Download Complete NIHAAD Chapter 18 By Khaleesat Haiydar Hausa Novel PDF

18

End of free pages…

Har aka kare hutun wata biyu Nihad bata nufi hanyar gidan Kamila ba balle nasu gidan, kamar yanda Mumy ke kiranta kullum haka ma Abbanta, a ko da yaushe cikin demanding kudi take daga wajensa kuma ko sau daya bai ta6a hanata ba, da tayi magana xai tura mata fiye da yanda ta tambaya, Umma ma kusan kullum sai ta kirata, duk kuma wannan abun Abba da Mumy na xaton Nihad na Kebbi tare da Kamila, Umma ce kadai ta san Nihad na kano sai kamilar, gaba daya Kamila ta daina xuwa gida a zuwan tana can kebbi, idan da wani abu sai dai Umma ta shirya ita taje gidanta,

A kullum Mumy bin Nihad take da addu’a, ta rasa dalilin da hankalinta ya ki kwanciya tun barin Nihad gidan, bata da rest of mind kwata kwata, gashi babu abinda xata iya yi game da hakan, ko me xata ce ma Abba baxai ta6a fahimtar ta ba sai dai ma ya juya xancen, a ko da yaushe ta kira Nihad sai ta mata nasiha a kan ta dai kula kuma banda rawan kai da yin kawaye, sai Nihad tace “Mumy ni da ba kowa na sani ba a garin sannan babu inda muke zuwa, kawai karatu nake ta yi against next semester” A haka dai kullum take gaya ma Mumy.

Ranan wata juma’ah Nihad da kawayenta duk suka shirya xa su je duba wata kawar Zully da tayi rashin lafiya, Naf ke driving din, Husnah tace “Amma fa ku kirata ko an sallameta asibiti kar mu je mu yi wahalar banza” Zully tace “Ai ko dai” wayarta ta dauka ta kira kawartata Yusra ta sa handsfree, tana dagawa Zully tace “Ya kuna asibitin har yanzu?” Yusrah tace “Wani asibiti da aka sallame mu tun jiya, ni kin gan ni a Bristol ina shan Ac, Saurayina Alhaji Muktar ne ya biya kudin kwana hudu sai gashi tafiyar gaggawa ya kamasa yau da safe kuma yace min xai kwana uku a Abuja, sai jibi kudin xai kare shine nace gwara in yi zamana a nan” Zully ta kyalkyale da dariya tace “Me ya fi ranki, to bari mu taho can din kawai”

Yusrah tace “Ai ko ku zo, ga abinci ga enough drinks, sannan ga Ac 24/7” Zully tace “To sai mun iso” Tana katse wayar, Naf ta dau hanyar Bristol, Husnah tace “Mu ma muje mu sha Ac kawai” Dariya duk suka yi, Nihad tace “Amma yaushe xa mu fito, kunsan ni bana son xuwa irin wajajen nan in broad daylight” Husnah tace “Mu da xa mu shiga daki mu yi xaman mu meye na wani damuwa” Nihad bata ce komai ba ta ci gaba da danna wayarta, suna isa makeken hotel din Naf ta samu wajen parking, Dai dai nan wayar Nihad ya fara ringing, ganin Abba ne ta ɗan wara ido, Husnah ta kalleta tace “Waye?” Nihad ta nuna mata screen din wayar, Husnah tace “Ohk, bari kawai mu sauka mu tafi ciki, sai ki tsaya motar ku yi waya, idan kun gama ki fito ki kulle sannan ki kirani mu gaya maki room number” Nihad tace “Ohk”

Duk suka sauka daga motar, Naf ta mika mata makulli suka wuce ciki, tuni wayar Nihad ya katse sai ga Abba ya kara kiranta, dagawa tayi hade da sallama tace “Abba ina yini?” Yace “Lafiya lau dear, how are you?” Tace “Alhamdulillah Abba ya aiki?” Abba yace “Mun gode Allah, yaushe xa ku yi resuming ne?” Nihad tace “In two weeks time Abba” Abba yace “Ohk, yaushe kamilar tace maki xa ku dawo?” Nihad tace “Ana saura 2 days mu koma school, tare da mijin xa mu dawo gaba daya” Abba yace “Ohk that’s good, take care dear” Nihad tace “Alright Abba, bye”

