Dowload Budurcina Yancina by Benaxir Omar Hausa Novel Complete PDF

BUDURCINA YANCINA

NA BENAXIR OMAR

Sunana Ambar,Rayuwata tana cike da

darasi,tausayi,alajabi, haushi dakuma dana

sani, bana kaunar kowacce ya mace ta

kasance acikin halin dana shiga koda kuwa

makiyata ne, zanbaku labarina nasan bani

kadai bace nake abunda na aikata, tabbas

akwai wasu mata, donhaka inafatan duk

wacce taji labarina inta kasance tanayi

tadaina!, duniya makarantace! Inhar baki

daina lokacin da idonki da kafafunki ke

taimakonki ba, zakiyi danasani wanda nima

nayi!

Sunana Ambar sadiq, mu biyune agun

iyayena, dani da kanwata amina,tsakanina

da amina shekara bakwai ne, kasancewata

yar fari na kasance tauraruwa a idon

iyayena, duk abinda nakeso anamin, ko baa

minba ni saina nema hanyan dana samu ta

dadi ko ta tsiya, tun ina shekara shida

mahaifina suke tafiya dani umra, har aka

haifi amina, muka fara zuwa da ita,

mahaifina banzan wani irin mutum bane a

addinin ma, izala ne? Shia ne? Dariqa ne?

Oho nidai nasan muna ibada, duk hakkin

musulunci yana karewa , dad dina dan siyasa

ne gaba da baya kuma mai sarauta ,jin

hakan basai na kara bayani ba mai karatu

kunsan irin dadin danake ciki, inada fannina

wanda da akace muzauna da ameena,anma

tsabar jinin mu bai haduba yasa dole daddy

yasa aka gyra mata wani fanni, fannina ciki

da falo da toilet saikuma library na, duk

abinda yakamata ace na mallakeshi a gydan

mijina toh na mallaka agydan ubana, daddy

yasha: gayamun duk abinda yakeyi yanayi

ne don insamu na huta, sannan kar zamani

ta rudeni, kar samari su huremin kunne

donshi bayason samarinnan, inbari nagama

makaranta nafara aiki tukun, nace tohm,

dama waya kam na malleketa don ina

primary

Tantiranci Hausa Novels Complete

6 dady yasiyamin waya yacemun na

rike, bazan manta ba kaf age mates dina

nikadai keda waya, kowa na amfani dana

gydansu, haka daddy yasiyamin samsung s1

nafara amfani da ita, a lokacin facebook

kawai akeyi donhaka tuni nima nafarayi,

daddy na duk wannan kayan duniyan da

yakemin, hakan baisa ya takuraniba, komi

nakeso zaasiya akawo, bazai bari ko kofar

gyda najeba kullum ina gyda, inbanda

makaranta saikuma gyda, sai islamiya, kuma

shima kaimu akeyi nida amina direba yajira

mugama mudawo, rayuwata tana tafiya cikin

kwanciyan hankali babu takuri babu

damuwa, dama daddy yasiyamin laptop, nida

amina, muyi game, muyi kallo, inyi chatn a

facebook, ko nayi karatu, ko na taya mama

aiki, duk da gatan danake ciki hakan baisa

nazama doluwa ba, ni nake daukan nadaya a

ajinmu rayuwata cikin walwala, anma

saime???????

