qur’ani dayan kuma rike da zungureriyar dorina,shine displine a Islamiyyar,ya iso inda suke fuska tamke,wanccan malamin yace”Yauwa Malam Nazifi,gatanan kayi mata hukuncin da ya dace,ina bayani hankalinta na wani wuri,nace ta fito kuma tafi karfin ta rage tsawonta”, jinjina kai Malam nazifin yayi daga haka d’ayan malamin ya juya ya tafi,
Kallon Fatuu yayi fuska A d’aure yace “bani hannuwanki! ta d’an marairace fuska tace”Malam don Allah ka buge ni a jiki’ dama malam nazifi yasan bata son bugu a hannu,hakan yasa ya k’ara tamke fuska yace”ina wasa dake? Girgixa masa kai tayi,ya d’aga bulalan ba tare da yace komae ba,a hankali Fatuu ta mika hannuwan suna dan rawa ta runtse idanunta ya fara bugunta tamkar da gayya,yana yi mata bulala biyar ta janye hannuwan tana dan yamutsa fuska don ba k’aramin zafin bugun take ji ba” yace”nace ki sauke hannuwan ne?” turo baki tayi tamkar zata fashe da kuka tace “don Allah malam kayi hakuri…..”ya katse ta “kinsan kina tsoron bugun kike ma mutane iskanci,bulala goma zanyi maki amman wllh kika yi wasa zata koma ishirin”,
sanin da gaske yake yasa ta sake mik’a masa hannu daya tana yi tana canjawa har ya gama,ta juya tana yayyerfe hannu don sosae ya bugeta hannuwan duk sunyi jawur,malam nazifi ya dakatar da ita daga tafiya ta hanyar fad’in “ban sallame ki ba” ta juyo tana kallonshi cikin ido ta d’aure fuska,”kije Office dinmu ki cika mana bokitinmu na ruwa,sannan kije ki wanke gaba d’aya bandakin ku na mata,basai nace kiyi ba,inkin so kina iya kin yi” daga haka ya juya ya shige Class dinsu don shine Malaminsu na Al’Qurani da tajweed,da sauri Haulat ta koma gun zamansu don dama tana a la6e bakin kofa tana ganin duk abunda ke faruwa.
Fatuu ta sauke ajiyar zuciya ta juya don zuwa yin purnishments din da Malam ya bata,a hankali ta ke sa hannu ta na goge kwallar dake zubo mata cikin ranta tana fad’in “Mugu kawae,dama yafi kowa tsanata a makarantar nan,daga yau ba sai ka sake gani na ba zaka bugan…”a fili tace”dama ban zo ba,tunda ba za’a kyale mutum da abunda ya isheshi ba,a daidai nan ta iso bakin staffroom din,Haulat nata faman zuba ido don ganin shigowar fatuu,lokaci bayan lokaci ta ke kai dubanta kan k’opar shigowa amman shiru gashi har an kusa tashi kuma har lokacin malam Naxifi na cikin class d’in saboda abu biyu yake masu,
sai lokacin da aka tashi Mlm Nazifi ya fita,da sauri Haulat ta d’auki jakarta had’i da ta Fatuu ta fice da sauri baiwar Allah har tana yin tuntu6e wurin fita,hanyar kewayensu ta nufa don taji Aikin da aka sa fatun,bata k’arasa isa ba ta hangota a hanya tana tahowa,Haulat ta ja ta tsaya tana kallonta itama Fatun kallon haulat d’in take har ta iso wurinta,hannu kawae ta mik’a mata alamar ta bata jakarta haulat ta mik’a mata jakar a hankali fatuu tace “nagode” daga haka tayi gaba, haulat itama ta bi bayanta har suka fita daga cikin Islamiyyar suka mik’i hanya,haulat a ranta tana ta tunanin mike damun fatuu haka,don tunda tazo ta lura da yanayinta tana cikin damuwa ga bugu da kuma aikin da aka bata,
A fili tace”ba abun mutum ya tambayeta ba tayi man wulakancin da ta saba,gara ma in kyaleta,da tana son in sani ai da ta sanar dani” can dae haulat ta kasa daurewa ta kira sunanta da yake ba tazara sosae a tsakaninsu don a hankali fatun ke tafiya ba kaman yadda ta saba wuwwurga kafa ba,bata juyo ba haulat ta sake cewa”Fatuu”a hankali ta juyo tace”minene”haulat ta k’arasa gabanta tace “mi yake damunki ne naga kaman kina cikin damuwa tunda kika zo” fatuu tayi yar ajiyar zuciya ta ta6e baki tace”Uhmm,in na gaya maki damuwar zaki man magani ne” d’an murmushi Haulat tayi tace”ai bansan mike damunki ba,balle in san ko zan iya yi maki maganin” girgiza kai Fatuu tayi cikin karewar murya tace “koma kinsani bazaki iya man magani ba,don haka ba sai kin ji ba” ta juya ta ci gaba da tafiya a hankali,
Haulat tayi tsaye sototo tana mamakin abunda Fatuu tace ma ta,don tasan bata 6oye mata abu in yana damunta,koma ta 6oye zata dawo ta bayyana mata,a ranta tace” to mike damunta haka da bazata fadi man ba…?