Katse wayar Abba yayi, ta bude motar ta sauka sannan ta kulle, tana rike da jakarta bayan ta kulle motar ta nufi entrance din hotel din tana kokarin dialing number Husnah, sunanta ta ji an kira, ta juya da sauri, wani tsohon saurayin Husnah ne, ya nufota da sauri yace “Hi Nihad” Ta ɗan yi murmushi tace “How are you Kabir” Yace “Alhamdulillah, ya kwana biyu?” Tace “Cool” Yayi er dariya yace “Kina da appointment yau a nan kenan?”

Ta ɗan kallesa sai kuma tace “Tare da kawayena nake, suna ciki” Yace “Ohk maa sha Allah, ya school” tace “Fine” A tare suka jera xuwa cikin reception din hotel din yana jan ta da hira, zaune yake a haraban hotel din karkashin inuwa tare da wani da baxai wuce sa’ansa ba yana sauraron duk abinda yake ce masa, da ido ya bi ta da Kabir, at first he quickly imagined ba ita bace kamace kawai,

but yanayin tafiyarta da kuma jakar hannunta wanda duk ya sani ya sa shi ajiye goran ruwan dake hannunsa ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, Buga table din abokinsa yayi da mamaki yace “Heyy!!” Da sauri ya dauke idonsa daga kallonta ya kalli abokin nasa, abokin yace “Why are u staring at her that way, burge ka tayi ko me? Kaga yarinya da saurayinta sun zo holewarsu kayi ta kallonta?” Still bai ce komai ba sai kallon abokin nasa yake babu ko kiftawa, Abokin yace “Khalil” Sauke idonsa yayi daga kallonsa sai kuma ya sauke ajiyar xuciya yace “Yea mamaki abun ya bani shi yasa na bi su da kallo” Dariya Sultan yayi yace

“Haba kai ma ai kasan wannan ba sabon abu bane, yan matan yanxu kam ai sun xama abinda suka zama sai addu’a, basa ma jin kunyan iskanci yanxu, ko wani hotels ka bi su ne, baka lura bane ko 10 mins ba ayi ba set of 3 girls suka wuce mu a nan, su ma kuma duk gun samarin suka zo na sani” Shi dai khalil bai ce komai ba, he was really shock, yarinyar da aka ce tana Kebbi ce ya gani a Bristol, Sultan yace “Kai dai tunda kana da Nadeeyah and upon her parents wealth she is decent sai ka gode ma Allah” Murmushi kawai khalil yayi, Sultan yace “Kuma kuna magana da ita all this while?” Khalil yace “Muna yi”

Sultan yace “Tasan kana kano?” Girgiza masa kai kawai khalil yayi, Sultan yace “Ya batun turawa gidansu?” Khalil yace “Yana nan” Sultan yace “Toh Allah ya nuna mana, but ya kamata kayi nazarin duk abinda nace maka Khalil, pls do so Frnd” Khalil ya sauke ajiyar xuciya yace “In sha Allah, and i appreciate u Sultan” Sultan yace “Nima nagode da ka bani lokacinka har ka saurareni” Murmushi kawai khalil yayi, Sultan ya mike yace “Toh ka koma can inda ka samar ma kanka aiki kar a fara nemanka ko” Khalil yace “Ina jiran wani ne still” Sultan yace “Wa kenan?”