BUDURCINA YANCINA

ina shigowa ss1 dady yace wannan karon ba

umra zamujeba, hajj zamuje. Banwani yi doki

ba, don dama nasaba zuwa, haka mukayi

aikin hajj sannan na muka wuce dubai momy

tayi sarin kaya muka dawo nja, a satin muka

koma makaranta, nan aka kawo mana new

comers, baiwani dameniba, anan fa naji ana

rumours ai ankawo wata yarinya batajin

magana, dontana ganin babanta nada kudi

meye meye, still ambar dai ban damuba, ko

tambaya banyiba balle nadamu nasan

wacece,wata rana nafito rike da books dina

zanwuce shago don nafarajin yunwa, naga

ancika hakan yasa naja nazauna, hankalina

duk akan assighnment din da aka bayar

kuma ance bayan break zaayi submitting

donhaka na zauna, inayi tunda shagon acike

yake, ji nayi an kwaramin coke ajikin

uniform!; wat dah fuck!!! Raina a bace nake

fada, namike da matsifa don ganin waye, tayi

sororo tana kallona, tace awh sorry banganki

bane, i was still mad at her. Don yanda nake

kallonta kaman zan cinyeta, babban bakin

cikina shine yadda ta jikamin papern

assighnment, ganin yadda nake kallonta ta

murmusa sannan tace ke ance miki sorry

kuma saiwani hararan mutum kikeyi, dana

tunxura nace u r very stupid, who do u think

u r? Kinyi laifi but u r still complaining, taja

tsaki tareda tambayan kawayenta waye

kuma wannan kwaron? Waye ubanta?sukayi

tsit nikuwa nazo har wuya, dana wanka

mata mari tasa hannu ta rama, nan muka

fara fada, kowa ya tsorata sosai don ba

wanda ya iya rabamu, dakyar wata malamar

mu tazo ta rabamu nan fa aka kaimu staff

office, mukayi kneeling, aka nemo shedu nan

suka zayyana abinda yafaru kowa ya ce nine

da laifi dana fara fadan tunda tabani hkr,

nikuma nace sam bahakaba, aikuwa aka ce

mu share masallaci nidai ko ajikina, tunda

lada zansamu washefari munxo assembly

naganta sai murmushi takemin ko kallonta

banyiba, anan sit mate dita kadija karaye,

take cemin sunan wannan yarinya hafsat

sadiq, naja tsaki nace she doesnt deserve my

dads name, nandai mukayi lessons har aka

fita break, ina zaune ina danne dannen

wayana, naji mutum agefena, ganin hafsat

dince yasa na kaida kai. Tace comon sorry, i

neva knew u r dat rich nd full, na harareta,

tace comon tsre da dafani a kafada, na

kalleta da kyau kyakyawa ce zubin fulani ba

ta da errors ko kadan, hatta magananta mai

jan hankali ne, nima hakan yasa nayi shiru

ina saurarenta, tagama sumbatunta daga

baya tace min plx lez be frnds, i like u, na

kalleta tareda cewa no, harna mike saita

kwace wayana, if bakice yes ba bazanbaki

wayanki ba, aikuwa dole na namika mata

hannu nace yes,

Tohfa mafarin tarihin kawance na da hafsat

sadiq kenan, wanda wainda basusaniba suna

zaton gydanmu daya da ita, hafsat irin spoilt

rich kids dinanne, basada mai fada agyda,

kuma. Komi takeso tanasamu, unlike ni

inada gatan anma daddy na yatsareni sosai,

ahankali nazo nayi noticing hafsat na zuwa

parties, sannan tana kawance da maza,

wanda ni har alokacin banda contact din

namiji daya inba daddy naba, muna haka

akaxo birthday din hafsat, a makaranta aka

kawo cake nine babbar kawa, da cake din

muka yanka akaci aka watse, dayamma ina

daki ta kirani kasancewar itama tanada

wayanta, tacemun zasu kara celebrating a

gyda nace momy bazata barniba, tace

habawa bari zanxo na tsmbaya

d secret behind dix shine hafsat wata irin

macece mayb i should say green snakes,

tanada innocent face ko yatsa akacemiki

hafsat ta cija bazaki yarda ba. Ga uwa uba

ladabi da biyaya, idan hafsat taje gydanku

karki sha mamaki iyayenki su gwada mata

so fiye dake, ladabi tsantsa ga kyautatawa,

ko aiki taga sunayi zakiga taje dasauri donta

tayasu agydansu ko batayi, , haka ta shanye

zuciyan iyayena, ga shigan mutunci in

zatazo, iyayena suna fifita ta akan kowacce

kawata, duk ta siyesu, donhaka data tashi

xuwa saita zo ta da hijabinta dogo har kasa,

ta tsugunna har kasa tagayshe da momy,

mumy ta amsa cikin faraa, tare da cewa

hafsat kin gujemu kwana biyu, ta sosa kai

cikin ladabi tace mummy ina nan, hadda ne

a islamiya ya turnukeni(kuji karya ko

islamiya bata zuwa), nan ta sosa kai tace

momy yau bday na, momy na cikin murna

tace inyee yarinya ashe tagirma,Allah karo

shekaru masu albarka, dama momy na

tsintsan wakene, donhaka dasauri hafsat taje

tana tayata nikuwa ina ganin ikon Allah, tana

tayata mummy sai hararana take wato ni

bazanyiba har kawata tafarayi, hafsat kuwa

ta ce momy dama akwai bday na a gyda

daddy yace zamuyi in gayyato kawayena

biyu shine nace barin tambayeki ko ambar

zataje? Mummy cikin rashin damuwa tace

bakomi barin nemo miki hbd, tamike take

daki ta hado mata super guda daya dakuma

turaruka guda biyu tayita godiya nikuwa

nafice sanye da abaya, muna isa gydansu

nace anma ke yar iska ce, danine zanmutu

ina tambayan momy bazata yarda ba, tace

ahap u r stupid ai, nan muka shige naga

tana canja kaya, tasa skin tight, da body

hook, tayi parking gashinta tadauko jaka oya

kema tube naki, nayi murmushi tareda cewa

haka naxo, tabude baki wat, ke haka zamuje

bday din? Da abaya? Nan taje wardrope

dinta tafara ciro wasu kayyayaki, nan tabani,

nasa, riga da wando ne, wandon iya gwiwa

ya matseni rigan kuma handless, nan muka

fito nace wani dakine, tace wani daki kuma

a hotel ne, mummy basanan kiyi sauri mutafi

kafin sudawo nace musu zanje gydanku ne,

nanfa mukafara yarjejeniya dakyar tashawo

kaina wai don Allah karna bata kunya, na

taimaka mata nan nace ina zuwa zamu

dawo tace tayarda mukaje zaranda, hall guda

aka kama alokacin karfe 8 na dare, hall

yacika tam! Maza da mata anata rawa ga

dim light bana iya ganin komi dole nacire

glass din dana saka, nanfa aka gayyato

celebranta tafito akace tayanka cake da

saurayinta abin mamaki baya wuce rananta,

naga tayi hugging dinshi yadauki caje din

yasa abakinshi, rabinda bai shigaba itakuma

tadauko bakinta tasa, suka hadu suka cinye

tare, nan fa aka zarce da kiss, subhannalahi

nayi yakai dari, hankslina yatashi nan tace

saura best frnd dintama, nadauki cake

nabata abaki anma hafsat sam tace batasan

maganan ba, nan kuwa nace saidai tamutu

ni bazanyi yadda sukayi ba, tafaracewa haba

kekuwa kar amana dariya wayewa ne fa,

naja jaka na zantafi tace noo dawo ba

damuwa, ta dauko cake tasa abunta taci aka

tafa, tarungumeni tamin kiss, ikon Allah,

aikuwa tafi raf raf raf akayi, kainane yafara

ciwo tsantsan kidan dake tashi, nan idona

yayi jaa nace hafsat zantafi ganin batada

niya nafito daniyyan tafiya dasauri tabiyoni

ke, ina zakije? Nace gyda tace ashigan

jikinki? Dole mukoma gydanmu kuma kinga

nasan momy sunanan dole muyi dabara

donhaka yazama dole kijirani, haushi da

takaici yasa naja na tsaya takoma abunta

tana rawa, nan gefena wasu yan shaye

shaye suka fara sandata dole nakoma ciki,

duk inda na tsaya saiwani yazo ya tsaya, i

felt like killing dem ol, basu suka gamaba sai

11 nan muka shiga motan wani frnd din

hafsat agemate dinmu ne daga gani shima

sato mota yayi yafito ya ajiyemu agyda,

tabayan windownta muka dira, dare yayi

dole na hakura akan dasafe na koma gyda,

hankalina yatashi sosai akan me momy

zatace,saida naga msg dinta data turomin

Dad dinki yadawo ki kwana kawai gobe ki

dawo gudnyt dear, nan hankalina yadan

kwanta mukayi bacci, kwata kwata banji

dadin hakan ba, indai haka party yske Allah

wadaran! Bazan sakeba! Wayyoni ambar

ashe duk saka nakeyi domin kuwa mafarin

lalacewata kenan

washegari da safe sai 11 muka tashi naji

haushi sosai don ni a gyda 5 nayi ake

tashinmu asuba, hafsat kuwa sai lokacin

dataga dama, ina tashi nayi wanka nayi

sallah, sannan alokacin itama tayi wankan

tafitar min da dogon riga sabo nasa, muka

