Download Maryama Sarauniya Complete Novel Chapter 5

MARYAMA SARAUNIYA…!!
Marubuciya: *_UMMI A’ISHA
NO.5

 

Tana bathroom tana wanka blessing ta shigo itace ta tsittsince kayan data zubar ta ajiye kowanne a muhallinsa ta sake fito mata da wasu kayan wanda zata saka yanzu,
Bata wani bata lokaci acikin bathroom dinba tafito tana rikeda karamin towel tana goge jikinta, kwalliyar da tayi yanzu bata kai ta dazu ba domin powder kawai ta shafa sai lipstick data shafa akan lips dinta, turare tabi ta feffesa sannan ta nufi abin sallarta,sallar azahar tayi data la’asar duk a lokacin, tana idarwa ta mike ta tasamma wurin kayan da blessing ta fito mata dasu,
Rigace Jessy irin ta yan kwallo baka da wando jeans blue fela sai bakin dan karamin gyale wanda zata daura akanta,

Kayan tasaka ta daura bakin dan kwalin akanta,ta daura bakin combos ta dauki wayarta guda daya wacce take amsa call ta fita da hanzari domin tasan tuni yanzu anfara wasan saboda ganin 5 harda yan mintuna,
Tana sauka kasa tafara kiran blessing,
“Blessing ina key din bike dina?”

Da Sauri blessing taje ta dauko ta kawo mata, tana karba tafita batare da koda ta tambayi dadanta ba ta nufi garejin ajiyar motoci, tana zuwa ni ummi A’isha na hango wani lafiyayyen bike machine kalarsa pink and blue irin wanda mata suke tukawa a kasar India, shi kansa machine din abun kallo ne domin ba karamin haduwa yayiba gashi awani mulmule da fankama fankaman glass agabanshi,
Fito dashi tayi daga cikin garejin ta hau ta bashi wuta tawuce, idan da sabo to mazauna barikin sun saba ganinta akai kusan kowanne yammaci,
Express way tabi titin da babu motaci dayawa akai kusanma duk motocin dake bin wurin masu koyan motane,

Gudun da takeyi bana wasa bane baka jin komai sai shuuuuuuuu wato karar da machine din yake fitarwa yayinda ita kuma tukinta kawai take cikin annashuwa ta kure music tana ji ta cikin earpiece din dake kunnenta wanda ta jono daga cikin wayarta dake sanye cikin aljihun jeans dinta,danjojin jikin bike din ta kunna suna kawowa suna daukewa wal wal,

Cikin mintuna kalilan ta isa stadium din wanda yake katon gaske mai daukar dumbin dubban mutane,

Wurin da aka tanada domin packing din ababan hawa ta nufa ta faka bike dinta ta kulle ta zare key din ta nufi wani dan karamin shop wanda aka tanada domin sayar da kayan sanyaya makoshi da ababan makulashe,

Coke ta karba naroba da popcorn cikin wata hadaddiyar karamar container, cikin stadium din ta hara hankalinta kwance domin hatta suma ma’abota halartar wurin sun santa kusan itace mace tafarko da take zuwa wannan wurin,

Kujerun sama taje ta zauna adaya daga ciki lokacin har anfara buga wasan, tana diban popcorn dinta tana ci tana korawa da coke sannan ta zuba ido tana kallon yanda wasan yake tafiya. Cikin kankanin lokaci samari matasa suka cika kujerun dake kusa da ita kowa yana son kulata amma yana tsoron karta wulakanta shi ita kuwa maryama shan coke din dake hannunta kawai takeyi tamkar bata san abinda suke yiba,

Har karfe 8 tayi ana buga wasan kasancewar wurin tal yake kamar hasken rana yasa mutane da dama basu san cewar dare yafara yiba domin hasken wurin ko allurar kace tafadi to zaka ganta, sai misalin karfe takwas da rabi sannan aka tashi daga wasan,haushi aran maryama kamar zatayi kuka kasancewar wadanda take supporting basune suka yi nasara ba,

“Mtswww….” Taja wani dogon tsaki tareda mikewa tsaye cikeda takaici domin ji take inama bata zo ta kalli wannan abin haushin ba, key din bike dinta ta ciro daga aljihun jeans dinta fuskarta babu walwala,

Wurin da tayi packing taje ta hau bike dinta tabashi wuta ta Lula…,gudun datake yanzu yafi na dazu saboda yanzu titin shiru yake sai yan ababan hawan dake wucewa tsilla tsilla, har tayi kwanar zuwa barikinsu sai kuma tafasa ta juya ta tasamma club domin tana son taje ta rage wannan haushin da ya cika mata zuciya,
Wani kayataccen club ta je wanda ya amsa sunansa domin abubuwan dake gudana acikinsa sai wanda yagani, ko ina na wurin samarine da yanmata wadanda idonsu ya bude suna shagulgulansu wasu kuma disco aka kunna musu suna rawa gefe daya kuma akwai wurin sai da drinks kala kala domin jika makoshi,
Hannuwanta duka biyu ta saka cikin aljihun wandon jeans dinta kunnenta makale da earpiece tana takawa ahankali,

“Abbas kazo mu bar wurinnan dan Allah saboda kasan nifa ban saba zuwa irin wadannan wuraren ba…” Kunnenta ya jiyo mata wata daddadar murya tana magana, zuciyarta ce ta tilasta mata son ganin fuskar mai maganar, juyawa tayi ta koma da baya wurinda taji muryar tana tashi,

“Kai Navy kacika matsala, ban san ko sai yaushe zaka waye ka fito gariba..”
“Babu wata wayewa da zan sake yi bayan wacce nake da ita ayanzu…”
Full light aka bawa wurin daga duhun hasken dake dan kawowa yana daukewa cikin kaloli red,blue,green, yellow da sauransu,

Ido ta zuba masa, shi dinma kallonta yayi cikeda tsanarta domin yagane kowacece,
Kallonta ta dauke daga gareshi tana kokarin barin wurin, ko shakka babu shine wannan guy din data gani agidansu awurin dada dazu da safe sai dai yanzu ba acikin uniform yake ba, kananan kaya yasaka wadanda suka yi daidai da siffarshi,
Ji tayi gaba daya club dinma ya isheta dan haka tafice da niyyar tafiya gida, daidai lokacin suma suka fito zasu tafi, yana kallonta taje ta hau bike dinta ta fita, ba karamin mamaki abin yabashi ba ganin yanda take tuka machine din tamkar wata namiji babu alamun tsoro atattare da ita dadin dadawa kuma ganinta da yayi a club din yasake tabbatar masa da ko ita wacece atake yaji ya tsani duk wata yarinya wacce ta kasance rainon bariki,

“Navy muje mana” muryar abbas ta katse masa tunanin da yakeyi,
Baiyi magana ba yawuce suka tafi,

28 JUMADA AKHIR 1445 AH
Prince neh

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.