Khalil yayi kasa da murya yace “Another caring frnd like you” Sultan ya sauke ajiyar xuciya yace “All this shall come to pass in sha Allah Khalil” khalil ya ɗan yi murmushi ya mike tsaye ya mika masa hannu sannan yace “I truly appreciate ur care Sultan, nagode kwarai” Sultan yace “Mention not abokina” Har mota Khalil ya rakasa sannan ya dawo ya zauna inda yake zaune har sannan yana cike da mamaki, har karfe shidda na yamma yana xaune wajen bai ga fitowar Nihad ba balle shi mutumin da ta shiga ciki da, kiran Aminu ne ya shigo wayarsa ya ciro ya daga ya kai kunne, Aminu yace

“Toh na ji ka shiru daga cewa xaka bakin titi ka dawo” Khalil yace “Ina nan dawowa yanxu” Aminu yace “Toh ga manyan mangwaro ma Hajiya Inna ta zo ta bada a ajiye maka” Khalil yayi murmushi yace “Toh nagode, sai na dawo” daga haka ya katse wayar. Har aka yi magrib Khalil bai ga fitowar Nihad ba, babu warce ta fado masa a rai sai Mahaifiyarta, ya ji tausayinta sosai, mata me kirki da mutunta ɗan Adam, and such a nyc woman didn’t deserve Nihad as a child… Wayarsa ya dauka yayi dialing number Nihal ya kai kunne, tana dagawa tayi masa sallama, ya amsa yace “Ya kike?” Tace “Alhmdlh, ina yini?

Yace “Lafiya lau, ya lectures?” Tace “Ya shirin jarabawa dai” Yace “Ohh haka ne, ya shirin jarabawa?” Tace “Alhmdlh” yace “Tare xa ku dawo da er uwarki kenan?” Nihal tace “Noo, ai ita tana kebbi” Yace “Ko?” Tace “Eh” Yace “Ita da wa suka tafi kebbi?” Nihal tace “Wannan yayar tawa da ka kai ni gidanta kwanaki” yace “Ohk, yaushe xa su dawo?” Tace “Jiya da na tambayi Umma tace min nan da sati biyu” Khalil ya ma rasa abinda xai ce, jin shiru tace “Hello” Yace “Eh ina jin ki, to shkkn, dama tambayarki xan yi ya jarabawa” Tace “Toh Nagode” Yace “Sai anjima” Daga haka ya katse wayar, kallon cikin hotel din yayi,

yana ta xaune har kusan Isha’i ganin Nihad ba fitowa xata yi ba ya mike ya tafi can inda yayi parking motar gidansu Nihad ya shiga ya bar hotel din, direct gidan Kamila ya nufa, bayan sun gaisa da mai gadin yace “Matar gidan na nan?” Mai gadin yace “Ehh tana ciki” Khalil yayi shiru, sai kuma yace “Ohk an aiko ni wajenta ne” Mai gadin yace “Toh bari ayi mata magana” Yana shiga gate khalil ya juya ya shiga motar ya bar layin.

Direct gida khalil ya nufa erasing everything off his mind kamar ba ayi ba, after all it’s none of his business and will neva be any of his business. Bayan sati biyun da Umma tace ma Abba su Nihad xa su dawo kano, sai ga Nihad tare da kamila a gidan da yamma, babu irin rokon da Umma bata yi ma Kamila akan su xo gida tare da kyar dai daga karshe ta yarda suka taho gidan da Nihad, akwatin kayanta daya kawai ta dawo gida da, tun da suka shigo gate Khalil ke kallon Nihad, ita kuwa shaff ta mance da wani batunsa a gidan sai yanxu da ta gansa, tana ganinsa kuwa mood dinta ya canxa, shkkn kuma ta dawo miserable house din nan da driver din nan a ciki, noo gaskiya ita dai baxata iya ba, xata roki Umma ta yi come up with another plan da xai sa ta sake barin gidan, Kamila ce kawai ta amsa gaisuwan mai gadi da khalil da ke gaisheta, Nihad kuwa tafiya take cike da isa ta nufi entrance din parlor,