fita donmu karya, komi a shirye muka karya,

sannan tace mukoma daki anma nace nikam

sam zantafi gyda yau saturday kuma ina so

nakoma,naje islamiya, haka kuwa akayi aka

dawo dani gyda, muka shiga da hafsat nan

ta bawa momy hakuri momy tanuna ba

komi, na wuce dakina, na shirya nawuce

islamiya, dama har amina ta tafi naje

islamiya ranan nasha duka don banyi hadda

ta ba, haka nadawo cike da bakin ciki da

takaici, ran monday a skul nanfa akafara

zancen birthday mundawo yan iskan cikin

skul, anma irin abunku da yara kowa

namana kallon mun waye, donhaka tuni na

sake raina, sit mate dita kadija karaye tunda

nazo takimin magana, kadija irin ustazannan

ne, da komi kankantan laifinki a addini saita

gyra miki, aikuwa tafaramin waazi a sit,

ambar kiji tsoron Allah iyayenki sunyi kokarin

kare miki mutunci ke bakiyi ba, ashe kenan

duk abinda suka miki a banza kenan?, kina

nema kisa rayuwarki cikin hatsari, na

yamutsa fuska nadauki cottonwool acikin

jakata natoshe kunnena, tayi shiru batace

komiba, ganin haka yasa tadauki littafinta

tayi gaba, badariya salim, wacce tsabar

rigimanta da son gayu take amfani da

badriri, sunan wata mawakiya rihanna,

mahaifinta yarasu tana zama agun kanin

mahaifinta , anan takeson shigemana nida

hafsat, duk da batada kwatan kwatacin

gatan damuke dashi inaga ko 5% riri

batadashi. Anma tana balain son shiga

jikinmu, ga rigima kaman me, ni bana wani

sonta, tazo gefena tazauna tareda cewa

kawas yakike? Na yamutsa fuska nayi shiru,

can tace wlh ingayamiki naji labarin bday

najiya wlh kun burgeni, u gelx rock, anma ni

banjeba cousin sisterna ne taje. Na ja tsaki

tare da cewa common english u cant speak,

how can she be ur cousin nd ur sister? Do u

even knw wat u r sayn? Ta tsaya kallona

tareda cewa kowa anan yasan menene

cousin sister toh akanme zakicemin wrpng

english don kawai kin tsaneni, na kuma jan

tsaki wanda yafi wancan karfi nace, a

dictionary daga first edition har xuwa 8th

edition kinuna min inda akayi defining cousin

sister!, saidai cousin daban sister daban, a

person who is related to u by blood shine

zakiyi clarifyn as sister, ur cousin kuma ur

aunt or uncles child!, so point of correction ,

a person can be ur cousin or sister, but can

neva be ur cousin sister, kokuma kice wa

kanin kakanki grandfather, nop hes ur grand

uncle or grand aunt, donhaka next time if

zakina rough turancinki. Karki yi agabana,

naja jakana nafita taji haushi sosai anma ba

yadda ta iya dani, alokacin ne hafsat takirani

take cemin wani wanda yaje partynta jiya

yaganni yace yanasona, nanfa na haukace

mata anma hafsat tarinka lallamina dole na

nahakura, takaini gunshi da aka tashi kafin

azo daukana, for the first time dana kebe da

namiji kenan wanda ba muharramina ba,

yanata murmushi farine sol dan kyakyawa,

kina gani kinsan kudi ta batashi, yanata

murmushi wanda hakan yafito da dimple

dinsa, amby yakike? Nace lfy, i was so

nervous duk yanda yajani da tadi sainaki

yarda, hakan yasa yakarbi numban wayata,

nabashi muka fito nashiga mota dama

amina tadade tana jirana,

muna xuwa gyda naga text message

dinshi, dat he miss me, abakacin naji haushi

sainaji dadi, daredare na rufe kaina adaki

mukasha wayanmu, asatin naga yayi inviting

dina 2go nan danan nayi downloading, nayi

inviting hafsat ma, da alamu 2go din sabone

don bakowa bane yake kai, muka fara chatn,

ahaka muka saba nida taslim, soyayya

mukeyi sosai kaman bazamu

rabuba,amakaranta kowa yasanmu tare, rich

kids! Kadija karaye kuwa kullum waazi fa

takeyi, ahaka muka zana jarabawanmu na

shiga aji biyar, muna dawowa muka bar

kasan natafi umrah, dama har lokacin taslim

baya xuwa gydanmu, muna dawowa na

shiga aji biyar nan wata sabuwar rayuwar

tafara, alokacin nafarajina nimafa yanmata

ne, duk cikana na budurwa duk yafito,

nadauki dinki nabawa tela yamin uniform

karami yadan matseni momy tayi mita harta

gaji, kadija karaye ma tayi mitan na zageta

tas nace tunda ba ita take siyamun uniform

ba tabarni, duk wannan abun dady baitaba

lura daniba domin kuwa hidimar siyasanshi

yasa hankalinshi baya ma kaina, muna ss2

alokacin karatuna yadan jaa baya, kullum

muna tare da taslim ina xuwa gyda zanhau

2go, nanma mukafara turo hoto, yace naturo

masa hoton kaina, natura, wataranma

innaga bakaya ajikina sainasa hijabi nadauka

natura masa, anma me? Taslim sai yake

gwadamin shi yafison yaganni haka, ina

somshi sosai donhaka sai banyi musu ba,

sai ina tura masa, washegari dama munyi

akan zamu hadu dashi hafsat da saurayinta

imam, mukaje bayan classes muka kebe,

agabana hafsat tarungume imamu, sai

kissing dinshi take, nikuwa sai kallon ikon

Allah, taslim na gefena shima na kallonsu

yace ko zaki gwadane kema, na zaro ido

habawa, bazan iyaba, kiss kyankyami

yakeban, it means zanyi sharing yawun

bakina da wanifa kenan, aikuwa kafin nalura

ya damkoni ya zura harshensa anawa, tuni

nafita a saiti, dakyar muka rabu rannan,

nadawo gyda a gajiye ashe dama haka hug

nd kiss din yake?,nakira hafsat tace yahto

yanmata novice, ya akayi? Ya kikaji abun?

Naja numfashi nace d best feeling in the

whole world kaman karna rabu da taslim naji

nakara sonsa, nanfa hafsat tayita

xugani,donma a skul ne shiyasa nakeso

muhada wani party ko zamu samu muhuta,

aikuwa tuni nace ae wlh, na matsu nima,

abu yaje yadawo nida hafsat duk inda ake

party sai munje mundau attendance, maana

saimunje, duk party indai agarinnnane bana

missing, kuma dama muna shirga karyanmu

wataran muce muna gydansu hafsat wataran

gydanmu, wataran inje zan kwana itama

tafadi haka saimutafi abunmu, mu da

samarinmu su suke kaimu a motocin

gydansu na iyayensu, wataran nida taslim a

mota muke zama musha hugs nd kiss dinmu

hankalina a kwance, nazo nayi realizing am

very sensitive, feelings dina nakusa, donko

tabani taslim yayi fita hayyacina nakeyi,

ahaka adaddafe mukayi candy, muna

gamawa muka hada gaggaruman party, su

kadija karaye kullum waazi, nikuwa nayi

nisa, don yanzu takai asalin romance nake

kwanciya naci nida taslim, muna candy baba

yace zainemamin admission a atbu dama

nida hafsat duk nan muka cika, dana dawo

zaman gyda sainajini a takure kwata kwata

banson zaman gyda wataran ko islamiya

zanje saina zagaya nayi hanyan gydansu

hafsat, kokuma a kofan islamiya taslim

yajiran ina zuwa mushiga motan, daganan

sai muwuce munemi gu marar mutane , muyi

huggs nd kisses dinmu mutaho

ana haka mahaifin taslim yanema masa

mskaranta a u.s, nanfa hankalinmu yatashi

zamu rabu, mukaci kuka kaman ba gobe,

taslim watarana yazoshi jiki a sanyaye na

sata hanya daga islamiya muna hira naga

duk jikinshi baa sake ba, yafadamin meye

yaki, kawai nafara kuka, jin hakan ya fizgi

mota. Fuuuu sai ganinmu nayi a guess inn,

nace ina zamuje? Me zamuyi,? Ya kallen

tareda cewa abunda muka sabayi,

mukashiga yayi logginhn, suka bamu keyn

dakin muna shiga yarufo kofan ya wurgani

kan gado, nanfa muka soma, tunmunayi

naga taslim yafara kiriniyan ciremin kaya,

tuni nayi surremder nace mezamuyi ba tsoro

bakomi yace sex!, gum naji gabana yafadi

dana tuna waazin da kullum mama takemin,

ambar mutunci da darajanki shine

budurcinki, shine yancinki shine gatanki

shine zinare da daham dinki karki kuskura

wani yamiki wayo ya keta, tuni na

tunkudeshi nace bazan iyaba kayi hkr, abun

mamaki sai ga taslim yana kuka, tsakaninshi

da Allah, wlh nayi alkawari zan aureki ambar

kibani karna mutu tuni tausayinsa yakamani

na sake jikina, haka ya ciremin kaya yaketa

min mutuncina, darajana, kimana, yancina,

rayuwata,jarina a matsiyata ta ya mace

narasa Komi na, bana da abun tunkaho

nadawo fankon fyefaye, nadawo maras gata.