cikin d’an d’aga murya haulat tace “Amman ko da bani iya yi maki maganin ai kilan in baki shawarar da zata iya yi maki maganin ko” shiru bata ce mata komae ba kuma bata juyo ba,hakan yasa Haulat juyawa tabi d’ayan 6arin dake kallon wanda fatuu tabi ta fara tafiya,Fatuu nata juya maganar haulat aranta na shawarar da tace zata bata,tabbas Haulat na bata shawara kuma shawarar nayi mata aiki,ta tuna wani laifi da tayi kwanakin baya wanda ta tsorata sosae hakan yasa Haulat ta bata shawarar yadda zata yi ta ku6uta bayan tayi mata fad’a,aikuwa shawarar tayi mata Amfani don ta tabbatar lokacin ba don aiki da abunda haulat din ta fadi mata ba Kawu Amadu sai ya karyata….,da sauri ta juya “Haulat,haulat..”
ta k’wala mata kira har sau biyu,sannan haulat taja ta tsaya ta juyo fuska a d’aure da alama tayi fushi ne,ganin haka yasa Fatuu ta nufeta ta tsaya gabanta tace”bari in fad’a maki to,amman shawarar zaki bani kar kice zaki man fada don aikin gama ya rigada ya gama, kuma ko baki man fada ba ma nayi dana sani bazan kara aikata irin hakan ba…”ta sunkuyar da kanta jin kwalla zasu zubo mata,ajiyar zuciya haulat ta sauke ta kai dubanta gaban wani gida dake agefensu,ta kamo hannun fatun tace”muje can to ki fadi man nan akan hanya muke” daga haka suka nufi jikin bangon gidan suka jingina,
Haulat tace “ina jinki,mike damunki?” Fatuu dake ta matsar kwalla kamar jira take haulat ta tambaye tan ta rushe da kuka tace “Haulat na bani na lalace,gidan yari za’a kai ni,kuma kilan acan zan mutu ma..” zaro idanu haulat tayi gabanta ya fara faduwa,cikin rashin fahimtar zancen fatuu tace”waye zai kai ki gidan yari?” cikin kuka Fatuu ta zayyana mata duk yadda sukai da Gaye harda aikenta da akai gidan Hajia jiya da daddare harta ga Haisam d’in.
Ajiyar zuciya mai karfi Haulat tayi tace “nasan maganar ma” da sauri ta kalleta tace”kinsan za’a kaini gidan yarin dama kuma baki fad’a man ba..” jinjina kae Haulat tayi tace”jiya da yamma nima na hadu da gayen kuma shine ya sanar dani abunda kika yi har da aka tashi nayi maki maganar, kuma naso in sanar dake Mutumin dan gidan Ha
jiyar Sanata ne amman kika k’i saurarata k’arshe ma sai cewa ki kae wai ko dan sarkin makka ne ke ina ruwanki….”