tayi wani kyau ta kara haske, kana ganinta kasan bata da damuwar komai, ba komai ya haddasa mata kara haske ba sai cream me shegen tsada irin nasu Husnah da take shafawa yanxu, ga sabulu ga shower gel, Khalil ya bi ta da kallo, suna shiga parlor Aminu yayi kasa da murya yace “Kaga yanda tayi wani haske tayi kyau uwa warce ta tafi duniyanci?” Khalil bai ce komai ba, but he really felt sorry for Abba and Mumy, ya jima bai hadu da mutane masu kirki da karamci irin tasu ba, a watanninsa kusan shidda a gidan Abba ya ja sa jiki kamar nasa,

ya kai ya kawo yanxu hatta Atm card Abba na basa ya ciro masa kudi wanda ko Habibu baya ba Atm card dinsa, shi ko Abba ya ya6a da hankali nutsuwa da girmamawa irin ta Khalil, ya sha gwadasa ya aikesa ya siyo masa abu sai ya linka kudin sau uku ya basa yace haka ake siyarwa amma in sha Allah sai Khalil ya kawo masa canjinsa, ya gwadasa ta fanni daban daban wanda shi khalil bai ma san yana yi ba, duk gidan babu wanda yake da matsala da warce ta zama second Nihad sai Umma, gaba daya ta dau karan tsana ta daura masa tun da Nihad ta fesa mata yana waya da Nihal, to uban me Nihal dinta xata yi da shi,

duk abinda take yi kuma baya damun khalil, Usman ma dai in ya zo basa wani gaisawa, amma Farooq idan yana gari mayar da bakin gate wajen zamansa yake yi sbda Khalil, xaka yi tunanin ya ta6a saninsa, kawai he enjoys gisting with him sbda yana magana kamar wanda yayi ilimi me zurfi, gashi he knows almost everything that’s happening in the world wato he is current, suna dadewa sosai suna hira….

Sai kuma Hajiya Inna da takanas sai ta aiki dreban gidansu Hamid ya zo ya kira mata khalil xata aikesa don hankalinta yafi kwanciya ta basa dukiyarta a kan yaran gidan, kuma aiken baya wuce na dari ko dari biyu. Tun da Nihad ta shiga bangaren Mumy bayan ta fito daga bangaren Umma Mumy ke kallonta, ita dai tana xaune tana ta danna waya, Mumy tace “Wani mai kike shafawa Nihad?” Nihad ta daga kai tace “Mumy cream din Aunty Kamila ne tace in dinga shafawa” Mumy bata ce komai ba, bayan few seconds tace “Ina sauran kayanki?” Nihad tace “Mumy Aunty Kamila tace in bar su a can gidanta” Mumy tace “To tashi driver ya kai ki ki kwaso yanxu” Nihad ta marairaice tace

“Mumy ni fa ba abinda nake bukata a cikin kayan” Tsawa Mumy tayi mata tace “Baxa ki tashi ba” Tashi Nihad tayi kamar xata yi kuka, sai kuma tace “Toh Ai Aunty Kamilan na nan ki bari idan ta koma gida Mumy” Mumy tace “Ba dai gobe za ku fara lectures ba?” Nihad ta gyada mata kai a hankali, Mumy tace “Toh dama ki tabbatar baki dawo gidan nan ba tare da akwatunan ki ba” Mumy na fadin haka ta wuce dakinta, Nihad ta turo baki ta mike ta fice daga parlon, ita har ta mance yaushe rabon a harareta balle a mata fada sai yau…

Washegari bayan ta shirya xuwa makaranta sai da Mumy ta kara jaddada mata kwaso akwatunan ta, har da guntun hawayenta, bayan ta fito compound ta ji ranta ya kara baci da ta tuna cewar shegen mutumin nan ne har yanxu Driver din gidan, kuma ita wllh baxata wani je ta hau adaidaita Sahu ba, tana isa gate suka hada ido da shi don kallon sama har kasa yake mata, wani matsiyacin kallo tayi masa tace