Ina kuka har yagama, yanagamawa yajuya

yafara baccinsa, dakyar namike naje bandaki

nashirya, nadawo nazauna natasheshi nace

yakaini gyda lokacin tashi a islamiya yayi

muna hanya nace ya sauken a gydansu

hafsat, tana daki nadhigo dakyar nake tafiya,

tarikoni tare da tambayata, na gayamata

komi, abun mamaki naga hafsat na dariya

toh shine kike damun kanki? Wannan ai its

normal, so barinsa miki ruwan zafi tasamin

ruwan zafin miski nashiga nazauna tukunna

naji daidai, sannan tace muje inrakaki gyda,

muna tafiya tacemun ke sai yanzu nikam

tun muna ss1, beta calm down university

zaki shiga inkikaje kina musu irin wannan

strange abun dariya zaamiki, nadawo gyda

saana momy batanan haka narufe dakina,

naci kukana, sai cankuma naga babu

amfanin jin haushin namike naci gaba da

hidimata, anma abunda yadamen shine har

lokacin taslim bai kiraniba, washegari

mahaka infact sai bayan kwana uku yakiran

yamin bankwana wai inyaje zai kirani,

nikuwa harda cemasa yarike slkawari yace

zai auren yace bakomi, ana haka admission

dinmu yafito mukayi registration,

nanfa mukaje muka kama daki a hostel,

nida hafsat, muka tattaro kayanmu muka

koma, randa zamu koma momy tazaunar

dani tamun waazi sosai na inkama

mutuncina insan irin kawayen dazanna yawo

dasu batasan cewa kawar da ta yarda da ita

tafi kowa cutarta, wato hafsat, muka shirya

daki tsaf zakave a gyda muke, mukasa gado

mukasa carpet da karamin fridge dimmu,

course dinmu daya dukkanmu accounting,

nan muka fara xuwa lecturesz saidai me nan

naga true colourn hafsat samari kala kala,

sannan bata daina komiba sai abunda

yakaru, party dai muna zuwa gwara

yanzuma naga ana lectures toh smtymz

nakan zauna karstu hafsat kuwa tafiya take

abunta, nikuma haka kawai sainaji shaawan

namiji, anma a lokacin nasa araina bazan

karaba, saidaime, na dandani zaginta bazan

iya bariba, tuni acikin samarina nafara

kulasu, duk lokacin da shaawata ta motsa

saina nemo daya muje dakinsu muyi nafito

abuna, hatta frnds nikam, inkuwa naga kawa

kinada saurayi saurayinki yamun kyau next

abunda zakiga nayi shine kiga saurayinki

yazo guna hira, abunda yataimaken inada

ilmi shiyasa , sannan duk haukan yatinya

bana kulata banda kawaye mata sai uban

samari da frnds maza, ko tafiya nake naga

namiji ina shaawansa kuma neman

numbansa nake daredare nakirashi yazo

hostel muna zaune nayi abunda naga dama,

alokacin nama manta me ake kira sallah,

duniya tamun dadi, daddy na turomin kudi

kan kudi saiyazama samarinma su suke bina

saboda kudina, nikuma shegen shaawa ne

dani, hafsat ma hakanne. Ahaka akafara

exams anafarawa na kashe wsyata nadena

kula kowa, saida aka gama exams nadawo

saiti Ahaka muka gama wannan semsetern

nadawo gyda, muka tafi abj nida momy da

amina ananma nabude wasu shafin samarin

duk wanda yazo hira sai ince wa momy frnd,

mony dataga haka tace karkowa yakara

xuwa tamun waazi akan nadaina tara maza,

anma ambar nayi kunnen kashi

nan fa nafara jina a takure, Allah Allah

nake mukoma , muna komawa nafara shirin

komawa makaranta, ran registration na dauki

motan gyda 406 na shige skul, adaidai dept

dinmu na tsaya, ina daddana wayata, nakira

hafsat tare da tambayanta tana ina? Tace

mun bata shigo ba tukun, jinayi an

kwankwasa glass din motan na dago ido don

ganin waye, yana tsaye da shadda ajikinshi,

yasa hula yayi balain kyau, nadan muskuta

kadan nabude glass din sannan yace don

Allah kidan matsa da motarki, nace tohm

batareda nace komi ba again na gyra

parking dina yazo yawuce da nasa, kallo

nabishi dashi, don shaawansa ce takamani

oo bawan Allahn yahadu, tuni nadauki plate

numbansa, ajiki ansa FUAD 4, harnagama

abunda zanyi hafsat tazo mukaje skul

restaurant dan muci abinci inaci ina buga

cokali, hafsat cikin rashin damuwa tace

“what r u cooking in ur head” nayi

murmushin mugunta sannan nace nothing,

ta ce wannan face dinkin is lyk u want to

screw someone” nace lol am a lady, u screw

me , ill screw u too, but den wannan guy din

is different hess soo cute, fuad i think, hafsat

cikkn murmushi tace kisa ranki a inuwa, u

will neva get dat man, yes he’s

rich,popular,handsome, but very strict, baida

kula yanmata balle kiyi mission dinki, nace

bawai nayi na ajiye bane, i love him , tayi

dariya tace duk maitata haka naga fuad

nabarshi donhaka is beta kihakura akan naci

hes not wat u think, nace hafsat lets mek a

bet. If bansamo hankalinshi ba zanbaki dubu

hamsin, tayi dariya sannan tace ashe inada

hamsin kyauta, by the way if kinsamu ill give

u 100k, nayi dariya nace hafsat dont

underestimate my interligence am a lady!,

tace naji so let it be!

daganan muka wuce ahanya nakira amoo,

amoo classmate dina ne, duk inda akabada

assighnments shiyake mun, sannan duk

lokacin danake bukatan information akan

wani amo ne yakesamomin, tare da numban

waya da address, tuni nace nabaka nan da

gobe kasamomin info akan FUAD, saidayayi

shiru na seconds kafin yace ambar bazaki

iya dashiba, ustaz ne fa, ga rashin kula

mata, nayi dariya nace all men are the same,

bawani ustaz, ustazai daga fuska anma

taciki kowane daniska ne, yayi shiru sannan

yace toh, ranan banyi bacci ba duk tunanina

fuad, dan maganan dayamin cikin sanyin

murya, da kuma kamshin turarensa oh God

dat guy is soo cute!, wadhegari ko mom

saidata tambayan lfy ambar? U luk awkward

nace bakomi momy, nanfa nawuce tsabar

doki har kofan gydansu amoo naje yafito

yashiga motan sannan yace gashi komi

kikeso yanacikin nan, na karbi envelope din,

hotunan fuad ne, sai whatsapp numbanshi

nace bana whatsapp but zanfara, ga address

dinsu. Dakuma plate numban motocin

dayake hawa, sai department dinshi

mechanical engineering yake, final year

student, Gp four pointer, position held yayi

sug president, nubass president, mess

president, wow. Nahadu da guru, nakarba

nace yaa result dimmu yaushe zai fito yace

kefa yar duniya ce, jiya dakika shiga ai result

yafito , nace muje naduba nanfa naje gabana

nafadi nagani, alhmdlh sunana yana pass list

gp 3point nadanji daidai, ranan nagayawa

momy result dina taji dadi sosai

hartagayawa dady, rabona da inga daddy

wata biyu saiyace aiki ya rikeshi, hafsat data

duba nata 1point ne tana carryn course

kusan uku,

Ran monday muka koma cikin skul gaba

daya nan nafara close mark wa fuad, duk

fita da shiganshi nasani bana xuwa skul of

eng. Anma saboda fuad kullum zaku ganni

agun, randa nafara kawo masa attempt a

dept dinsune, yana karatu nazauna a

gefensa, baidamuba can nace hy, yadago

yakallen saiya kara sunkuyawa bance komi

ba. Natafi , a restaurant yanacin abinci

nazauna kusa dashi nima nayi ordern abinda

yakeci, anma duk wannan banmishi

maganaba, nagama naje nabiya masa

nawuce natafi, aka sanar dani anbasu

assighnment but baya gari, tuni nakarbi

assighnment naje nasamu wani frnd dina na

lallasheshi yamun, nasa sunan fuad da reg

numbanshi namishi submitting, bayan kwana

hudu ina hostel aka kiran, nafito don ganin

waye, naganshi a tsaye rai abace yace meye

amfanin sawa amin assighnment angayamiki

banda masu min ne? Ina lura dakefa duk

shigemin dakikeyi. Toh barin takamiki birki,

bazanyi taraiya dake ba, keba mutumiyar

arziki bace, ina zankai mai xuwa party?