cikin kuka Fatuu tace”ai ni nayi zaton tambayana kike ko nasan mutumin” taci gaba da rusa kuka,Haulat tace “ki daina kuka,ki kwantar da hankalinki…” a fusace Fatuu ta katseta tace”amari hakkilo?ya za kice wai na daina kuka,kuma taya zan kwantar da hankalina bacin nasan tabbas duk abunda gaye ya fad’a gaske ne..” Haulat ta juyar da kanta gefe ta dan gwalo ido cikin ranta tace”tabb lalle abu yayi abu,yau su Fatuu harda yin fullanci,ita da bata son yi,wani lokacin inta fama da ita tayi man ta k’i yi”
Fatuu dai sai kuka take tana sambatu “ni wllh bansan haka motan keda tsada ba,da bazan ma fara fasa masa gilashi ba,ace kudin shanu gomaa har sau goma ne kudin motar,ba dole gilashin ma yayi tsada ba” Haulat ta jinjina kae ta kalleta tace “nawa yace motar take ne” da sauri fatuu tace”Miliyan goma faaa” haulat tace “bama tada tsada sosae…”,a fusace fuska jage jage da hawaye fatuu tace”
miliyan goman ne ba tsada,shiyasa nace baki da hankali,koda yake nasan baki taba sanin yawan miliyan a hannu bane shiyasa zaki ce haka,yo inama zaki gansu” girgiza kae haulat tayi sam bata ji komae ba don dama ta saba datsa mata magana,tace “dama ban ce ai na ta6a ganinsu ba ko,kawae dae nasan akwae motoci masu tsada sosae da yan gayu ke hawa,don na ta6a ji yaya Osman dinmu yace harta miliyan d’ari akwae” da sauri Fatuu ta dafe kai tana fitar da numfashi mai karfi a rude tace “kice Allah yaso ni da ba irinta na fasa ma gilashi ba,yasin nasan wannan sai dae a harbe ni kawae” ta k’ara fashewa da kuka,ita kam haulat dan juyar da kanta tayi tana murmushi don dariya maganar ta bata,
Zamewa k’asa Fatuu tayi ta zauna dirshan taci gaba da kuka tana sambatu”mi woni ni fatuu,mi woni..,na bani na,in Gwaggo taji wannan maganar nasan sai tasa kawu Amadu ya kakkarya ni kafin awuce dani kuma gidan yari inje in rink’a cin gabza kwarkwata kuma ta gwaigwaye man gashi,tunda nasan ba yafe man zai yi ba,gaskiyar Gaye wllh nasan ko kawu Amadu nayi ma haka ba zai ta6a kyale ni ba sai ya dau mummunan mataki akaina,balle wannan da ba abunda na had’a dashi,nasan ko hajia taji bazata hanashi ya dau mataki a kaina ba,daman kullum tana man fadan in daina rashin ji,ko jiya ma saida tace zamu 6ata,yanzu kuma taji wannan asaran da na yiwa d’anta ta uban kudi haka,tabb ai nasan ma ba za tace ya yafe ba,to mima muka had’a da ita da zasu yafe,daga makwabtaka….,ga Hajiya dama ta iya masifaa….mi maye ni Fatuu,na mutu kawae” ta d’ora hannuwanta saman kai kafin ta dago tana kallon Haulat wadda tuni dama ita ta ke ta kallo cike da tausayi,tace”dama nasan ba wata shawara da zaki iya bani,wannan babban abu ne ba irin wanda ki ka saba ban shawara bane,nasan dole sai an kaini gidan yarin” ta kai maganar tana ta faman yin sheshsheka.
A hankali Haulat ta durk’usa kusa da ita ta kalleta tace”duk da haka ina da shawarar da zan baki,kuma ina tunanin Insha Allahu zata yi aiki…” da sauri fatuu tace”kenan kina ganin in nayi amfani da ita ba za’a kaini gidan yarin ba?mutumin zai hakura?” d’an murmushi haulat tayi”tace ehh,in Allah ya yarda zai hakura nike tunani…” fatuu ta k’ara katseta da sauri”toh don Allah fada man abunda zan yi ko minene zanyi indai za’a kyale ni nidai” Haulat tace “saurin mi kike,zan fad’i maki amman sai kin yi mani Alkawarin in dae aka kyale ki bazaki kara aikata makamancin wannan abun da kika yi ba” wani irin kallo fatuu ta juyo tana mata mai kama da harara,can kuma ta dauke fuskarta ta kalli gefen haulat d’in tace “da yake kare mai bak’in baki ne ya cije ni zan k’ara aikata hakan,ko baki ji tun d’azun nace maki nayi dana sani kuma bazan k’ara ba”
ta kai maganar tana turo baki,Haulat tace”nasan halinki ne kin iya tuban mazuru,sau nawa kike cewa baki k’ara yin abu kuma kizo ki karan” Cike da gatse Fatuu tace”to gwaggo kiyi hakuri…,don kawae kinga ina neman taimakonki zaki taman maganganu sai kace ni mahaukaciya ce zan sake,ni in zaki fada man abunda zan yi ki fada man lokaci na k’urewa” ta kai maganar tana dan turo baki tana kallon hanya,
Karasa zaunawa a kasa Haulat tayi,ta juyo tana kallon fatuu tace”KI JE KI BASHI HAKURI……..

FAST DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete A SANADIN MAKWABTAKA

The most reliable and easiest way to obtain the complete A SANADIN MAKWABTAKA isto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete A SANADIN MAKWABTAKA in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete A SANADIN MAKWABTAKA booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.