“Da bashi ne kake kallona haka?” Aminu dai sai gwaggwale ido yake, Ta wani ja tsaki ta ma gwammace taje ta hau adaidaitan sbda ganinsa kadai na kona mata rai, ficewarta tayi daga gate Aminu yace “Ohh fitina ta dawo ni Aminu, wllh har na manta da ita a duniyar nan” Khalil dai bai ce komai ba. Bayan kwana biyu da komowar Nihad gida tana kwance bedroom din Umma tana bata labarin yanda suka yi da Aliyu jiya da daddare, Umma dake xaune gefen gadon ita ma ta mike da sauri tace “Kice wllh” Nihad na Murmushi tace “Wallahi Umma” Wani guda Umma ta saki tace “Alhamdulillah, Allah na gode maka…

Yaushe yace xa su xo?” Nihad tace “Nan da sati biyu” Umma tace “Alhamdulillah, Alhamdulillah, amma in ji baki gaya ma kowa ba?” Nihad tace “Aa ke kadai da Husnah na fada ma” Umma tace “Kin ji ki, wacece kuma Husnah, meye na gaya mata xa a kawo kudin ki? Duniyar nan da ta lalace yanxu ai kowa boye kansa yake, kar ki sake gaya ma kowa” Nihad tace “Har Mumy?” Nihad tace “Aa ba dai kin gaya min ba ai shkkn, ni xan mata magana sannan inyi ma Abbanku magana, amma sai xuwa next week” Nihad tace

“Toh Umma” Wani gudar Umma ta kuma saki tace “Allah nagode maka diyata xata xama surkar Janar jikamshi” Dariya kawai Nihad tayi, Umma tace “Toh sai ki kula ki kama kanki kar ki sake kula kowa tunda dai kina da tsayayye yanxu” Nihad tace “Toh, amma Umma yana wani ce min xai rabani da su Husnah” Umma tace “Ahhh!!! shi kuma ya haka??” Nihad tace “Wallahi, kuma ni banga abinda xai sa ya rabani da su ba” Umma tace “Toh ke dai kar ki musa masa ku samu matsala, kiyi ta bin sa duk abinda yace kice to, su kuma ko a hankali ai xa a rabu, ke da kasar waje xa ku xauna? Ko ba haka ba” Nihad tace “Haka yace min” Umma tace “Toh kinga, su Husnah da ba kasar wajen xa su bi ki ba”

Nihad tace “Ai shine” Umma tace “Kai amma nayi farin ciki da wannan labarin Nihad, Allah Ubangiji ya nuna na yan baya haka” Nihad tace “Ameen, Umma bari in dauko wayana” Umma tace “Toh je ki dauko” Daga haka ta fita daga dakin. Ko da wasa Nihad bata sanar ma Mumy ba, tana ta sabgar gabanta throughout the week, kuma har tambayarta Aliyun yayi ko ta gaya ma Mumy tace masa eh. Duk da warning din da Umma tayi ma Nihad na kan cewa kar ta sake gaya ma kowa Aliyu xai turo sai da ta gaya ma Farooq, kamar yanda take favourite din Abbanta haka take favourite din Farooq a gidan, a WhatsApp suke chatting ta gaya masa sai ga shi ya sauka ya kirata, tana dagawa yace “Are you serious?”

Tace “Ehh ya farooq” Yace “Tohh maa sha Allah, Amma Abba bai sanar min ba” Nihad ta zaro ido tace “Yaya Umma tace xata gaya masa” Farooq yace “Ohk, toh Allah ya kai mu next week din, though xan shigo kano jibi” Tace “Toh Allah ya kai mu” Sallama yayi mata ya katse wayar, Tana komawa saman chatting taga message din Nihal tana congratulating dinta, wato har Umma ta gaya mata, murmushi Nihad tayi tace “Thanks twinny” Washegari da Nihad ta fito xata school khalil ya bi ta da kallo disgustingly as usual, sarai jiya Nihal ta gaya masa xa a kawo kudinta next week ta kuma gaya masa daga familyn da xa a kawo kudin, and he really pity the well reputable family, da shi kansa wanda xai aureta din, ganin irin kallon da yake mata ta tsaya tana kallonsa tace “Wai kai Allah ya tsine maka ne da xaka dinga min wani irin kallo idan kaga na fito? Ko da wani abu da muka hada ne ban sani ba?