Marar kamun kai? Kowani namiji sai

anganshi dake? Toh fuad ni nafi karfinki,

randa kika shiryu kika nutsu saiki nemi mijin

aure don jamia bata karbekiba, yana juyawa

zaitafi cikin hawaye nace fuad ko da hakan

na nufin zanmutu ne, zan canja halina

zanbar duk abinda nakeyi, saboda taraiya

dakai yafi komi muhimmanci agareni,

yakalleni yajuya yatafi, tun daga ranar ni

Ambar na nutsu, nadaina xuwa duk wani

party, hatta shigana na canja, naje kasuwa

nasiyo yadin hijabai nadinka nafara sawa,

nadaina kula kowa, saidai har lokacin fuad

yaki bani fuska, narame ina shirin fita

hayyacina domin soyayya, ibada na dawoyi

sosai ina rokon gafaran Allah sannan ina

neman hankalin fuad, nazauna a barhaq ina

cin abinci watarana, wani yazo yanata

murmushi ambar, na kalleshi na kauda kai,

yayi yayi naki kulashi. Kaina a sunkuye, can

naji mutum yazauna kusa dani yakira mai

bada abinci yayi ordern abinda nayi order,

inajinshi anma tunanina baya gun, hankalina

bai nutsu ba, can yace ambar, gabana yayi

mummunan fadi, muryan fahad dayadda

yake kiran sunana na dago naga shine for

the first time naga yanamun murmushi. Sai

yace kishirya karfe 5 zanxo anjima yaci

abincinss harya gama bance komiba, kodan

murna ne,? Ina xuwa hostel nayi wanka nayi

sallah dama hafsat taje abuja gun wani

saurayinta, nashirya tsaf cikin abaya karfe

biyar yazo yakiran nafita muka zauna a

motarsa yace nalura kin canja sosai ambar,

hakan dakikayi shine mutunci kinga kinjawa

kanki mutunci, ko ina kikaje, anma macen

dabata da kamun kai ba mace bace, nan

yace ambar tun randa nafara sonki naji ina

sonki saidai da aka gayamun halinki naji na

tsaneki, nayi niyyan bazantaba alaka dake

ba anma ganin kincanja saboda ni yasa

nabaki chance, ambar i love u, kuka nayi

sosai, bance komaiba, har muka rabu,

tundaga ranan nida fuad kaman tom nd jerry,

soyyanmu tayi karfi soyayya mai tsabta,

hannuna fuad baitaba rikewa ba, duk

shaawata haka nake dannewa yazo yakawo

nafara azumi hakan ya mugun taimakona,

dlfuad ya taimakamin ina kara ilmin addini,

duk wanda yasanni yasan fuad har gun

momy nakaishi taji dadi saboda tayaba da

hankalinshi, nanfa ma hassada akasamu

abunyi yau akai wa fuad wannan gulman jibi

akai masa, most abunda ya fi burgeni shine

baitaba sauraransu ba, saidai yayi ignoring ,

tuni nasawa raina nasamu mijin aure, a

satin hafsat tadawo nan namata bayani fuad

atake nace oya bani dubu dari na. Tace zata

samun, hankalina a kwance, bansaniba ashe

hafsat ma son fuad take tadade tana

harinnsa bata sameshiba gashi tashi daya

nasameshi abinda ya bata mata rai kenan,

haka muka gama wannan semestern nida

fuad kullum tare cin abinci tare. Karatu tare

komi tare, munason junanmu sosai, saidai

duk lokacin da fuad yaga hafsat baya

sakewa yasha cemun narabu da ita ba kawa

bace karnazo ina dana sani, nakancemasa

itakadai natashi da ita anma zanyi kokari

naga ta. Canja

10anma duk dahaka fuad bayaso, ahaka

muka shiga aji biyu alokacin fuad yagama

yafita da second class upper munyi murna

sosai, nan yafara shirin tafiya service,

mukuma munshiga aji biyu watarana ina

assighnment naga kiranshi nadauka tareda

cewa my dear, yace fito inason ganinki

yadda yayi maganan muryanshi narawa nace

toh, inafita kofan hostel nace dear na meya

faru, yace karki kuskura ki yaudaren,

macuciya azzaluma, marar imani ashe haka

kike nayi danasanin saninki, nayi danasanin

haduwa dake. Hankalina yatashi sosai nace

fuad menayi yaja tsaki yace ashe

soyayyanmu akan bet kikeyi? Akan dubu dari

ambar kika karbi soyayyata? Allah ya isa

tsakanina dake, nace fuad bahaka bane wlh

tlh fuad bahaka bane, yace ki amsamin yes

or no, na sunkuyar da kai sannan nace yes,

ya buga motan dakarfi how could u ambar?

Y? Ya shiga cikin motansa sannan yace kisa

aranki baki taba sanin waye fuad ba,

tsakanina dake yakare, yaja motansa yatafi

kuka nafarayi nadauki wayata nakira hafsat

tace tana daki dasauri naje raina abace nace

akanme zaki fada wa fuad? Tace luk hafsat

rayuwace, kowacce mace da basirarta,

kinmanta kema duk macen dakika ga

saurayinta kwacewa kikeyi? Yes naga fuad i

love him, kuma naga yanasonki so i have to

separate the two of u before na iya shiga

ransa, na rikota nahadata da bango hafsat i

hate u, nayi regretn saninki , saninki

baijawomin komi ba sai bakin ciki, nan fa

muka fara fada dakyar aka rabamu na

tattara kayana nadawo gyda, nan momy

hankalinta yatashi dana gayamata meya faru

momy shiru tayi tace kiyi hkr, kicireshi kema,

nace mony fuad nacikin bacin raine anma

inya huce zanbashi hkr tace tohm, anma

me???, sati daya nagagara cin abinci fuad

baya picking calls dina z nima nadaina zuwa

lectures koyaushe ina nemanshi ranan muka

hadu akofan barhaq ina bashi hkr haka fuad

yakallen gashi akwai mutane haka nasauke

girman kai, yadauki ruwan gora ya watsamin

tareda cewa ambar in mafarki kikeyi kifarka

nace bansanki ba i hate u, ko ke mayyace?

Nayi kuka sosai har cikin raina, bantashi

shiga tashin hankali ba saidanaga hafsat da

fuad a mota suna dariya cikin kwanciyan

hankali, innalilahi wainna ilaihi rajiun sanda

ne agefena na karfe nadauka ina xuwa jikin

motan nabude najawo hafsat na kwala mata

ko ta ina ajikinta fuad dakarfi ya fizgeni for

the first time arayuwata da fuad yarikeni, ya

wankamin mari tareda cewa ambar bana

sonki bana sonki bana kaunar ganinki kifita

acikin rayuwata dolene? Kuka nakeyi sosai

ga mutane suncikaa ina kuka sosai, har suka

tafi, yakai hafsat clinic, nayi ciwon SO, maza

mayaudara ne, maci amana, basuda

alkawari, duk sacrifice dazaki musu idan

halinsu ya motsa saisunyi abunda ransu

yabasu, idan zaki bawa namiji hakorinki na

karshe anma namiji zaiyi using wannan

hakorin yayi dariya wa wata, zaki iya

mutuwa akan namiji anma namiji zai je

dawata janaizarki, tuni nafita hayyacina,

nafara sumbatu domin kuwa son fuad yamin

kololuwan illa, of all girls inrasa

meyaudarata sai hafsat? Sumbatu nake,

bana hayyacina, tuni nakoma ruuwa

tsundum, wannan karon harda shaye shaye

nafara

rayuwata ta kara shiga garari, randa

naga bazan iyaba kawai na wuce club

daredare anan nahadu dawani banma san

sunanshi ba don alokacin nafara ganinshi

yalura ina cikin damuwa tuni yabani kwalban

giya yace nasha kadan, aikuwa dana kafa

kai saida nasha yafi rabi, yayi dariya yace

daga yanzu bazaki kara jin damuwa ba, tuni

na fita hayyacina nan nafara surutai ba buge

buge. Yadaukeni yakaini hotel, dama sanadin

fuad nashiryu nadena kula maza donhaka

atake nazubar da randan shaawan dake

damuna, mun mori juna duk abuge,

washegari dasafe ganina nayi nikadai a hotel

tuni nasa kayata nadauki wayata nayi gida,

momy hankalinta yatashi anan na mata

karyan ai na kwana a makaranta saboda

wani assighnmemt nan tamin fadan aidana

fada mata sannan duk lokacin da zankwana

nagayamata, nan nacigaba da xuwa party na

aboye, ina shaye shaye na, idan nayi high

sai dai na tsinceni a hotel, gaba daya

kwanyata ta toshe nadena karatu hatta

exams banyi cikakke ba, muna hutu wata

rana natashi da amai, sosai hakan yasamin

zazzabi nanfa hsnkalin momy yatashi tace

ko malaria ne, anan mukaje asibiti test din

farko likitan yace inada ciki, tunda momy ta

haifen bantaba shiga tashin hankali irin

wannan ba, momy atake tazubar da wayoyin

hannunta, tace likita zamu dawo , tasani

agaba mukaje gyda, momy tana kuka amina

na kuka, momy nacewa yanzu ambar

tarbiyan dana baki kenan? Haba ambar!

Yaza ki samin zargin cewa ban baki tarbiya

mai kyau ba, innalilah. Tadauki waya takira

daddy tace kayi kazo gyda duk garin dakake,

tarufeni adaki nikuwa sai kuka, danasani fal

a fuskata, nan na fara tunanin wacce irin

rayuwa nadauka ma kaina, washegari daddy

yadawo har lokacin bawanda yaci abinci

acikinmu, tamishi bayani a harzuke daddy

yacire belt yashigo dakina yarinka naushina,

duka kam nasha har takeni daddy yayi

tsantsan duka, yanacewa shiba irin tarbiyan

dayabanba kenan, infita inbarmoshi gida

karna spoiling masa image a matsayinsa na

babban mutum sannan dan siyasa, nan

momy takafe cewa laifin dady ne inba kana

zaune agyda ba tayaya zaka dauramin

tarbiyan yara mata ahannuna nikadai,

inbanda aikinka baka da lokacin kowa, gashi

yarka ta kwaso maka rabonka, nanfa fada

yakoma kan momy, daddy yace ya

gwammaci ace masa na mutu akan acemasa

na yi ciki, habawa sai duka yarufeni yace

kasheni zaiyi, tabbas nasan zai iya daddy

nada mummunan zuciya donhaka tuni naroki

momy ta taimakamin tadauko atm da purse

kudine aciki tace gashi ambar kibar garinnan

ki tafi gombe akwai kudi aciki kiyi settling

zanzo nasameki , tabudemin kofa ina kuka

nafice motan gombe nashiga tunani nakeyi

sosai don Allah yagani nayi dana sanin

abunda na aikata

Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 15

3 days ago

Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 14

6 days ago

Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 13

1 week ago

Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 15

3 days ago

Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 14

6 days ago

Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 13

1 week ago

Share this on WhatsApp

Share this on WhatsApp

muna isa gombe bansaniba saida ta

gefena ta tabani sannan ta sanar mun ,

nafito jiki a kasale, na hau kekenapep nace

malam kataimaka kakaini inda zansamu

hotel, aikuwa yakaini wata hotel yar daidai

nakama daki na sati nashiga ciki da falo,

kwantawa adakin nayi nafara kuka sosai,

nayi nadama sosai, tunanin momy da daddy

nake, bayan gydan nashiga domin na yi

wanka, nashiga bathtub din fad na sulale

nafadi, na bugu sosai sannan namuke nafito

jini ke zuba ajikina nan nakira hostel service

din tuni suka kaini asibiti bansan adadin

kwana nawa nayiba nidai nabude naga

momy agefena, zanyi magana tahanani, nan

take cemun ai cikin ya zube, a hotel din

sunrasa wazasu nema nawa, saisuka dauki

wayata suka kirata, tace alhmdlh da cikin

yafita yanzu kinga daddynki zai hakura

kizauna, Allah yagani haushin dadyna nakeji

duk shiyajawomin bayada lokacinmu, harda

laifina nabin kawayen banza dasunan

wayewa akarshe wa wa gari ya waya?

Nagama asara , ba budurci ga ciki ga shaye

shaye ga hulda da maza. Subhannalah, kuka

nayi sosai koda aka sallamen nadawo gyda

dakyar daddy yabarni nazauna, nanfa naciga

da rayuwa a takure, anan nakejin lbrn ai

hafsat sunrabu da fuad,anma bawanda

yasan dalili, gashi anma result gp na ya

balain saukowa har 1point ga courses

danake carryn, naji haushi tuni nasiya sabon

littafin canja rayuwa, nadawo mumina, ba

ruwana azubi mon nd thurs, ga hijabi da

liqab, ga zuwa islamiya rayuwata nadawo

ina takurata ahaka nasamu nacigaba da

karatuna, wasa wasa bana da saurati

tsayayye guda daya na arziki wanda zanfitar

a matsayin miji, duk samarin danake ganin

sunmin over yanzu lokaci yakai da bana

ganinsu , magidantan ma insunxo jikina

sukeso daga baya nadawo nukadai kaman

mayya dox moments are the worst moment

of life, momy tace i should learn a simple

lesson from dat duk wacce batayi usn

ooppotunitynta ba tym will come da

zaiwucemiki nd u shall regret it, aikuwa

nagani don wasa wasa gashu har nayi grads

babu mijin aure. Gashi inason auren, anma

me,??

samarin duk sun gudu, bana ganin

kewar kowa, tunda na kama kaina, harnake

cewa tph kowani namiji dan iska ne, wasa

wasa harnagama atbu nayi 6yrs dakyar

nafita da second class lower, nan nazo

inajiran inyi service duk dahaka shiru,

watarana nafito daga sallooon zanyi gyda

kawai abun mamaki naga taslim a

makwabta yaje hira, na kare masa kallo

tabbas yakara girma gashi yayi kyau , ga

kwarjini yayi fresh na kalleshi saina tunafa

ashe shine yafaramin illa a rayuwata, gashi

yazauna da wata a mota hankalinsa kwance

sai hirarsa yake nazo na wucesu, anma

ranan ban iya bacci ba, taslim is my first

love dole sonshi tadawo min danye araina,

nanfa nalura yarinyan dayake xuwa gunta

fauxa ss2 take lalle namiji dan iska ne,

yagama lalata yanmata anma sai kuga

yanabin kananun yara dasunan aure, aikuwa

tuni haukata ta motsa nace idan ban

aureshiba toh kuwa bawacce zata aureshi,

nasa aka nemomin nukbansa nakirasa yayi

mamaki kwarai tareda cewa yazata nayi

aure nace masa aina zanyi aure munyi

alkawari dakai, yayi murmushi yace bakida

mantuwa ambar ai lokacin yarinta ne, dakin

yi aurenki dont bother abt me, nace but i do,

so is beta kasan nayi don naga kwana biyu

inda kake xuwa yu bets change plans or yull

c a big problem, yayi shiru can yakashe ina

zaune naga txt dinshi gashi akofar gydanmu

nafita nasameshi yakalleni yace ambar nazo

mu fahimci juna, ambar u r my age mate,

aurenmu bazaiyi yiwuba kuma ni tuni na

manta dake. Nayi darriya nace dole kamanta

dani tunda ka kwanta ka ketamin budurcina,

yaja tsaki toh ai kinga matsalar ku kenan na

hausawa mace don kayi havn sex da ita

saitace aurenka zatayi, ke kintsba ganin anyi

haka,? Na kwanta dake na aureki? No i need

a fresh blood, kinmun tsufa, kuma am quite

sure badani kadai kikayi ba, beta find away,

before nazama ciwon kai, yaja motarsa

yatafi nayi kuka sosai nayi dana sani, duk

dadin bakinsa ina yake? Namiji zaimiki dadin

bakine idan yanada bukata duk lokacin

dakika kuskura kika bayar toh daga ranan

dake da slippers darajanku daya, zaki iya

zama da namiji yana binki akan kibashi

kanki for years kiyi tunanin sonkine, anma

inaaa duk randa kika kuskura toh wlh zai

rabu dake, idan bai rabu dake alokacinba toh

kinzama masa sex machine don zai bukaceki

ko yaushe sannan maganan aure na tasowa

shikenan zakiga ya ware, toh waini meya

kaini tun farko? Na farko bin kawar banza,

na biyu rashin rikon addini, don nasan ko

salloli nake tsayarwa da kyau bazai barni na

aikata zinaba, duk mai zunubi mai aikatawa

ya binciki addininsa, ga dai tarbiyan iyaye

alhmdulilah sunyi kokari, kuka nake sosai

bantashi fuskantan tashin hankali ba sai da

aka cemin aminanmu zatayi aure, wayyoni

kanwata ta kama kanta gashi miji yazo mata

tun tana ss2 yafi mata, nifa ? Yatawa

rayuwar take?