Toh wllh wllh wllh duk ranan da na sake fitowa ka min kallon walakanci Allah sai na gaura maka mari, kaji har na rantse” Khalil na kallonta yace “Ki mari wa?” Cike da rashin kunya tace “In mareka nace, ko uban waye kai da kake tunanin baxan iya marinka ba? Ni fa wallahi bayan na bar gidan nan na mance an halicce wani mutum me kama da kai a duniya? Toh akan me daga dawowa ta xaka dinga bi na da kallon raini?”

Khalil bai ce mata komai ba cause the sight of her is making him feel feverish, ga wani tafarfasa da zuciyarsa yake, jin bai ce mata komai ba ta ja wani tsaki tace “Banza kawai” Daga haka ta fice daga gidan, Aminu dake lekosu ta dakinsa ya fito yace “kaii, Allah ya wadaran wannan yarinya”

Ana saura kwana hudu su Aliyu xa su kawo kudi, Nihad na bacci da rana Kasancewar ranan asabar ce babu lectures wayarta ya fara vibrate, bude ido tayi don Aliyu yace xai kirata tana jawo wayar taga wata Coursemate dinta Sajida da ba wani shiri suke ba ce ke kiranta, da kamar baxata daga ba sai kuma ta daga ta kai kunne, Sajidah tace “Nihad what is this i am seeing on social media?” Nihad ta bude ido tace “Kamar me?” Sajidah tace “Hau WhatsApp” Daga haka ta katse wayar, sai ga kiran wata secondary school mate dinta Hafsah, tana ta kallon kiran sai kuma ta daga, daga daya bangaren Hafsah tace

“Nihad what’s happening?” Nihad ta mike xaune tace “Ban gane ba?” Hafsah tace “Ki hau WhatsApp” Nihad na kokarin shiga WhatsApp sai ga kiran wata warce suka yi islamiyya tare, kawai haka nan taji gabanta ya fadi, ta dai daga kiran, Badiyya tace “Nihad garin yaya haka don girman Allah??” Hankali tashe Nihad tace “Wai me ke faruwa?” Badiyya tace “Ki kunna data” Nan Nihad taji jikinta ya fara rawa, wani kiran ne ya shigo taki dagawa tayi rejecting ta bude data ta hau WhatsApp din da sauri, messages ta gani rututu na shigo mata, kawai ta bude wanda hannunta ya kai, Wata school mate dinta ce ta turo mata video tana tambayar “what is this Nihad??” Hannun Nihad na rawa ta bude video din, kanta ta gani with just skimpy undies a saman gado ba kuma bacci take ba, sai kuma taga ta mike tsaye turning all over jefar da wayar tayi jikinta na rawa tana zaro ido tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”

sai kuma ta saki wani kara ta sauka daga kan gadon ta durkusa kasa, ringing kawai wayarta ke yi amma ta kasa motsawa daga inda take, bude kofar dakinta aka yi ta daga kai da sauri, Umma ta shigo tana zaro ido tace “Nihad me ke faruwa a social media yanxu Nihal ta kirani tana kuka, kuma wai ta kiraki bakya dagawa”

Nihad ta kasa cewa komai, bata ta6a zama soo weak all her life ba kamar wannan moment din, ji take kamar komai na jikinta ma ya daina aiki, wayar Umma ne ya fara ring ta daga da sauri, Nihal na shessheka tace “Umma ki hau WhatsApp na tura maki” Umma tace “Tohh” Da sauri Umma ta hau WhatsApp ta shiga chat dinta da Nihal ta bude video din, salati ta saki bayan ta gama kallon video din har karshe ta jefar da wayarta kan gado tace “Nihaddd????”