nanfa mukayi bikin amina muka gama

tasha gata kam, nanfa nafara jin surutai

danginmu anfara maganan meyasa bazanyi

aureba, nanfa momy hankalinta yatashi dady

kuwa cewa yayi yaban sati biyu idan ban fito

da miji ba toh zai badani, ban damuba

gwara ma yayi hakan saboda ayanzu da

banda tsayayyen nab gwara hakan, aikuwa

daddy yabadani wa dan abokinsa aliyu

haidar, ali baitaba aureba anma shekaransa

34 nanfa ba shiri aka fara hidiman biki ko

bari baayi munsaba ba, shimadai ba yabo ba

fallasa, tun randa daddy yace nafito da miji

ko yasamamin nafara dilka da gyran jiki,

akalla na kashe sama da dubu dari duk dan

na suke kar ali yagane, idan muna waya

yakance ina burgesa yaga nagama jamia

anma ba ruwana kaina akame, shiru nakeyi

don dayasan past dina daba haka ba, nayi

gyran jiki sosai na kimtsu, atunanina duk

bazai ganeba tunda na suke, abinda

bansaniba ko ince mata dayawa basu saniba

shine wannan gyran da akeyi its not natural,

cusa wancan kimtsa wancan no matter how

pure it is, mace tana zuwa da niimanta tun

haihuwa, donhaka idan tabari yatafi

samunsa bamai wahala bane anma kowa

yafison original, nadauka budurci baida wani

muhimminci tunda nayi gyran jiki, anma

budurci fata ce ajikin mace, idan yafita babu

mahaulakin dazai iya sama miki wani, don

haka magani ko gyran jiki bazai kwace ya

mace ba, saidai yarufe hanya!, ahaka mukayi

biki banda wasu kawaye sosai saboda duk

sunyi aure nanfa daddy yazubamin kaya na

tare agydan mijina aliyu, darenne yakamata

ace tazama tafarkona toh anma bahakanba,

washegari ali yadda yake ba yabo ba fallasa

donhaka saina fara tunanin ko bai ganeba

harda adduoina, muna zaune lfy da ali ina

service dina yana aiki, saidai abunda ban

gane ba shine duk lokacin da ali yakiran yajii

inagun service sai yace na bawa kawata

daya mugaysa , baidamenba tunda idan suka

karbama cewa yske su lura dani, sannan duk

lokacin danace zanfita idan kasuwa nace

zanje zaikaini yajirani nagama mudawo hatta

wani hidiman dangi yana makale nikuma

sainaga rashin dacewar hakan, donhaka

naxaunar dashi nace karya damu zanna

zuwa ko ina, yanuna rashin amincewarsa

anma na dage sai yabarni, watarana muna

office dinmu yakamata ace naga officerna

don yamin sighning wasu papers, anma

mutumin baizoba akace sai bayar na

yamma, don haka naxauna muka jirashi

haryazo alokacin na nemi abun hawa narasa,

sai nadauko wayata don nakira ali anma

naga ba caji, hankalina yatashi sosai ga

magrib tayi, wasu yan batch dinmune zasuyi

gyda kasancewar suna girmamani a

matsayita ta matar aure sukace bari su

saukeni nayi niyyan naki amincewa saidai

ganin dare zaimin a gun gashi bakowa yasa

nashiga yana ajiyeni a kofar gyda nabude

gydan nashiga ali nazaune rike da cup din

coke batare da na lura da yanayinsa ba nace

dear yau na wahala da kyar nasamu mai

kawoni bansamu abun hawa ba, yaja tsaki

wacce ta sa najuyo idonsa jajur cikin tashin

hankali nace meya faru dear? Ransa abace

yace kimin shiru munafuka, azzaluma

mayaudariya, iskancin dakikayi awaje bai

isheki ba yanzu kin yi aure bazaki dainaba?

Aini naji mamaki ashe cutana zaayi aka

daukeki akabani, wacce tagama saida

mutuncinta wa samari awaje, yanzu wani

yakawoki a mota anma zakicemin wai aiki,

yanzunnan nadawo agun meyasa ban

samekiba, wlh nayi nadaman aurenki , meye

amfanin auren karuwa???

idona cike take da hawaye, nace bahaka

bane sir, kirifamin baki jahilar banza, kuka

nake sosai anma bai kulani ba, tunda ga

ranan zaman dadi ta karemin agydan ali,

bayacin abincina, baya dawowa gyda sai

tsakar dare sannan idan yafara zagina har

kakkanina saiyazaga, na zauna zaman

hakuri harna gaji daganan na yanke

shawaran nanemi takardata, saidai nace

barin kira momy naji, ina kuka nake mata

bayani tace nanemi izini nazo , dana

tambayeshima cewa yayi adawo daga

karuwanci lfy, nadai kimtsa da kyar nafita

ina xuwa gyda na tarar amina ma tazo, tayi

bul abunta ga ciki ajikinta sainaji hawaye

nazubomin nace amina hankalinki a kwance

ko? Tace adda ambar kinyi kuskure tun

farko dakika dau wannan rayuwar, ganinan

dai duk kawayena suna cemin ban wayeba,

anma meye rashin wayewan dasuke nufi?

Rashin harka da maza, zuwa party

dasauransu na yadda, saboda a tunanina

shine asalin jahilci. Meye wayewa kina harka

da maza? Kowani namiji yarainaki? Yasan

hawanki yasan saukanki? Ina wayewa aciki

kowani namiji yasan bangare najikinki? Ina

wayewa aciki namiji yataba jikinki wanima

gobe yaxo yataba? Wannan shine jahilci. , ki

kama kanki kizama mace on ur own, be d

boss of ur own life, karki kuskura wani

namiji yaga saukanki, neva b a victim, do not

cry for a guy, it would be used against you,

karki bari namiji yaga downfall dinki,

donkinason namiji bashine zaiza yayi dake

kaman akuya ba, yayi ruling dinki kaman

bakida yanci. Balle harki biye mishi waidon

kiyi ladabi da biyayya,

inata kuka amina na bayaninta nayi

nadama sosai inata kuka momy ma kuka

take, tacemun kiyi hakuri bakomi, yanzu ki

koma da ubangijinki kawai anma maganan

ali yasakeki adda baitasoba, kizauna kiyi

hakuri laifin da kika shuka kike girbawa, ba

kedai ba, kowacce mace me irin halinki dole

ta fuskanci tashin hankali a rayuwanta,

baaayiwa Allah wayo, nayi kuka sosai,

momy da amina suka bani shawaran

nazauna a gydan ali duk hakurin aure ake,

kowani aure dakika gani hakuri akeyi, momy

nafada tana kuka tace daddynku duk da

baku taba ganin tashin hankalinmuba

bakusan me nake cikiba, anma nayi hkr

nazauna shiyasa kuka tsinceni haryau,

dadynku baya zama siyasansa yafi masa mu,

momy na kuka tana bamu tarihinta da daddy

yadda tasha wahala sosai, gashi dan siyasa

yanmata suka tsaya mata agaba, dasunan

partners, nanma amina tadaura dacewa ko

hafsat dakike fada kinji lbrnta? Nace a a,

tace toh hafsat haryau batayi aureba, last a

makwabta nakejin labari tabi mijin

makwabciyata kuma kanjamau take dashi,

hauka ne yafara damunta domin kuwa shaye

shaye yamata yawa, ambar ki gode Allah kin

nutsy rayuwanki tacanja so use ur time kiyi

hakuri kizauna har Allah yadawo miki da

hankalinshi, haka na hakura nakoma

nacigaba da zaman gydan ali, abu sai gaba

yake har nazo nafara lura ali neman aure

yake, tunda nake bantaba shiga tashin

hankali da tsanan kaina ba da nadama sosai

akan abubuwan danayi abaya sosai,

haka inaji ina gani abdul ko fadan

kishiya bai kawomin ba, momy ce tazauna

tahadamin kaya akwati set hudu, sannan

tacanjamin kayan daki, ranan mungama gyra

daki nida amina nace amina nifa tunda muka

fara rikicinnan baya saurarona gashi zai kara

aure nasan gatana takare, amina tsyi dariya

tace bai kareba yaruwa auren shine kadai

hanya kisa musu ido karki tanka musu.

Sannan ki gyra jikinki sosai idan momy zasu

tafi london kice tasiyo miki kananun english

wears, sannan ga littafin girki na kawomiki.