Dai dai da second daya wayar Nihad bai samu breathing space ba, kiran su Husnah ne, Naf, Zully, infact calls upon calls kawai amma ta kasa kwakkwaran motsi inda take a durkushe balle ta daga wani waya, sai rufe ido take tana budewa kamar dai warce ke mafarki tana son ta farka, Umma na tafe hannu ta fashe da kuka tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, na shiga uku na lalace ni Sumayya, Nihad wa ya maki haka? Garin yaya haka Nihad?” Bude kofar dakin aka yi Mumy ta shigo da tashin hankali kwance fuskarta, Umma ta fashe da matsanancin kuka tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Allah mun gode maka ni Sumayya, me xa mu gani haka Nihad” muryan Mumy na rawa tace “Nihad??”

Kawai sai ga hawaye na xuba idonta tana girgiza kai, Wannan ne yasa Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace “Na shiga uku na lalace” Kwalban turare da Mumy ta gani gaban mirror din dakin ta figa tayi kanta amma tuni Nihad ta shige bandaki ta sa makulli, Umma kuma ta rirrike Mumy tana kuka tace “Aa Maryam ki kai zuciyarki nesa kiyi ta furta innalillahi wa inna ilaihi raji’un, nima shi nake yi” A haka ta ja mumy dake kukan bakin ciki da takaici suka fita daga dakin.
kafin dare kai ka ce mutuwa aka yi a gidan, gaba daya iyalan gidan Alhaji Abubakar sun iso gidan Abba, makusantan Mumy duk sun xo gidan, Umma ma yan uwanta da kawayenta duk suna gidan, Aminu sai bin duk wanda ya shigo yake da kallo cike da mamaki don ba ace masu kowa ya mutu a cikin gidan ba gashi khalil da yake ma gulma baya nan tun rana ya fita, kowa kuma ya shigo babu walwala yake nufar entrance din parlor, all the way from Abuja haka Farooq ya biyo flight ya dawo, Usman ma daga kaduna haka ya taho…

Tun faruwan abun nan Umma ke kuka non stop, handkici hudu duk sun yi jagab a hannunta, Mumy kuwa in ka ganta sai ka tausaya mata she is so heartbroken, banda kanninta mata biyu da Yaya farooq da suka jibgi Nihad son ransu babu wanda yayi attempting ta6a ta ko ce mata komai a gidan…… Tashin hankalin Nihad bai linku ba sai da taga alamar Aliyu yayi blocking dinta ta ko ina, WhatsApp, IG, Phone call, Twitter, infact all, kawai sai take fatan Allah ya dau ranta ta huta kawai, gashi har lkcn ta rasa a ina aka mata wannan video din idonta biyu ba bacci take ba…..

Karanta>>> Tabarmar Kashi Chapter 1 By Safiyya Huguma

*Ci gaban labari*

A hankali Nihad ta bude idonta tana bin inda take yashe da kallo, tsakiyar parlor ne kuma a kasan Carpet, gashi babu kowa parlon, everywhere looks strange to her, da sauri ta mike xaune as if trying to recall something, dai dai nan aka bude kofar wani daki ta juya suka yi ido hudu da shi, sai da numfashinta ya dauke na few seconds da kyar ta jawo numfashin, lkci daya komai ya dawo mata ta kurma wani uban ihu jikinta na rawa tana kallonsa, sai kuma ta mike a guje tayi hanyar kitchen kamar mahaukaciya….

Na Yi tsallake na na page,so Kuma page din Yana da muhimmanci shiyasa xan yi post dinshi saboda lbrin ya tafi daidd

 

FAST DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete NIHAAD Chapter 17 By Khaleesat Haiydar

The most reliable and easiest way to obtain the completeNIHAAD Chapter 17 By Khaleesat Haiydaristo purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete NIHAAD Chapter 17 By Khaleesat Haiydar in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the completeNIHAAD Chapter 17 By Khaleesat Haiydar booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.