Adda mikewa tsaye zakiyi ba boka ba

malam, mijinki nasonki donhaka ki kokarta

duk abinda zai jawo zargi a tsakaninku ki

kawar, nace amina toh mufara da gyran jikin

naji wata a gydan biki kwanaki tana cewa

akwai hadin dawo da budurci, amina tayi

dariya tace adda babu, duk duniya babu

mahaulakin dazaice miki maganan gyran

mata zai dawo miki da budurci karyane ko

shi wayene, sannan idan mai siyarwa ne toh

sunfadane don kawai kisiya kayansu,

maganin gyra saidai ya tsukeki, don budurci

kam karyane don budurci fata ne ajikinki,

saidai maganin gyra yamiki maintainin

jikinki, toh idan yana dawowa da budurci

nawa kika kashe da amarcinki? Almost

200,000 anma meyasa budurcin baidawo ba

har ali yagane? Sannan bakowani maganin

gyra zaki dauka ki cusa ajikinki ba, ki

tabbatar da asalinsa, donhaka dakanki ma

zaki iya gyra jikinki, kisiya miski, gabaruwa,

ganyen magarya da lalle, saiki dage da shan

fruits musamman kankana, wadannan kadai

inkin rike ba ruwanki da asaran kudin gyran

jiki, domin specified ne daga matan zamanin

annabi, ga girki karki kuskura ki maimaita

abinci a sati. Kaya kuwa sai inda karfinki

yakare, habawa nan fa muka dukufa, amina

ta tafasa ruwan ganyen magarya da

gabaruwa tasa nashiga ciki na zauna tace

nayi na sati, ga shafa miski idan nafito,

saikuma shan kankana, sai inyi blendn dinshi

da dabino da mazar kwaila insa madara

insha, tamin hadin mayukan jiki tuni nayi bul,

nayi shirin amarya, ga dinkuna na agun tela,

satin biki sukayi abinsu nima ba yabo ba

fallasa, nadan sake, anma abun cin fuskan

shine nida ali watanmu sha daya anma

harya kara aure, aka kawo amarya tana site

dinta, daredare ali yakiran yazaunar damu

dukka biyu yayi waazi sannan suka wuce

daki, ranan kasa bacci nayi, kwana nayi ina

sallah saidai asuba ne bacci yadan

kwasheni, karfe bakwai naci kwaliyya taf

shaar dani nafito nashirya kumalo, na ajiye

musu nakoma daki ali da amaryarshi basu

fito ba sai karfe goma, anan suka karya

nafito na gaysheshi ya amsa sai wale baki

yake, itakuwa saiwani fici fici take da ido,

nan nakare mata kallo tas, shikuwa kaman

munafiki, ina zuwa daki nazauna lallecin

fuska yarasa wacce zai dauko min sai riri?

Wacce mukayi secondry da ita? Wannan yar

iskan yarinyan? Toh ai angudu baa tsira ba,

munafuka jiya tana ganina ashe shiyasa

dayake waazi tarufe fuska cikin gyale

maima zaiyi da ita? Kyau dai da komi

ba abunda banfitaba, naja tsaki na cigaba da

goge daki, haka har sukayi sati, ninake girki

bai damenba, randa zan karba ba kunya tayi

sallama tazo dakina bayan mungaysa wai

ambar nazo rokan alfarma ne, don Allah

kitaimaka ki sayar min da kwananki, nayi

dariya nace kiyi hkr, nima ina bukatar mijina,

haka tamike tafice, dayadawo ma yana

kwance a falo ina daki, hakadai harya fita

dama kwana bibbiyune, , ganin haka yasa

nazauna nayi tunani barikinta takeyi a gyda

yadda taga dama, idan suka fara wasu

surutai tashi nake nabar musu gu donhaka

na yanke shawaran nima zasu ga nawa

fannin lokacin momy tadawo tasiyomin wasu

arnan english wears. Na jerasu a wardrope,

nan nayi shirin aiki, da sassafe sainayi

wanka naci kananun kaya, wataran mini

skirt da top, wataran wando gajere wataran

bomshot inci kwaliyya inyi paking gashina

infeshe jikina da turaruka, munacin abinci ina

daddana wayana ina ci cikin kissa ina

lumshe idona, takasan ido ina hankalce dashi

sai hadiyan yawu yake, ya kallen yajuya,

dazatan nagama innatashi tafiya nanfa

zanzage na juya jikina sosai, ga kananun

kayannan sunzauna, inje kicin ingama abuna,

inje falo, ko yazo yazauna sai insa ear piece

a kunneta ina jin radio, anma duk ina

hankalce dashi, riri kuwa haushi takeji sosai

saboda bayadda ta iya dani jikinta nanan

kaman na maza kotasa kayan bazatayi

kyauba sannan batada gashin yin yanda

nake, kwata kwata bata da kyau da

charisman dazata hada kai dani donhaka

nayita rayuwata ina sane dasu anma daga

ita harshi sasu nake a kwandon shara,

musamman shi naga yanzu yafara sake

fuska, inyaggani wataran da wani adon sake

baki yake , gashi riri ta rasa aina nake siyo

kaya haka takarbi kudi agunshi tasiyo

enfmglish wears ina kallonta tafara sawa

dariya ma taban. Nanfa nacigaba dabasu

assighnment, tuni ali yadawo saiti yafara

gwadamin maitarsa anma inaaaa ambar

jaaa ajikinki, abinda zuciyata kefadamin

kenan yadda ya wulakantani gwara nadan

jamasa rai duk da cewa nasan m payn for

my misteks, kuma inason kasancewa ds

mijina anma dole nayi hakuri

kullum kwaliyan daban nake, nakoyi

kuskurena, nayi nadama kuma kullum ina

kara nadama, fatana Allah ya gafarceni

abinda na aikata, na lura da son da ali

yakemin,hmnn danma ban kaimishi

budurcina ba, da ace nakai mutuncina da

kimana zaifi haka yawa, bazai taba zargi

naba, kullum acikin koyan sabon salon girki

nakeyi, zanbashi yaci yakoshi, idan kwanana

ne na gyra mishi daki na feshe da turare

sannan na wanke mishi toilet bana bari mai

aiki tayimin wannan, sai akwanan riri ne mai

aiki ke masa hidima, donhaka sainayi usn

wannan advantage din, nadawo da tunanin

mijina kaina, ran jumaa itace ranar da nayi

niyyan mushirya mu daidaita, aikuwa godiya

kan godiya da alkawuruka kala kala, nasan

adduoi danakeyi ne yasa Allahna yaji

tausayina, ahaka nadaidaita da ali komi

normal, ina tarairayan kayana kaman jariri,

ahaka nasamu ciki riri ma haka , nan muka

cigaba da rainon yaran cikinmu duk wani

bita da kulli da riri ke hadamun bana kulata,

hakan yasa fada baya hadamu, cacar baki

ma sai naga dama nake kulata, ahaka

wataran naje biki makwabciyata ammata

kishiya, nayi mamaki sarai danaga hafsat

agun bikin itace kawar amaryar, ta lalace

duk jikinta yasake, gashi tana abu kamar

marar saiti, ba cikaken hankali kuma

haryanzu ba mijin aure ga makarantan

tagama anma miji shiru, yanzu ko

samarinma zaurawan tadena gani, rokona

tayi tayi gafara acewarta ita tayi sanadin

rabani da fuad, anma fuad nasona, nayi

dariya nace dama can ba mijina bane, kinga

mijina muna zaman lfy, taban hkr nan

nabata shawara nace tayi nadama ta gyra

rayuwanta ko Allah zaijikanta inyaso ko da

magidanci ne tasamu, tacemin akwai wani

matansa biyu yana sonta anma ita tana

tsoron wulakancinsa

nayi dariya sosai sannan nace ai

rayuwar dakika dauko dolene namiji ya

wulakantaki shanyewa zakiyi kiyi hakuri

kijure, tace bakomi, bayan natafi satin na

haihu nasamu na mace, nasa mata suna

amina, riri ma ta haihu na mace, tasa mata

bilki,nan muka samu dakyar muke dan hada

kai, duk da mukan samu sabani wani lokacin

anma ba wannan bane damuwata, babban

damuwana shine mijina yasoni kuma ya kula

dani, alhamdulilah bayan gyran kuskure na

danayi, nasamu hankalin maigida na, fuad

ina ganin sanarwan bikinsa wata ustaziyan

mace yanemo ance tana da hankali banyi

mamaki ba tunda dama shidin haka yake,

wanda yafiban mamaki shine taslim yar

sarkin malamai ya aura ance yarinyan akwai

zubyn hadda, naji mamaki kwarai, namiji ba

abun yadda ba, su zasu zauna su bata miki

rayuwa anma insungama suje sunemo

ustaziya, ya ishi mata ishara duk wacce

namiji ke binki don jikinki ya ke yaruwa

kisani yana samun abunsa zaiyi gaba bazai

aureki ba, zainemo yar mutunci da kamala,

shawara ta rage name shiga rijiya, anan

nakawo karshen labarin budurcina yancina,

(don Allah wannan labarin hadawa ko ince

kirkira nayi it has nothing to do da rayuwan

wani, but if plx yazo mistakenly daya da

rayuwar wata, am sorry, don anfara bina

privately ana min wasu illegal tambayoyi,and

please masu copy and paste, idan zaku tura

kuna cire numbana don Allah, ana yawan

adyn dina tahaka) muhadu a labarina na

gaba wato A SANADIN HAKURI

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.